Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sahih Muslim

Lamba 1514

Lamba 1514Littafi na 5, lamba 347Lambar Larabci 663.01
حَدَّثَنَا يَحْيَى بْنُ يَحْيَى، أَخْبَرَنَا عَبْثَرٌ، عَنْ سُلَيْمَانَ التَّيْمِيِّ، عَنْ أَبِي عُثْمَانَ النَّهْدِيِّ، عَنْ أُبَىِّ بْنِ كَعْبٍ، قَالَ كَانَ رَجُلٌ لاَ أَعْلَمُ رَجُلاً أَبْعَدَ مِنَ الْمَسْجِدِ مِنْهُ وَكَانَ لاَ تُخْطِئُهُ صَلاَةٌ - قَالَ - فَقِيلَ لَهُ أَوْ قُلْتُ لَهُ لَوِ اشْتَرَيْتَ حِمَارًا تَرْكَبُهُ فِي الظَّلْمَاءِ وَفِي الرَّمْضَاءِ ‏.‏ قَالَ مَا يَسُرُّنِي أَنَّ مَنْزِلِي إِلَى جَنْبِ الْمَسْجِدِ إِنِّي أُرِيدُ أَنْ يُكْتَبَ لِي مَمْشَاىَ إِلَى الْمَسْجِدِ وَرُجُوعِي إِذَا رَجَعْتُ إِلَى أَهْلِي ‏.‏ فَقَالَ رَسُولُ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم ‏ "‏ قَدْ جَمَعَ اللَّهُ لَكَ ذَلِكَ كُلَّهُ ‏"‏ ‏.‏
Daga Ubayyu ɗan Ka'ab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wani mutum ya kasance nesa da masallaci sama da kowa a iya sanina, kuma ya kasance ba wata sallah da take wuce shi, ya ce: Sai aka ce masa: Ko nace masa: Ai da za ka sayi jakin da zaka dinga hawan shi cikin duhu, da zafin rana, sai ya ce; Ba na son gidana ya kasance a gefen masallaci, lallai ni ina son a rubuta mini tafiya ta zuwa masallaci, da dawowa ta idan na dawo zuwa iyalaina, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: «‌Haƙiƙa Allah Ya haɗa maka wadannan gaba ɗayan su».

Fassara: HadeethEnc.comSharhinsa

Tushen bai rubuta wata daraja ga wannan ruwaya ba.

Inda Insakulofidiyar Hadisan Annabi da aka Fassara (HadeethEnc.com) take da ainihin rubutun wata ruwaya, ana nuna fassararta a ƙarƙashin wannan ruwayar tare da sunan tushen. An haɗa su biyun ne ta hanyar shiri, daga Larabcin kaɗai: dukan rubutun hadisin da ke cikin insakulofidiyar, tare da sunan Sahabin da ya ambata, shi ne ƙarshen ruwayar harafi da harafi. Babu wanda ya bincika wannan haɗin, kuma masu bitar Sabīl ba su duba fassarar ba. Larabcin shi ne rubutun.

Littafi na 5 · The Book of Mosques and Places of Prayer

Rubutun Larabci, lambobi, sunayen littattafai da darajoji ana nuna su daidai yadda suke a cikin wani buɗaɗɗen tarin bayanai (hadith-api). Sabīl bai tabbatar da daidaitonsa ko haƙƙoƙinsa ba tukuna, kuma ba a fara bitar malamai a kansa ba. Kafin lokacin, ku kwatanta ruwaya da bugaggen littafi kafin ku dogara da ita.