Daga Ibn Abbas -Allah ya yarda da su- ya ce Manzon Allah ya buxe mana labule kuma Mutane sunyi Sahu a bayan Abubakar sai ya ce: "Ya ku Mutane babu abunda ya ragu daga cikin Alamomin Annabta sai Kyakkyawan Mafarkin da Musulmi zai ganshi, ko a ganar masa, ku saurara kuma lallai ni ina hana karanta Al-qur'ani a a Ruku'u ko a Sujada amma a Ruku'u ku girmama Allah kuma a Sujada to kuyi qoqrin Addu'a an kusa a amsa Muku"
Tushen bai rubuta wata daraja ga wannan ruwaya ba.
Inda Insakulofidiyar Hadisan Annabi da aka Fassara (HadeethEnc.com) take da ainihin rubutun wata ruwaya, ana nuna fassararta a ƙarƙashin wannan ruwayar tare da sunan tushen. An haɗa su biyun ne ta hanyar shiri, daga Larabcin kaɗai: dukan rubutun hadisin da ke cikin insakulofidiyar, tare da sunan Sahabin da ya ambata, shi ne ƙarshen ruwayar harafi da harafi. Babu wanda ya bincika wannan haɗin, kuma masu bitar Sabīl ba su duba fassarar ba. Larabcin shi ne rubutun.
Rubutun Larabci, lambobi, sunayen littattafai da darajoji ana nuna su daidai yadda suke a cikin wani buɗaɗɗen tarin bayanai (hadith-api). Sabīl bai tabbatar da daidaitonsa ko haƙƙoƙinsa ba tukuna, kuma ba a fara bitar malamai a kansa ba. Kafin lokacin, ku kwatanta ruwaya da bugaggen littafi kafin ku dogara da ita.