Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Lallai Allah Ya rubuta kyakkyawa da mummuna, sannan ya bayyana haka

عَنْ ابْنِ عَبَّاسٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا عَنْ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فِيمَا يَرْوِي عَنْ رَبِّهِ تَبَارَكَ وَتَعَالَى، قَالَ: «إنَّ اللهَ كَتَبَ الحَسَنَاتِ وَالسَّيِّئَاتِ، ثُمَّ بَيَّنَ ذَلِكَ، فَمَنْ هَمَّ بِحَسَنَةٍ فَلَمْ يَعْمَلْهَا؛ كَتَبَهَا اللهُ عِنْدَهُ حَسَنَةً كَامِلَةً، وَإِنْ هَمَّ بِهَا فَعَمِلَهَا؛ كَتَبَهَا اللهُ عِنْدَهُ عَشْرَ حَسَنَاتٍ إلَى سَبْعِمِائَةِ ضِعْفٍ إلَى أَضْعَافٍ كَثِيرَةٍ، وَإِنْ هَمَّ بِسَيِّئَةٍ فَلَمْ يَعْمَلْهَا؛ كَتَبَهَا اللهُ عِنْدَهُ حَسَنَةً كَامِلَةً، وَإِنْ هَمَّ بِهَا فَعَمِلَهَا؛ كَتَبَهَا اللهُ سَيِّئَةً وَاحِدَةً».
Daga Ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin abin da yake ruwaitowa daga wurin Ubangijinsa - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka -, Ya ce: «Lallai Allah Ya rubuta kyakkyawa da mummuna, sannan ya bayyana haka, wanda ya yi niyyar (aikata) kyakkyawa bai aikatata ba; Allah zai rubuta masa kyakkyawa cikakkiya a wurinSa, idan ya yi niyyar yinta sai ya aikatata; Allah zai rubutata a wurinSa kyakkyawa goma har zuwa ninki ɗari bakwai har zuwa ninkin ba ninkin. Idan kuma ya yi niyyar mummuna bai aikatata ba; Allah zai rubuta ta kyakkyawa cikakkiya a wurinSa, idan kuma ya yi niyyarta sai ya aikatata; Allah zai rubutata mummuna ɗaya».
Bukhari da Muslim Suka ruwaito shi a cikin litattafansu da wannan lafazinDarajaIngantacce ne
Sharhi

Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa Allah Ya ƙaddara kyawawa da munana, sannan Ya bayyanawa Mala'iku biyu yaya zasu rubuta su: Wanda ya yi nufin ya aikata kykkyawa za'a rubuta masa kyakkyawa ɗaya ko da bai aikatashi ba, idan ya aikatashi, to, za a ninkashi da tamkarsa goma zuwa ninki ɗari bakwai, zuwa ninki da yawa, ƙarin yana kasancewa ne da gwargwadan abin da ke cikin zuciya na ikhlasi da ƙetarewar amfani da makamancin hakan. Wanda ya yi nufin aikata mummuna sannan ya barshi saboda Allah, za a rubuta masa kykkyawa, idan ya barshi don shagaltuwa da barinsa, tare da rashin aikata sabubbanta ba za a rubuta masa komai ba, idan ya barshi don gajiyawa daga gareshi za a rubuta masa niyyarsa, idan ya aikatata za a rubuta masa mummuna ɗaya.

Fa’idoji
  1. Bayanin falalar Allah mai girma ga wannan al'ummar wajen ninka kyawawa da kuma rubutasu a wurinsa, da rashin ninka munana.
  2. Muhimmancin niyya a cikin ayyuka da kuma tasirinta.
  3. Falalar Allah - Mai girma da ɗaukaka - da saukinsa da kyutatawarsa cewa wanda ya yi nufin kyakkywa bai aikatashi ba, to, Allah Zai rubutashi a matsayin kykkyawa.
Madogara

صحيح البخاري (8/ 103) (6491). صحيح مسلم (1/ 118) (131). التحفة الربانية في شرح الأربعين حديثًا النووية (ص85). شرح الأربعين النووية، لابن عثيمين (ص368). فتح القوي المتين في شرح الأربعين وتتمة الخمسين، للعباد (ص125). فتح الباري، لابن حجر (11/ 324).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
Kaɗaita Allah cikin sunayenSa da siffofinSa

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com