Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa dukkan mumini zai tsaya a gaban Allah a ranar lahira shi kaɗai, kuma cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Zai yi magana da shi ba tare da wani wasiɗa ba, kuma babu wani tafinta a tsakaninsu wanda zai fassara zancen, sai ya yi duba ɓangaren dama da hagu saboda tsananin firgici, wataƙila zai samu hanyar da zai gudu a cikinta dan ya tsira daga wutar dake gabansa. Idan ya yi duba a ɓangaren da ke damansa ba zai ga komai ba sai abinda ya aikata na aiki na gari Idan ya yi duba a hagunsa ba zai ga komai ba sai abinda ya gabatar na mummunan aiki, idan ya duba gabansa ba zai ga komai ba sai wuta, kuma babu abinda zaisa shi kauce mata dan babu makawa daga wucewa akan siraɗi. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Ku sanya kariya tsakaninku da wuta da sadaka da aiki na gari, koda da wani sassauƙan abu ne kamar rabin dabino.
- Kwaɗaitarwa akan sadaka koda dan kadan ne, da ɗabi'antuwa da ɗabi'u ababen yabo, da mu'amala da sauƙi da tausasan zance.
- Kusancin Allah - Maɗaukakin sarki - ga bawanSa ranar lahira, dan babu wani shamaki ko wasiɗa ko tafinta a tsakaninsu, to mumini ya kiyayi saɓawa umarnin Ubangijinsa.
- Yana kamata ga mutum kada ya wulaƙanta abinda zai yi sadaka da shi koda ƙarami ne, domin shi kariya ne daga wuta.
صحيح البخاري (9/ 148) (7512). صحيح مسلم (2/ 703) (1016). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين. بهجة الناظرين، لسليم الهلالي (1/ 476). نزهة المتقين، مجموعة من الباحثين (1/ 370). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (2/ 201). بهجة قلوب الأبرار، عبد الرحمن آل سعدي (ص181).