Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya labarta cewa Allah idan Ya so bawanSa mumini; mai biyayya ga umarninSa mai nisantar hane-hanenSa sai Ya kira (Mala’ika) Jibril: Lallai cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Yana son wane to ka so shi. Sai shugaban mala'iku (Mala’ika) Jibril - aminci ya tabbata agare shi - ya so shi, sai Jibril yayi kira a cikin mala'ikun sama: Lallai cewa Ubangijinku Yana son wane to ku so shi, sai waɗanda ke sama su so shi, sannan a sanya masa karɓuwa a cikin zukatan muminai da soyayya da kuma karkata gare shi da kuma yarda da shi. Idan Allah Ya ki wani bawanSa sai Ya kira Jibril: Lallai cewa Ni ina ƙin wane to ka ƙi shi, sai (Mala’ika) Jibril ya ƙishi, sannan Jibril yayi kira a cikin waɗanda ke cikin sama: Lallai Ubangijinku Yana ƙin wane to ku ƙishi; sai su ƙishi, sannan a sanya masa baƙin jini da ƙiyayya a cikin zukatan muminai.
- Abu Muhammad Ibnu Abi Jamrah ya ce: A cikin gabatar da umarni da hakan ga (mala'ika) Jibril kafin waninsa cikin mala'iku akwai bayyanar da girman matsayinsa a wurin Allah - Maɗaukakin sarki - akan waninsa daga cikinsu.
- Wanda Allah Ya so shi to halittun dake cikin sama da ƙasa zasu so shi, wanda Allah Ya ƙishi to halittun dake cikin sama da ƙasa zasu ƙishi.
- Sindi ya ce: Faɗinsa (za'a sanya masa karɓuwa a cikin ƙasa), ba ya lazimtar gamewa, kai hakan akan gwargwadan abinda Allah Ya yi nufi ne na karɓuwa a doron ƙasa, ta yaya alhali ƙiyayyar mutanen banza ga zaɓaɓɓun mtane sananniya ce.
- Kwaɗaitarwa akan cika ayyukan alheri akan saɓanin nau'ikansu farillansu da sunnoninsu, da kuma gargaɗarwa daga saɓo da kuma bidi'o'i; domin cewa su masu sabbaba zato ne na fushi.
- Ibnu Hajar ya ce: Kuma ana fahimta daga gare shi cewa soyayyar zukatan mutane alamar soyayyar Allah ce, abinda ke cikin jana’iza yana ƙarfafa shi: "Kune shaidun Allah a doron ƙasa".
- Ibnul Arabi al-Malaki ya ce: Kawai ana nufi da waɗanda ke cikin ƙasa wanda ya san shi daga cikinsu ne kawai banda wanda bai san shi ba, baima taɓa jinsa ba.
صحيح البخاري (4/ 111) (3209). صحيح مسلم (4/ 2030) (2637). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (3/ 268). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 355). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (6/ 308). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 455).