Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Mafi soyuwar garuruwa a wurin Allah sune masallatansu, kuma mafi ƙin garuruwa a wurin Allah sune kasuwanninsu».
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa mafi soyuwar gurare a wurin Allah - Mai girma da ɗaukaka - sune masallatan garuruwan; domin su wuraran ayyukan biyayya ga Allah ne, kuma ginshiƙansu akan tsoron Allah ne.
Kuma mafi ƙin garuruwa a wajen Allah sune kasuwanninsu; domin cewa galibi guri ne na algus da yaudara da riba da rantse-rantse akan ƙarya, da saɓa alƙawari, da bijirewa ambatan Allah.
Fa’idoji
Alfarmar masallatai da gurarensu; domin su gidajen da ake ambatan Allah da yawa ne a cikinsu.
Kwaɗaitarwa akan lazimtar masallatai, da yawan kaikawo zuwa garesu, dan neman soyayyar Allah - Maɗaukakin sarki - da yardarSa, da kuma ƙaranta kaikawo zuwa ga kasuwanni, sai dan buƙata; dan nisanta daga faɗawa cikin sabubban ƙiyayyar (Allah).
Imam Nawawi ya ce: Masallatai gurare ne na saukar rahama, kasuwanni kuwa kishiyarsu ne.
Madogara
صحيح مسلم (1/ 464) (671).
نزهة المتقين، لمجموعة من الباحثين (2/ 1250).
بهجة الناظرين، لسليم الهلالي (3/ 305).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (6/ 655).
كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (21/ 526).
Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com