Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Wani bawa ba zai suturta wani bawa a duniya ba sai Allah Ya suturta shi a ranar Alƙiyama

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «لَا يَسْتُرُ عَبْدٌ عَبْدًا فِي الدُّنْيَا إِلَّا سَتَرَهُ اللهُ يَوْمَ الْقِيَامَةِ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wani bawa ba zai suturta wani bawa a duniya ba sai Allah Ya suturta shi a ranar Alƙiyama".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa wani musulmi ba zai suturta ɗan uwansa musulmi ba a cikin wani al'amari daga al'amura, sai Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya suturta shi a ranar alƙiyama; sakayya tana daga jinsin aiki, kuma suturcewar Allah gare shi zai zama da suturcewar laifukansa da saɓonsa daga yaɗasu ga ma'abota taron alƙiyama, zai iya kasancewa da barin yi masa hisabi akansu da kuma anbata masa su.

Fa’idoji
  1. Halaccin rufawa musulmi asiri idan ya aikata wani saɓo, tare da yin inkari akansa da kuma yi masa nasiha, da tsoratar da shi Allah, amma idan ya kasance daga ma'abota sharri da ɓarna ne masu bayyana saɓo da fasiƙanci, to cewa shi ba ya kamata a rufa musu asiri; domin rufa musu asiri zai sa su ƙarfin hali akan saɓo, kawai ana ɗaga al'amarinsa ne zuwa ga hukuma, koda a hakan akwai anbatansa; domin cewa shi mai bayyanar da fasiƙancinsa ne da kuma saɓonsa.
  2. Kwaɗaitarwa a kan rufa asirin kurakuren wasu.
  3. Daga fa'idojin rufa asiri: Bada dama ga mai yin zunubi ya yi tinani kuma ya tuba zuwa ga Allah; domin bayyanar da aibuka da al'aurori yana daga yayata alfasha, kuma yana ɓata yanayin zamantakewa, kuma yana ruɗar mutane da aikata su.
Madogara

صحيح مسلم (4/ 2002) (2590). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 329). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 255). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (4/ 533). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (3/ 14).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
Kaɗaita Allah cikin sunayenSa da siffofinSa

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com