Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana bayanin Allah maɗaukaki Yana sakkowa a kowanne dare zuwa sama makusanciya lokacin da ɗaya bisa uku na dare ya saura, yana kwaɗaitar da bayinSa a kan su roƙe shi, shi kuma zai amsawa wanda ya roƙe Shi, yana zaburar da su a kan su tambaye Shi abin da suke so, Shi kuma zai ba wanda ya tambaye Shi, yana kiransu da su roƙi gafararSa daga zunubansu Shi kuma yana gafartawa bayinSa muminai.
- Falalar ɗaya bisa ukun ƙarshe na dare da Sallah da Addu’a da neman gafara a lokacin.
- Ya kamata ga mutum a lokacin da ya ji wannan Hadisi ya kasance yana da tsananin kwaɗayin ribatar lokutan amsar Addu’a.
صحيح البخاري صحيح البخاري (2/ 53) (1145). صحيح مسلم (1/ 521) (758). الإفصاح عن معاني الصحاح، ليحيى بن هبيرة (6/ 195).