An zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da wasu ribatattu daga (ƙabilar) Hawazin, sai ga shi a cikinsu akwai wata mace tana neman ɗanta, sai ga shi ta samu wani yaron da ta ɗauke shi sai ta shayar da shi saboda cutuwa da tayi ta hanyar taruwar nono a cikin hantsarta, sai ta samu ɗanta a cikin ribatattu sai ta ɗauke shi, sai ta ɗanfara shi a cikinta ta shayar da shi, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya cewa sahabbansa: Shin yanzu kuna zatan cewa wannan matar zata jefa ɗanta a cikin wuta? Muka ce: Ba zata jefa shi da yardarta ba har abada. Sai ya ce: Allah Ya fi jin tausayin bayinSa daga wannan matar da ɗanta.
- Rahamar Allah mai yalwa ce ga bayinSa, kuma Shi Yana nufin alheri da aljanna garesu, da kuma tsira daga wuta.
- Fa'idantuwa daga abubuwan dake faruwa da kuma alaƙanta su a kan fadakarwa da kuma koyarwa.
- Yana kamata ga mumini ya zama mai kyakkyawan zato ga Allah, kuma kada ya yanke ƙauna tare da tsoron Allah da kuma tabbata akan AddininSa, domin Shi - tsarki ya tabbatar maSa - Ma'abocin rahama ne mayalwaciya.
صحيح البخاري (8/ 8) (5999). صحيح مسلم (4/ 2109) (2754). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 380). تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص284).