Daga Anas - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan dayanku ya yi alwala kuma ya sanya huffinsa to ya yi sallah da su, kuma ya yi shafa akansu, sannan kada ya ciresu in ya so sai dai saboda janaba".
Dar Al-Kutni ne Ya Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa idan musulmi ya sanya huffinsa bayan ya yi alwala, sannan ya kari (hadasi) bayan nan kuma ya yi nufin alwala, to yana da damar yin shafa akansu idan ya yi nufin hakan, kuma ya yi sallah da su kada ya ciresu a wani sanannen lokaci, sai dai idan ya samu janaba to cire huffin ya wajaba a gare shi saboda yin wanka.
Fa’idoji
Shafa akan huffi ba ta halatta sai dai idan an sanya huffin bayan cikar alwala.
Tsawan lokacin shafa ga mazauni: Shafa yini da dare, matafiyi kuma: Yini uku da dararensu.
Shafa akan huffi yana keɓantar ƙaramin hadasi ne banda babba, amma hadasi babba to shafa tare da shi ba ya halatta, kai babu makawa sai an cire huffin da kuma wanke ƙafafuwan.
An so yin sallah da takalmi da kuma huffi da makancinsu dan saɓawa Yahudawa, hakan idan sun kasance masu tsarki, kuma babu cutar da masu yin sallah da su, ko (cutar da) masallaci kamar masallacin da aka shinfiɗa masa shinfiɗu to ba za’a yi sallah da su ba.
Akwai sauƙi da sawwaƙawa ga wannan al'ummar a (lamarin) shafa akan huffi.
Madogara
سنن الدارقطني (1/ 376) (781).
توضيح الأحكام مِن بلوغ المرام، لعبد الله البسام (1/ 274).
سبل السلام شرح بلوغ المرام، للصنعاني (1/ 86).
Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com