Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

SHAFA A KAN HUFFI DA MAKAMANTANSA

Hadisai 9

Ka barsu don na shigar da su suna da tsarki

عَنْ المُغِيرَةِ رضي الله عنه قَالَ: كُنْتُ مَعَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فِي سَفَرٍ، فَأَهْوَيْتُ لِأَنْزِعَ خُفَّيْهِ، فَقَالَ: «دَعْهُمَا، فَإِنِّي أَدْخَلْتُهُمَا طَاهِرَتَيْنِ» فَمَسَحَ عَلَيْهِمَا.
Daga Mugira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a wata tafiya, sai na sunkuyo don in cire masa huffi, sai ya ce: "Ka barsu don na shigar da su suna da tsarki" sai ya yi shafa akansu.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance a daya daga tafiye-tafiyensa sai ya yi alwala, lokacin da ya isa wanke kafafuwa sai Mugira dan Shu'uba - Allah Ya yarda dashi - ya mika hannayensa dan ya cire abinda ke saman kafar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - na kuffi dan wanke kafafuwansa, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Ka barsu kada ka cire su, ni na shigar da kafafuwamna a cikin kuffin alhali ni ina da tsarki (Alwala). Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi shafa akan kuffinsa, maimakon wanke kafafuwa kenan.

Fa’idoji
  1. Halaccin shafa akan kuffi yana kasancewa ne a lokacin alwala na karamin kari, amma wanka dan babban kari (janaba, al’ada) babu makawa daga wanke kafafuwa.
  2. shafa yana kasancewa ne sau daya da shudar da hannu mai danshi akan saman kuffin banda kasansa.
  3. An shardanta shafa akan kuffi ya zama ya sanyasu bayan ya yi cikakkiyar alwala ya wanke kafafuwansa da ruwa, kuma kuffin ya zama mai tsarki, mai suturta bigiren farillar na kafa, kuma shafarsu ya zama a karamin kari ne ba a janaba ba ko abinda yake wajabta wanka ba, kuma shafar ta zama a kayyadajjen lokaci a shari'ance shi ne yini da dare ga mazaunin gari, matafiyi kuma kwana uku da dararensu.
  4. Ana kiyasta dukkanin abinda yake suturta kafafuwa akan kuffi na jaurabi da wasunsu, to shafa akansu yana halatta.
  5. Kyakkyawan dabi'un Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da koyarwarsa, inda ya hana Mugira ciresu, ya kuma bayyana masa dalili: Cewa shi ya shigar da su suna tsarki; dan ransa ya natsu, ya kuma san hukuncin.
Madogara

صحيح البخاري (1/ 52) (206). صحيح مسلم (1/ 230) (274). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، لعبد الله البسام (ص50). الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (1/ 36). خلاصة الكلام شرح عمدة الأحكام، لفيصل آل مبارك (ص27).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Na kasance tare da annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya kai zuwa jujin wasu mutane, sai ya yi fitsari a tsaye,

عَنْ حُذَيْفَةَ رضي الله عنه قَالَ: كُنْتُ مَعَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَانْتَهَى إِلَى سُبَاطَةِ قَوْمٍ، فَبَالَ قَائِمًا، فَتَنَحَّيْتُ فَقَالَ: «ادْنُهْ» فَدَنَوْتُ حَتَّى قُمْتُ عِنْدَ عَقِبَيْهِ فَتَوَضَّأَ فَمَسَحَ عَلَى خُفَّيْهِ.
Daga Huzaifa - Allah Ya yarda da shi - ya ce: "Na kasance tare da annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya kai zuwa jujin wasu mutane, sai ya yi fitsari a tsaye, sai na yi nesa, sai ya ce: "ka kusanto" sai na kusanto har na tsaya daura da maƙyangymansa sai ya yi alwala sai ya yi shafa akan kuffinsa biyu.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Huzaifa Dan Yaman - Allah Ya yarda da su - yana bada labarin cewa shi ya kasance tare da annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya so ya yi fitsari, sai ya shiga jujin wasu mutane; shi ne gurin da ake zubar da tsummokara da sharar da ake sharewa a cikin gidaje, sai ya yi fitsari alhali shi yana tsaye, ya kasance mafi yawancin al'adarsa shi ne ya yi fitsari a zaune. Sai Huzaifa ya yi nesa da shi, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce masa: Ka kusanto, sai Huzaifa ya kusanto gare shi har ya tsaya a bayansa daura da ƙarshen diga-digansa; dan ya zama kamar kariya gare shi daga kallonsa a wannan halin. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi alwala, lokacin wanke ƙafafuwansa biyu, sai ya wadatu da shafa akan kuffinsa biyu - su ne abinda ake ɗaurawa a ƙafa na fata mara kauri da makamancinta kuma yana zama mai suturce idan sawu - kuma bai ciresu ba.

Fa’idoji
  1. Halaccin shafa akan kuffi biyu.
  2. Halaccin yin fitsari a tsaye da sharaɗin kada wani fitsarin ya same shi.
  3. Yadda annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agre shi - ya nemi juji, shi ne bola da shara domin cewa su a galibi masu sauƙi ne fitsari ba zai dawowa mai yin fitsarin ba.
Madogara

صحيح البخاري (1/ 54) (224). صحيح مسلم (1/ 228) (273). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام (ص51). تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، لابن عثيمين (1/ 61).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Ya kasance yana umartarmu idan mun kasance a halin tafiya ko matafiya cewa kada mu cire huffinanmu kwanaki uku da dararensu sai dan janaba, amma bahaya da fitsari da bacci (to a'a)

عَنْ زِرِّ بْنِ حُبَيْشٍ قَالَ: أَتَيْتُ صَفْوَانَ بْنَ عَسَّالٍ المُرَادِيَّ، أَسْأَلُهُ عَنِ المَسْحِ عَلَى الخُفَّيْنِ، فَقَالَ: مَا جَاءَ بِكَ يَا زِرُّ؟ فَقُلْتُ: ابْتِغَاءَ العِلْمِ، فَقَالَ: إِنَّ المَلاَئِكَةَ لَتَضَعُ أَجْنِحَتَهَا لِطَالِبِ العِلْمِ؛ رِضًا بِمَا يَطْلُبُ، فَقُلْتُ: إِنَّهُ حَكَّ فِي صَدْرِي المَسْحُ عَلَى الخُفَّيْنِ بَعْدَ الغَائِطِ وَالبَوْلِ، وَكُنْتَ امْرَأً مِنْ أَصْحَابِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَجِئْتُ أَسْأَلُكَ: هَلْ سَمِعْتَهُ يَذْكُرُ فِي ذَلِكَ شَيْئًا؟ قَالَ: نَعَمْ، كَانَ يَأْمُرُنَا إِذَا كُنَّا سَفْرًا أَوْ مُسَافِرِينَ أَلَّا نَنْزِعَ خِفَافَنَا ثَلاَثَةَ أَيَّامٍ وَلَيَالِيهِنَّ إِلَّا مِنْ جَنَابَةٍ، لَكِنْ مِنْ غَائِطٍ وَبَوْلٍ وَنَوْمٍ، فَقُلْتُ: هَلْ سَمِعْتَهُ يَذْكُرُ فِي الهَوَى شَيْئًا؟ قَالَ: نَعَمْ، كُنَّا مَعَ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فِي سَفَرٍ فَبَيْنَا نَحْنُ عِنْدَهُ إِذْ نَادَاهُ أَعْرَابِيٌّ بِصَوْتٍ لَهُ جَهْوَرِيٍّ: يَا مُحَمَّدُ، فَأَجَابَهُ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَلَى نَحْوٍ مِنْ صَوْتِهِ: «هَاؤُمُ» وَقُلْنَا لَهُ: وَيْحَكَ اغْضُضْ مِنْ صَوْتِكَ، فَإِنَّكَ عِنْدَ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، وَقَدْ نُهِيتَ عَنْ هَذَا، فَقَالَ: وَاللَّهِ لاَ أَغْضُضُ، قَالَ الأَعْرَابِيُّ: المَرْءُ يُحِبُّ القَوْمَ وَلَمَّا يَلْحَقْ بِهِمْ، قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «المَرْءُ مَعَ مَنْ أَحَبَّ يَوْمَ القِيَامَةِ»، فَمَا زَالَ يُحَدِّثُنَا حَتَّى ذَكَرَ بَابًا مِنْ قِبَلِ المَغْرِبِ مَسِيرَةُ عَرْضِهِ، أَوْ يَسِيرُ الرَّاكِبُ فِي عَرْضِهِ أَرْبَعِينَ أَوْ سَبْعِينَ عَامًا.
Daga Zirr Dan Hubaish ya ce: Na zo wurin Sufwan bn Assal al-Muradi - Allah Ya yarda da shi - ina tambayarsa game da shafa akan huffi, sai ya ce: Meke tafe da kai ya Zir? Sai na ce: Dan neman ilimi, sai ya ce: Lallai Mala'iku suna shimfiɗa fukafukansu ga mai neman ilimi, dan yarda da abinda yake nema, sai na ce: Lallai shafa akan huffi bayan gayaɗi da bawali ya sosu a cikin zuciyata, kai kuma mutum ne daga cikin sahabban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai na zo ina tambayarka: Shin ka ji shi yana faɗin wani abu a cikin hakan? Ya ce: Eh, Ya kasance yana umartarmu idan mun kasance a halin tafiya ko matafiya cewa kada mu cire huffinanmu kwanaki uku da dararensu sai dan janaba, amma bahaya da fitsari da bacci (to a'a), sai na ce: Shin ka ji shi yana faɗin wani abu a sha'anin soyayya? ya ce: Eh, mun kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a halin tafiya lokacin muna wurinsa sai wani balaraben ƙauye ya kira shi da babbar murya: Ya Muhammad, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya amsa masa gwargwadan muryarsa: «Haum» kuma mukace da shi: Kaicanka ka ƙanƙanta muryarka, lallai kai kana wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -:, alhali an hanaka wannan, sai ya ce: Wallahi bazan ƙanƙar da muryata ba, balaraben ƙauyen ya ce: Mutum yana son mutane amma bai risku da su ba, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: ya ce: «Mutum yana tare da wanda ya so a ranar alƙiyama» bai gushe ba yana zantar da mu har sai da ya ambaci wata ƙofa a ɓangaren yamma, tafiyar faɗinta, ko mahayi zai yi tafiya a faɗinta tsawon shekara arba'in ko saba'in.
Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad Suka ruwaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Zir bn Hubaish ya zo wurin Safwan bn Assal - Allah Ya yarda da shi -, yana tambayarsa game da shafa akan huffi, sai Safwan ya ce: Meke tafe da kai ya Zir? sai ya ce: Dan neman ilimi, sai ya ce: Lallai mala'iku suna shimfiɗa fukafukansu ga mai neman ilimi; dan yarda da girmamawa ga abin da mai neman ilimi yake aikatawa, sai Zir ya ce: Lallai shafa akan huffi bayan gayaɗi ko fitsari ya yi kai kawo a cikin zuciyata, alhali kai kana daga cikin sahabban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - shi ya sa nazo ina tambayarka shin ka ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya faɗi wani abu a kan haka? Safwan ya ce: Eh, ya kasance yana umartarmu idan mun kasance matafiya kada mu cire huffunanmu tsawon kwana uku da dararensu saboda hadasi ƙarami, kamar gayaɗi da fitsari da bacci, sai dai saboda janaba kawai, to ya wajaba a cire, sai na ce: Shin ka ji shi ya faɗi wani abu game da so? Ya ce: Eh, mun kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin wata tafiya mun kasance muna wurinsa sai ga wani balaraben ƙauye ya kira shi da babbar murya: Ya Muhammad, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya amsa masa da babbar murya kusa da muryarsa: Zo, sai mukace masa: Kaicanka ka ƙanƙar da muyarka, kaifa kana wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, alhali an hanaka ɗaga murya a wurinsa. Saboda kakkausan halinsa sai ya ce: Wallahi ba zan ƙanƙar da muryar ba, sai balaraben ƙauyen ya ce: Ya Manzon Allah, mutum yana son mutane nagari amma bai yi irin aikinsu ba? Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Mutum yana tare da wanda ya so a ranar alƙiyama, Zir ya ce: Safwan bai gushe ba yana zantar da mu har sai da ya ambaci wata ƙofar tuba a ɓangaren Sham, Allah Ya halicceta ranar halittar sammai da ƙasa, mahayi zai yi tafiya a faɗinta tsawon shekara arba'in ko saba'in, kuma ba za'a kulleta ba har sai rana ta ɓullo ta yammacinta.

Fa’idoji
  1. Falalar neman ilimi, da girman matsayin mai neman ilimi, da taruwar mala'iku saboda shi.
  2. Bayanin kwaɗayin Tabi'ai akan neman ilimi daga sahabbai - Allah Ya yarda da su -.
  3. Halaccin shafa akan huffi, da kuma adadin kwanakinsa, yini uku da dararensu ga matafiyi, mazaunin gida kuma yini ɗaya da darensa.
  4. Shafa akan Huffi tana kasancewa ne a ƙaramin hadasi kadai.
  5. Halaccin mai tambaya ya nemi malami ya faɗa masa dalilinsa, shin nassi ne ko kuma kafa hujja ne da kuma ijtihadinsa, kuma ya wajaba akan malami kada ya ji damuwa akan hakan.
  6. Ladabi tare da malamai da mutanen kirki, da ƙanƙar da murya a majalisan ilimi.
  7. Sanar da jahili kyawawan ladabi da ƙa'idodjin Tarbiya.
  8. Kwaɗaitarwa akan koyi da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a haƙurinsa, da kyawawan ɗabi'unsa, da yadda yake magana da mutane gwargwadon ilimunsu da kuma hankulansu.
  9. Al-Mubarakafuri ya ce: Kaɗai Annabi - tsira da aminci su tabbata agare shi - ya ɗaga muryarsa ne ta hanyar tausaya masa dan kada aikinsa ya ɓaci saboda faɗinSa - Allah Maɗaukakin sarki -: {Kada ku ɗaga muryarku sama da muryar Annabi}; sai ya yi masa uzuri saboda jahilcinsa, kuma Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ɗaga muryarsa ne har ta zama kwatankwacin muryarsa (shi mutumin) ko sama da ita dan yawan tausayinsa.
  10. Kwaɗaitarwa akan zama da salihai da kusantowa zuwa garesu da kuma son su.
  11. Nawawi ya ce: Kasancewarsa tare da su ba ya hukunta matsayinsa da sakamakonsa ya zama kwatankwacin nasu ta kowanne ɓangare.
  12. Buɗe ƙofar fata da kwaɗayi da albishir da tsira, da tausasawa a cikin wa'azi.
  13. Yalwar rahamar Allah - Mai girma da ɗaukaka -, da buɗewarsa ƙofar tuba.
  14. Kwaɗaitarwa akan gaggawar tuba da yi wa zuciya hisabi da komawa zuwa ga Allah - Maɗaukakin sarki -.
Madogara

سنن الترمذي (5/ 505) (3535). سنن ابن ماجه (1/ 302) (478). مسند أحمد (30/ 18) (18095). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 36). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (1/ 107). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 57). المعجم الوسيط (2/ 968).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Cewa naga Manzon Allah-Tsira da Amincin Allah su Tabbata a gareshi- yana Karanta ta kuma yana sanya yana shafar saman Huffinsa

عن عبد خير، عن علي رضي الله عنه ، قال: لو كان الدين بالرأي لكان أسفل الخُفِّ أولى بالمسح من أعلاه، وقد «رأيت رسول الله صلى الله عليه وسلم يمسح على ظَاهر خُفَيْهِ».
Daga Abd Khair, daga Ali -Allah ya yarda da shi- ya ce: da ace Addini Ra'ayi nre da qasan Huffi ya dacewa da shafa daga Samansa, kuma haqiqa: "Cewa naga Manzon Allah-Tsira da Amincin Allah su Tabbata a gareshi- yana Karanta ta kuma yana sanya yana shafar saman Huffinsa"
Abu Daud Ya Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Ali, Allah ya yarda da shi, yana cewa idan da za a dauki addini da hankali ba tare da yadawa ba, to da kasan silifa ya fi dacewa a share fiye da na sama. Saboda kasan silifa yana ratsa kasa, da datti da datti, saboda haka ya fi kyau a goge daga gefen tunani, amma Sharia ta zo akasin haka, don haka ya zama dole ayi aiki da ita kuma a bar ra'ayin da ya saba wa matanin. , da kuma cewa ya taba ganin Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya shafa saman silifas din, da abin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yarda Ga hankali a gefe guda; Domin idan ya goge gindin silifas din da ruwa, hakan zai haifar masa da dauda, don haka ya sanya shafa a sama don cire kurar da ta makale a ciki. Saboda bayyanar khuff shine wanda aka gani, don haka shafawar tasa ta fara.

Madogara

سنن أبي داود، تأليف: سليمان بن الأشعث السِّجِسْتاني، تحقيق: محمد محيي الدين عبد الحميد، الناشر: المكتبة العصرية، صيدا. مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، تأليف: علي بن سلطان القاري، الناشر: دار الفكر، الطبعة: الأولى، 1422هـ. مشكاة المصابيح، تأليف: محمد بن عبد الله التبريزي، تحقيق : محمد ناصر الدين الألباني، الناشر: المكتب الإسلامي، الطبعة: الثالثة، 1985م. تسهيل الإلمام بفقه الأحاديث من بلوغ المرام، تأليف: صالح بن فوزان بن عبد الله الفوزان، الطبعة: الأولى، 1427 هـ - 2006 م. توضيح الأحكام مِن بلوغ المرام، تأليف: عبد الله بن عبد الرحمن بن صالح البسام، الناشر: مكتبة الأسدي، مكة المكرّمة الطبعة: الخامِسَة، 1423 هـ - 2003 م. سبل السلام شرح بلوغ المرام، تأليف: محمد بن إسماعيل بن صلاح الصنعاني، الناشر: دار الحديث الطبعة: بدون طبعة وبدون تاريخ. شرح سنن أبي داود، تأليف: عبد المحسن بن حمد بن عبد المحسن العباد، نسخة الإلكترونية.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Manzon Allah SAW ya aika Tawagar Yaqi, sai Sanyi ya same su, yayin da suka isowa Manzon Allah SAW sai ya Umarce su da suyi shafa kan Rawunansu da Huffin su

عن ثوبان رضي الله عنه ، قال: «بعث رسول الله صلى الله عليه وسلم سَرِيَّةً، فأصابهم البَرْد فلما قَدِموا على رسول الله صلى الله عليه وسلم أمَرَهُم أن يَمْسَحوا على الْعَصَائِب والتَّسَاخِين».
Daga Sauban -Allah ya yarda da shi- ya ce: "Manzon Allah SAW ya aika Tawagar Yaqi, sai Sanyi ya same su, yayin da suka isowa Manzon Allah SAW sai ya Umarce su da suyi shafa kan Rawunansu da Huffin su"
Abu Daud Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Sahabbansa su hadu da kafirai, kuma a lokacin da suke tafiya yana da wuya su cire rawani da kirji saboda yanayin sanyi, lokacin da suka zo Madina, sai suka gaya wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - game da wannan , kuma ya basu izini su goge rawani da pumice, ko fata ce, ko ulu, ko riguna, don sauƙaƙawa da sauƙaƙa Wajibi ne akan waɗanda ake tuhuma, kuma wannan shekarar ce mai tsayayyar halarta da tafiya tare da uzuri kuma ba tare da uziri.

Madogara

سنن أبي داود، تأليف: سليمان بن الأشعث السِّجِسْتاني، تحقيق: محمد محيي الدين عبد الحميد، الناشر: المكتبة العصرية، صيدا. مسند الإمام أحمد، تأليف: أحمد بن محمد بن حنبل، تحقيق: شعيب الأرناؤوط وغيره، الناشر: مؤسسة الرسالة، الطبعة: الأولى، 1421هـ. صحيح أبي داود - الأم، للألباني، نشر: مؤسسة غراس للنشر والتوزيع، الكويت، الطبعة: الأولى، 1423هـ - 2002 م. توضيح الأحكام مِن بلوغ المرام، تأليف: عبد الله بن عبد الرحمن بن صالح البسام، الناشر: مكتبة الأسدي، مكة المكرّمة، الطبعة الخامِسَة، 1423 هـ - 2003 م. فتح ذي الجلال والإكرام، شرح بلوغ المرام، تأليف: محمد بن صالح بن محمد العثيمين، الناشر: المكتبة الإسلامية، تحقيق: صبحي بن محمد رمضان، وأُم إسراء بنت عرفة. منحة العلام في شرح بلوغ المرام، تأليف: عبد الله بن صالح الفوزان، الناشر: دار ابن الجوزي، الطبعة الأولى ، 1427 هـ - 1431 هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Idan dayanku ya yi alwala kuma ya sanya huffinsa to ya yi sallah da su, kuma ya yi shafa akansu, sannan kada ya ciresu in ya so sai dai saboda janaba

عَنْ أَنَسٍ رضي الله عنه أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «إِذَا تَوَضَّأَ أَحَدُكُمْ وَلَبِسَ خُفَّيْهِ فَلْيُصَلِّ فِيهِمَا، وَلْيَمْسَحْ عَلَيْهِمَا ثُمَّ لَا يَخْلَعْهُمَا إِنْ شَاءَ إِلَّا مِنْ جَنَابَةٍ».
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan dayanku ya yi alwala kuma ya sanya huffinsa to ya yi sallah da su, kuma ya yi shafa akansu, sannan kada ya ciresu in ya so sai dai saboda janaba".
Dar Al-Kutni ne Ya Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa idan musulmi ya sanya huffinsa bayan ya yi alwala, sannan ya kari (hadasi) bayan nan kuma ya yi nufin alwala, to yana da damar yin shafa akansu idan ya yi nufin hakan, kuma ya yi sallah da su kada ya ciresu a wani sanannen lokaci, sai dai idan ya samu janaba to cire huffin ya wajaba a gare shi saboda yin wanka.

Fa’idoji
  1. Shafa akan huffi ba ta halatta sai dai idan an sanya huffin bayan cikar alwala.
  2. Tsawan lokacin shafa ga mazauni: Shafa yini da dare, matafiyi kuma: Yini uku da dararensu.
  3. Shafa akan huffi yana keɓantar ƙaramin hadasi ne banda babba, amma hadasi babba to shafa tare da shi ba ya halatta, kai babu makawa sai an cire huffin da kuma wanke ƙafafuwan.
  4. An so yin sallah da takalmi da kuma huffi da makancinsu dan saɓawa Yahudawa, hakan idan sun kasance masu tsarki, kuma babu cutar da masu yin sallah da su, ko (cutar da) masallaci kamar masallacin da aka shinfiɗa masa shinfiɗu to ba za’a yi sallah da su ba.
  5. Akwai sauƙi da sawwaƙawa ga wannan al'ummar a (lamarin) shafa akan huffi.
Madogara

سنن الدارقطني (1/ 376) (781). توضيح الأحكام مِن بلوغ المرام، لعبد الله البسام (1/ 274). سبل السلام شرح بلوغ المرام، للصنعاني (1/ 86).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Manzon Allah SAW ya sanya kwana Uku da daraensu ga mafiyi, da kuma Kwana xaya da Darensa ga mazaunin gida

عن شريح بن هانئ، قال: أتيتُ عائشة أسألها عن المسح على الخُفَّين، فقالت: عَلَيْكَ بِابْنِ أبِي طالب، فَسَلْهُ فإِنَّه كان يُسَافِرُ مع رسول الله صلى الله عليه وسلم فسألناه فقال: «جَعَلَ رسول الله صلى الله عليه وسلم ثَلَاثَةَ أَيَّامٍ وَلَيَالِيَهُنَّ للمسافر، ويوما وليلة للمُقيم».
L: Na zo wurin A’isha don na tambaye ta game da silifa a kan silifa, sai ta ce: Lallai ku yi da Ibn Abi Dalib, don haka ya tambaye shi, saboda yana tafiya tare da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi aminci - don haka muka tambaye shi, sai ya ce: “Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya yi masa kwana uku. Ga mazaunin».
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Shurayh bin Hani daya ne daga cikin sahabban Ali - Allah ya yarda da shi - kuma ya zo wajen Ali - Allah ya yarda da shi - yana tambaya game da lokacin shafa kan safa, kuma wannan binciken ya kasance ne bayan mahaifiyarmu A’isha, Allah ku yarda da ita, sai ku tura shi zuwa ga Ali. Saboda shi masani ne a sunnar shafa, sai ya ce: (Mun tambaye shi game da shafa) wannan shi ne: game da tsawon lokacinsa, kuma shafawa rauni ne na jika a hannu ga memba, kuma silifas din takalmin fata ne wanda yana rufe duga-dugai, kuma sock shine nadewar mutum na kowane abu wanda ya kasance gashi ko ulu, mai kauri ko na bakin ciki, zuwa sama. Ana ɗaukar diddige don sanyi, kuma hukuncin daidai yake da takalmin yayin shafa Ali bin Abi Dalib - Allah ya yarda da shi - ya ba su amsa: (Kwana uku da dararensu ga matafiyi, da yini daya da dare ga mazaunin.) A ciki akwai hujja ga abin da mafi yawan malamai suka tafi a kansa lokacin binciken ta kwana uku ga matafiyi, da rana daya da dare ga mazaunin, amma tsawon lokacin ya karu ga matafiyin. Saboda ya fi cancanta da izini fiye da mazaunin don wahalar tafiya.

Madogara

صحيح مسلم، مسلم بن الحجاج القشيري النيسابوري، تحقيق محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، الطبعة: 1423 هـ. توضيح الأحكام مِن بلوغ المرام، عبد الله بن عبد الرحمن البسام، مكتبة الأسدي، مكة المكرّمة، الطبعة: الخامِسَة 1423هـ، 2003م.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Manzon Allah yayi rangwame ga Matafiyi kwana Uku da dararensu, Mazaunin gida kuma Kwana xaya da dare

عن أبي بكرة نُفيع بن الحارث الثقفي رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم أنه رَخَّصَ للمسَافر ثلاثةَ أيَّام ولَيَالِيهنَّ، وللمُقِيم يوما وليلة، إذا تطَهَّر فَلَبِسَ خُفَّيه: أَن يَمسَحَ عليهما.
Daga Abu Bakarata Nufai'i Bin Al-harith Al-thaqafi -Allah ya yarda da shi- daga Manzon Allah SAW cewa Manzon Allah yayi rangwame ga Matafiyi kwana Uku da dararensu, Mazaunin gida kuma Kwana xaya da dare
Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Al-Dar Al-Kutni Ya Rawaito shiDarajaHasan ne
Madogara

صحيح ابن خزيمة، محمد بن إسحاق بن خزيمة النيسابوري، المكتب الإسلامي، بيروت، الطبعة: 1390هـ. صحيح ابن حبان بترتيب ابن بلبان، محمد بن حبان بن أحمد بن حبان، تحقيق: شعيب الأرنؤوط، مؤسسة الرسالة، بيروت، الطبعة: الثانية 1414هـ، 1993م. سنن الدارقطني،أبو الحسن علي بن عمر الدارقطني، تحقيق: شعيب الارنؤوط وآخرون، نشر: مؤسسة الرسالة، بيروت، لبنان، الطبعة: الأولى، 1424هـ، 2004م. تسهيل الإلمام بفقه الأحاديث من بلوغ المرام، صالح بن فوزان بن عبد الله الفوزان، اعتنى بإخراجه عبدالسلام بن عبد الله السليمان، الرسالة، بيروت، الطبعة: الأولى 1427هـ، 2006م. توضيح الأحكام مِن بلوغ المرام، عبد الله بن عبد الرحمن البسام، مكتبة الأسدي، مكة المكرّمة، الطبعة: الخامِسَة 1423هـ، 2003م. منحة العلام في شرح بلوغ المرام، عبد الله صالح الفوزان، دار ابن الجوزي، الطبعة: الأولى 1428هـ، 1432هـ. مشكاة المصابيح، محمد ناصر الدين الألباني، نشر: المكتب الإسلامي، بيروت، الطبعة: الثالثة 1985م.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
8 cikin 9
Hadisai 9
  1. Ka barsu don na shigar da su suna da tsarki
  2. Na kasance tare da annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya kai zuwa jujin wasu mutane, sai ya yi fitsari a tsaye,
  3. Ya kasance yana umartarmu idan mun kasance a halin tafiya ko matafiya cewa kada mu cire huffinanmu kwanaki uku da dararensu sai dan janaba, amma bahaya da fitsari da bacci (to a'a)
  4. Cewa naga Manzon Allah-Tsira da Amincin Allah su Tabbata a gareshi- yana Karanta ta kuma yana sanya yana shafar saman Huffinsa
  5. Manzon Allah SAW ya aika Tawagar Yaqi, sai Sanyi ya same su, yayin da suka isowa Manzon Allah SAW sai ya Umarce su da suyi shafa kan Rawunansu da Huffin su
  6. Idan dayanku ya yi alwala kuma ya sanya huffinsa to ya yi sallah da su, kuma ya yi shafa akansu, sannan kada ya ciresu in ya so sai dai saboda janaba
  7. Manzon Allah SAW ya sanya kwana Uku da daraensu ga mafiyi, da kuma Kwana xaya da Darensa ga mazaunin gida
  8. Manzon Allah yayi rangwame ga Matafiyi kwana Uku da dararensu, Mazaunin gida kuma Kwana xaya da dare
  9. Na ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi fitsari, sannan ya yi alwala kuma ya yi shafa akan huffinsa

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com