Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Mafi tsananin azaba a wurin Allah a ranar Alkiyama wadanda suke kwaikwayon halittar Allah

عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المُؤمنينَ رضي الله عنها قَالَتْ: دَخَلَ عَلَيَّ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، وَقَدْ سَتَرْتُ سَهْوَةً لِي بِقِرَامٍ فِيهِ تَمَاثِيلُ، فَلَمَّا رَآهُ هَتَكَهُ وَتَلَوَّنَ وَجْهُهُ وَقَالَ: «يَا عَائِشَةُ، أَشَدُّ النَّاسِ عَذَابًا عِنْدَ اللهِ يَوْمَ الْقِيَامَةِ الَّذِينَ يُضَاهُونَ بِخَلْقِ اللهِ» قَالَتْ عَائِشَةُ: «فَقَطَعْنَاهُ فَجَعَلْنَا مِنْهُ وِسَادَةً أَوْ وِسَادَتَيْنِ».
Daga Aisha Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce : Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shigo wurina, hakika na rufe jarkata da wani labule a jikinsa akwai hotuna, lokacin da ya gan shi sai ya yaye shi, fuskarsa ta janza ya ce : "Ya A'isha, Mafi tsananin azaba a wurin Allah a ranar Alkiyama wadanda suke kwaikwayon halittar Allah" A'isha ta ce: "Sai muka yanke shi sai muka maida shi shinfida ko shinfidu biyu".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiga dakinsa ga A'isha - Allah Ya yarda da ita - sai ya sameta ta rufe jarkarta karama wacce take sanya kayanta a ciki da wani yanki a jikinsa akwai hotunan masu rayuka, sai launin fuskarsa ya canja dan fushi saboda Allah sai ya cire shi, ya ce: Mafi tsananin azaba a ranar Alkiyama wadanda suke kamanta halittar Allah da hotunansu. A'isha ta ce: sai muka maida shi shinfida ko shinfidu biyu.

Fa’idoji
  1. Hana abin ki a lokacin ganinsa da rashin jinkiri a hakan, muddin dai babu wata barna mafi girma a hakan.
  2. Azabar ranar Alkiyama tana banbanta a tsanani gwargwadan girman zunubi.
  3. Yin hoton abubuwa masu rai yana daga manyan zanubai.
  4. Yana daga hikimomin haramta hoto kamanceceniya da halittar Allah - Madaukakin sarki -, duk daya ne mai hoton ya yi nufin kamanceceniya ne ko bai yi nufi ba.
  5. Kwadayin shari'a akan kiyaye dukiyoyi ta hanyar fa'idantuwa daga gare su bayan an nisantarsu abinda ya haramta a cikinsu.
  6. Hani akan kera zanen abubuwa masu rai akan kowanne yanayi ya kasance, koda sun kasance a wulakance ne.
Madogara

صحيح البخاري (7/ 168) (5954). صحيح مسلم (3/ 1668) (2107). القول المفيد على كتاب التوحيد، لابن عثيمين (2/ 442). الملخص في شرح كتاب التوحيد، لصالح الفوزان (ص399). الجديد في شرح كتاب التوحيد، للقرعاوي (ص441). كتاب التوحيد لمحمد بن عبد الوهاب (ص138).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
Kaɗaita Allah cikin Rububiyya

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com