عن أبي ذر الغفاري رضي الله عنه مرفوعاً: "ما الكرسي في العرش إلا كحلقة من حديد ألقيت بين ظهري فلاة من الأرض".
Daga Abu Dhar al-Ghafari - yardar Allah ta tabbata a gare shi - da sarkar makamai: "Kujerar tana cikin karaga sai dai kamar zoben karfe da aka jefa a tsakanin bayana na masu gidan."
Ibnu Abi Shaiba ne ya rawaito a Babin Magana kan Al'arshi - Al-Thahabi Ya Rawaito shi a Babin Uluwwi (Daukakar Allah bisa Bayinsa(DarajaIngantacce ne
Sharhi
Yana fada - Allah ya kara masa tsira da aminci - a cikin hadisin Abu Dharr cewa kujera, tare da karfi da girma dangane da karaga, kamar zoben karfe ne wanda aka sanya shi a cikin jejin kasa mai fadi. Wannan yana nuna girman Mahaliccin sa da kuma cikakken ikon sa.
Madogara
1- فتح المجيد شرح كتاب التوحيد، مطبعة السنة المحمدية، القاهرة، مصر، الطبعة: السابعة، 1377هـ - 1957م.
2- القول المفيد على كتاب التوحيد، دار ابن الجوزي، المملكة العربية السعودية، الطبعة: الثانية, محرم، 1424ه.
3- الملخص في شرح كتاب التوحيد، دار العاصمة الرياض، الطبعة: الأولى 1422هـ- 2001م.
4- الجديد في شرح كتاب التوحيد، مكتبة السوادي، جدة، المملكة العربية السعودية، الطبعة: الخامسة، 1424هـ - 2003م.
5- التمهيد لشرح كتاب التوحيد، دار التوحيد، تاريخ النشر: 1424هـ.
6- شرح العقيدة الطحاوية، المؤلف: محمد ناصر الدين الألباني، الناشر: المكتب الإسلامي – بيروت الطبعة: الثانية، - 1414ه.
7- العرش وما روي فيه، المؤلف: محمد بن عثمان ابن أبي شيبة العبسي، تحقيق: محمد بن حمد الحمود، الناشر: مكتبة المعلا – الكويت، الطبعة الأولى، 1406ه.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ عَبْدِ اللهِ بنِ مَسْعُودٍ رضي الله عنه قال: سَأَلْتُ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: أَيُّ الذَّنْبِ أَعْظَمُ عِنْدَ اللهِ؟ قَالَ: «أَنْ تَجْعَلَ لِلهِ نِدًّا وَهُوَ خَلَقَكَ» قُلْتُ: إِنَّ ذَلِكَ لَعَظِيمٌ، قُلْتُ: ثُمَّ أَيُّ؟ قَالَ: «وَأَنْ تَقْتُلَ وَلَدَكَ؛ تَخَافُ أَنْ يَطْعَمَ مَعَكَ» قُلْتُ: ثُمَّ أَيُّ؟ قَالَ: «أَنْ تُزَانِيَ حَلِيلَةَ جَارِكَ».
Daga Abdullahi dan Mas'ud - Allah ya yarda da shi - ya ce: Na tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Wanne zunubine mafi girma a wurin Allah? ya ce:
" Ka sanyawa Allah kishiya alhali Shi Ya halicceka" Na ce: Lallai wannan mai girmane, na ce: Sannan wanne? Ya ce: "Ka kashe danka; dan tsoron ya ci tare da kai". Na ce: Sannan wanne? ya ce: "Ka yi zina da matar makocinka".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Antambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - daga mafi girman zunubai sai ya ce: Mafi girmansu babbar shirka, ita ce ka sanya tamka ko kini ga Allah a AllantakarSa ko UbangidantakarSa ko sunayenSa da siffofinSa, wannan laifin Allah - Madaukakin sarki - ba ya gafartashi saida tuba, idan mai aikata shi ya mutu akansa to shi madawamine a cikin wuta. Sannan mutum ya kashe dansa dan tsoron ya ci tare da shi, kashe rai kuwa haramun ne, saidai zunubinsa yana girmama idan wanda aka kashe din yana da alaka ta jini da wanda ya yi kisan, kuma zunubinsa yana girmama yayin da manufar wanda ya yi kisan ta zama dan tsoron ya yi tarayya da wanda aka kashe din ne a arzzikin Allah. Sannan mutum ya yi zina da matar makocinsa shi ne ya yi kokarin rudar da matar makocinsa har ya yi zina da ita ta mika wuya gare shi . Zina haramun ce , saidai zunubinta yana girmama idan wacce aka yi zinar da ita matar makoci ce wanda shari'a ta yi wasicci da kyautatawa zuwa gareshi da yi masa kirki da kayauta zama da shi.
Fa’idoji
- Fifikon zunubai a girma, kamar yadda ayyuka na gari ma suna fifko a falala.
- Mafi girman zunubai: Yi wa Allah - Madaukakkin sarki - shirka, sannan kashe da don tsoron ya ci tare da kai, sannan ka yi zina da matar makocinka.
- Arziki yana hannun Allah tsarki ya tabbatar maSa, Ya yi lamuni da azurta ababen halitta.
- Girman hakkin makwabci, kuma cutar da shi, shi ne mafi girman zunubi daga cutar da waninsa.
- Mahalicci Shi ne macancanci ga bauta, Shi kadai Yake ba Shi da abokin tarayya.
Madogara
صحيح البخاري (6/ 18) (4477).
صحيح مسلم (1/ 90) (86).
شرح النووي على مسلم (2/ 79).
فتح ذي الجلال والاكرام بشرح بلوغ المرام، لابن عثيمين (6/ 288).
توضيح الأحكام من بلوغ المرام، للبسام (7/ 335).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المُؤمنينَ رضي الله عنها قَالَتْ: دَخَلَ عَلَيَّ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، وَقَدْ سَتَرْتُ سَهْوَةً لِي بِقِرَامٍ فِيهِ تَمَاثِيلُ، فَلَمَّا رَآهُ هَتَكَهُ وَتَلَوَّنَ وَجْهُهُ وَقَالَ: «يَا عَائِشَةُ، أَشَدُّ النَّاسِ عَذَابًا عِنْدَ اللهِ يَوْمَ الْقِيَامَةِ الَّذِينَ يُضَاهُونَ بِخَلْقِ اللهِ» قَالَتْ عَائِشَةُ: «فَقَطَعْنَاهُ فَجَعَلْنَا مِنْهُ وِسَادَةً أَوْ وِسَادَتَيْنِ».
Daga Aisha Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce : Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shigo wurina, hakika na rufe jarkata da wani labule a jikinsa akwai hotuna, lokacin da ya gan shi sai ya yaye shi, fuskarsa ta janza ya ce : "Ya A'isha, Mafi tsananin azaba a wurin Allah a ranar Alkiyama wadanda suke kwaikwayon halittar Allah" A'isha ta ce: "Sai muka yanke shi sai muka maida shi shinfida ko shinfidu biyu".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiga dakinsa ga A'isha - Allah Ya yarda da ita - sai ya sameta ta rufe jarkarta karama wacce take sanya kayanta a ciki da wani yanki a jikinsa akwai hotunan masu rayuka, sai launin fuskarsa ya canja dan fushi saboda Allah sai ya cire shi, ya ce: Mafi tsananin azaba a ranar Alkiyama wadanda suke kamanta halittar Allah da hotunansu. A'isha ta ce: sai muka maida shi shinfida ko shinfidu biyu.
Fa’idoji
- Hana abin ki a lokacin ganinsa da rashin jinkiri a hakan, muddin dai babu wata barna mafi girma a hakan.
- Azabar ranar Alkiyama tana banbanta a tsanani gwargwadan girman zunubi.
- Yin hoton abubuwa masu rai yana daga manyan zanubai.
- Yana daga hikimomin haramta hoto kamanceceniya da halittar Allah - Madaukakin sarki -, duk daya ne mai hoton ya yi nufin kamanceceniya ne ko bai yi nufi ba.
- Kwadayin shari'a akan kiyaye dukiyoyi ta hanyar fa'idantuwa daga gare su bayan an nisantarsu abinda ya haramta a cikinsu.
- Hani akan kera zanen abubuwa masu rai akan kowanne yanayi ya kasance, koda sun kasance a wulakance ne.
Madogara
صحيح البخاري (7/ 168) (5954).
صحيح مسلم (3/ 1668) (2107).
القول المفيد على كتاب التوحيد، لابن عثيمين (2/ 442).
الملخص في شرح كتاب التوحيد، لصالح الفوزان (ص399).
الجديد في شرح كتاب التوحيد، للقرعاوي (ص441).
كتاب التوحيد لمحمد بن عبد الوهاب (ص138).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أنس بن مالك رضي الله عنه: أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَمُعَاذٌ رَدِيفُهُ عَلَى الرَّحْلِ قَالَ: «يَا مُعَاذُ بْنَ جَبَلٍ»، قَالَ: لَبَّيْكَ يَا رَسُولَ اللهِ وَسَعْدَيْكَ، قَالَ: «يَا مُعَاذُ»، قَالَ: لَبَّيْكَ يَا رَسُولَ اللهِ وَسَعْدَيْكَ، ثَلَاثًا، قَالَ: «مَا مِنْ أَحَدٍ يَشْهَدُ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ وَأَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اللهِ صِدْقًا مِنْ قَلْبِهِ إِلَّا حَرَّمَهُ اللهُ عَلَى النَّارِ»، قَالَ: يَا رَسُولَ اللهِ، أَفَلَا أُخْبِرُ بِهِ النَّاسَ فَيَسْتَبْشِرُوا؟ قَالَ: «إِذًا يَتَّكِلُوا». وَأَخْبَرَ بِهَا مُعَاذٌ عِنْدَ مَوْتِهِ تَأَثُّمًا.
Daga Anas Ɗan Malik Allah Ya yarda da shi Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, Mu’azu yana bayan shi a kan jaki, Ya ce: Ya Mu’azu Ɗan Jabal!!)). Ya ce: Amsawarka bayan Amsawarka Ya Ma’aikin Allah da taimakawa bayan taimakawa, Ya ce; Ya "Mu’azu" Ya ce: Amsawarka bayan Amsawarka Ya Ma’aikin Allah da taimakawa bayan taimakawa sau uku [ya faɗa], ya ce: Babu wani mutum da zai shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma (Annabi) Muhammad Manzon Allah ne da gaske daga zuciayarsa sai wuta ta haramta a gareshi)). Ya ce: Ya Ma’aikin Allah shin ba na ba mutane labarin nan ba domin su yi murna? Ya ce: Za su saki jiki.
Sai Mu’azu ya ba da labarin bayan rasuwar Ma’aikin Allah gudun kada ya ɓoye ilimi.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Mu’azu Ɗan Jabal Allah Ya yadda da shi, ya kasance yana bayan Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a kan abin hawa na dabbarsa, sai ya kira shi Ya Mu’azu, ya maimaita kiran na sa har sau uku, domin ƙarfafawa da Kuma muhimmancin abin zai faɗa masa.
A duka kiran Mu’azu Allah Ya yarda da shi yana amsa masa da cewa; Amsawarka bayan Amsawarka Ya Ma’aikin Allah da da farincin hakan bayan farinciki, Wato na amsa maka Ya Ma’aikin Allah bayan amsawa, kuma na nemi farinciki da wannan amsawa.
Sai Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ba shi bayanin babu wani mutum da zai shaida babu abin bautawa da cancanta sai Allah. Wato; Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammad Ma’aikin Allah ne da gaske daga zuciyarsa ba ƙarya ba, idan har ya mutu a wannan hali, to, Allah Ya haramta masa wuta.
Sai Mu’azu Allah Ya yarda da shi ya tambayi Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a kan ya baiwa mutane labari domin su yi farin ciki su yi wa juna bushara ta alheri?
Sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ji tsoron kada su saki jiki da hakan, su ƙaranta ayyuka.
Mu’azu bai ba da wannan bayanin ba sai dab da rasuwarsa, don tsoron kada ya faɗa cikin masu ɓoye ilimi.
Fa’idoji
- Tawalu’un Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ta yadda ya goya Mu’azu a bayansa a kan dabbarsa.
- Tsarin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi wurin karantarwa, yadda ya maimaita kira ga Mu’azu don jan hankali a kan abin da zai faɗa.
- Daga sharuɗɗan shaidawa: Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, kuma [Annabi] Muhammad Ma’aikin Allah ne, shi ne ; Mai faɗarta ya kasance mai gaskiya da yaƙini ba mai ƙarya ba ko kuma shakka.
- Ma’abota Tauhidi ba sa dawwama a wutar jahannama, ko da sun shigeta saboda zunubasu, za a fitar da su daga cikinta bayan an tsaftace su.
- Falalar kalamar shahada ga wanda ya faɗeta da gaske.
- Halaccin barin karantar da wani karatu a wani lokaci idan hakan zai janyo wata ɓarna.
Madogara
صحيح البخاري (1/ 37) (128).
صحيح مسلم (1/ 61) (32).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين (1/ 377).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 487).
كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (6/ 496).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ زَيْدِ بْنِ خَالِدٍ الجُهَنِيِّ رضي الله عنه أَنَّهُ قَالَ: صَلَّى لَنَا رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ صَلَاةَ الصُّبْحِ بِالْحُدَيْبِيَةِ عَلَى إِثْرِ سَمَاءٍ كَانَتْ مِنَ اللَّيْلَةِ، فَلَمَّا انْصَرَفَ أَقْبَلَ عَلَى النَّاسِ، فَقَالَ: «هَلْ تَدْرُونَ مَاذَا قَالَ رَبُّكُمْ؟» قَالُوا: اللهُ وَرَسُولُهُ أَعْلَمُ، قَالَ: «أَصْبَحَ مِنْ عِبَادِي مُؤْمِنٌ بِي وَكَافِرٌ، فَأَمَّا مَنْ قَالَ: مُطِرْنَا بِفَضْلِ اللهِ وَرَحْمَتِهِ، فَذَلِكَ مُؤْمِنٌ بِي وَكَافِرٌ بِالْكَوْكَبِ، وَأَمَّا مَنْ قَالَ: بِنَوْءِ كَذَا وَكَذَا، فَذَلِكَ كَافِرٌ بِي وَمُؤْمِنٌ بِالْكَوْكَبِ».
Daga Zaidu Dan Khalid AlJuhani - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi mana sallar Asuba a Hudaibiyya a bayan (ruwan daya sauka) a wannan daren da ya wuce, lokacin da ya sallame sai ya juya ya fuskanto mutane, ya ce: "Shin kun san mai Ubangijinku Ya ce?" Suka ce: Allah da Manzonsane mafi sani, ya ce: "Mumini da kafiri sun wayi gari daga bayina"
Amma wanda ya ce: An yi mana ruwa da falalar Ubangiji da rahamarSa, to wannan ya yi imani da Ni, kuma ya kafircewa taurari. Amma wanda ya ce: Da tauraro kaza da kaza, to wannan ya kafirce mi Ni kuma ya yi imani da taurari".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi sallar Asuba a Hudaibiyya - ita wata alkaryace kusa da Makka bayan wani ruwa da ya sauka a wannan daren, Lokacin da ya yi sallama ya idar da sallarasa sai ya fuskanto mutane da fuskarsa, sai ya tambayesu: Shin kun san me Ubangijinku - Mai girma da daukaka - Ya ce ? Sai suka amsa masa: Allah da ManzonSane mafi sani. Sai ya ce: Lallai Allah - Madaukakin sarki - Ya bayyana cewa mutane a lokacin saukar ruwa sun kasu gida biyu: Bangare daya sun yi imani da Allah - Madaukakin sarki -, daya bangaren kuma suka kafircewa Allah - Madaukakin sarki -; Amma wanda ya ce: An yi mana ruwa da falalar Allah da rahamarSa, ya danganta saukar ruwa ga Allah - Madaukakin sarki -; to wannan ya yi imani da Allah Mahalicci Mai jujjuya al'amura a cikin halittarsa , kuma ya kafircewa taurari. To amma wanda ya ce: An yi mana ruwa da tauraro iri kaza da kaza; to wannan ya kafircewa Allah kuma ya yi imani da taurari, shi karamin kafarcine ta inda ya danganta saukar ruwa ga taurari; kuma Allah bai sanya shi wani sababi na shari'a ba ko na kaddara, Amma wanda ya danganta saukar ruwa da waninsa daga fararrun abubuwa na kasa ga motsin taurari a bullowarsu da faduwarsu yana mai kudire cewa su ne masu aikin na hakika to shi kafirine kafirci babba.
Fa’idoji
- Anso fadin: An yi mana ruwa da falalar Allah da rahamarSa bayan saukar ruwa.
- Wanda ya danganta ni'imar saukar ruwa da wasunsu ga taurari a halitta da samarwa to shi kafirine kafirci babba, idan ya danganta shi akan cewa shi wani sababi ne to shi kafirine kafirci karami domin cewa shi ba sababi ne na shari'a ko na gani ba.
- Lallai ni'ima tana kasancewa sababi na kafirci idan an butulce, kuma tana zama sababi na imani idan an gode.
- Hani akan fadin: "An yi mana ruwa da tauraro kaza da kaza", koda an nufi lokaci; dan toshe kafar shirka.
- Wajabcin damfarar zuciya ga Allah - Madaukakin sarki - a jawo ni'imomi da tunkude bala’o’i.
Madogara
صحيح البخاري (1/ 169) (846)، صحيح مسلم (1/ 83) (71)، البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (2/ 484)، المفهم لما أشكل من تلخيص كتاب مسلم (1/ 260).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ قَتَادَةَ رحمه الله قال: حَدَّثَنَا أَنَسُ بْنُ مَالِكٍ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ أَنَّ رَجُلًا قَالَ: يَا نَبِيَّ اللهِ كَيْفَ يُحْشَرُ الْكَافِرُ عَلَى وَجْهِهِ؟ قَالَ: «أَلَيْسَ الَّذِي أَمْشَاهُ عَلَى الرِّجْلَيْنِ فِي الدُّنْيَا قَادِرًا عَلَى أَنْ يُمْشِيَهُ عَلَى وَجْهِهِ يَوْمَ الْقِيَامَةِ؟» قَالَ قَتَادَةُ: بَلَى وَعِزَّةِ رَبِّنَا.
Daga Katada - Allah Ya yi masa rahama - ya ce: Anas Dan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya zantar damu cewa wani mutum ya ce: Ya Annabin Allah ya za’a tashi kafiri akan fuskarsa? Ya ce: " Shin wanda ya tafiyar da shi akan kafafuwa biyu a duniya bai zama yana da iko akan ya tafiyar da shi akan fuskarsa ranar Alkiyama ba?"Katada ya ce: Eh na rantse da buwayar Ubangijinmu.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
An tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Ya za'a tashi kafiri akan fuskarsa a ranar Alkiyama ?! sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce; Shin yanzu wanda ya tafiyar da shi akan kafafuwa biyu a duniya bai zama mai iko akan ya tafiyar da shi akan fuskarsa a ranar Alkiyama ba?! Allah Mai ikone akan dukkan komai.
Fa’idoji
- Wulakantar kafiri a ranar Alkiyama kuma zai yi tafiya akan fuskarsa.
Madogara
صحيح البخاري (8/ 109) (6523)، صحيح مسلم (4/ 2161) (2806)، الإفصاح عن معاني الصحاح (5/200)، فتح الباري (11/382)، عمدة القاري شرح صحيح البخاري (23/ 105)، البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (43/ 454).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أَبِي العَبَّاسِ، عَبْدِ الله بْنِ عَبَّاسٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا قَالَ: كُنْت خَلْفَ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَوْمًا، فَقَالَ: «يَا غُلَامِ! إنِّي أُعَلِّمُك كَلِمَاتٍ: احْفَظِ اللَّهَ يَحْفَظْكَ، احْفَظِ الله تَجِدْهُ تُجَاهَكَ، إذَا سَأَلْتَ فَاسْأَلِ اللهَ، وَإِذَا اسْتَعَنْتَ فَاسْتَعِنْ بِاَللهِ، وَاعْلَمْ أَنَّ الأُمَّةَ لَوْ اجْتَمَعَتْ عَلَى أَنْ يَنْفَعُوكَ بِشَيْءٍ لَمْ يَنْفَعُوكَ إلَّا بِشَيْءٍ قَدْ كَتَبَهُ اللَّهُ لَكَ، وَإِنِ اجْتَمَعُوا عَلَى أَنْ يَضُرُّوكَ بِشَيْءٍ لَمْ يَضُرُّوكَ إلَّا بِشَيْءٍ قَدْ كَتَبَهُ اللَّهُ عَلَيْكَ؛ رُفِعَتِ الأَقْلَامُ، وَجَفَّتِ الصُّحُفُ».
وَفِي رِوَايَةِ غَيْرِ التِّرْمِذِيِّ: «احْفَظِ اللهَ تَجِدْهُ أَمَامَكَ، تَعَرَّفْ إلَى اللهِ فِي الرَّخَاءِ يَعْرِفْكَ فِي الشِّدَّةِ، وَاعْلَمْ أَنَّ مَا أَخْطَأَكَ لَمْ يَكُنْ لِيُصِيبَكَ، وَمَا أَصَابَك لَمْ يَكُنْ لِيُخْطِئَكَ، وَاعْلَمْ أَنَّ النَّصْرَ مَعَ الصَّبْرِ، وَأَنْ الفَرَجَ مَعَ الكَرْبِ، وَأَنَّ مَعَ العُسْرِ يُسْرًا».
Daga Abul Abbas, Abdullahi ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Na kasance a bayan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - wata rana, sai ya ce: «Ya kai yaro! zan sanar da kai wasu kalmomi: Ka kiyaye Allah Zai kiyayeka, ka kiyaye Allah zaka same shi a daura da kai, idan za ka yi roƙo, to, ka roƙi Allah, idan za ka nemi taimako, to, ka nemi taimakon Allah, ka sani cewa da ace al'umma za su taru a kan su amfaneka da wani abu, ba za su amfaneka ba sai da abin da tabbas Allah Ya rubuta maka, da za su taru kuma a kan su cutar da kai da wani abu, ba za su cutar da kai ba, sai da abin da tabbas Allah Ya rubuta a kanka; an ɗauke alƙaluma kuma takardu sun bushe». A cikin wata riwayar da ba ta Tirmizi ba: «Ka kiyaye Allah zaka same shi a gabanka, ka nemi sanin Allah a lokacin wadata zai taimakeka a cikin tsanani, ka sani cewa abin da ya kuskure maka bai zama zai sameka ba, abin da kuma ya sameka bai zama zai kuskure maka ba, ka sani cewa nasara tana tare da haƙuri, kuma yaye baƙin ciki yana tare da farin ciki, kuma sauƙi yana tare da tsanani».
Tirmizi da Ahmad ne sun rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - yana ba da labarin cewa ya kasance yana ƙarami yana haye tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Zan sanar da kai wasu al'amura da wasu abubuwan da Allah zai amfanar da kai da su: Ka kiyaye Allah ta hanyar kiyaye umarninSa da nisantar hane-hanenSa, ta inda Zai sameka a ayyukan biyayya da kusanci, ka da Ya sameka a ayyukan saɓo da zunubai, idan ka aikata haka sakamakonka zai kasance shi ne Allah Zai kiyayeka daga abubuwan ƙi na duniya da lahira, kuma Zai taimakeka a ayyukanka a duk inda ka fuskanta. Idan ka yi nufin roƙon wani abu, to, kada ka roƙi kowa sai Allah, to, domin haƙiƙa Shi Allah Shi kaɗai ne wanda Yake amsawa masu roƙo. Idan ka yi nufin neman taimako, to, kada ka nemi taimakon kowa sai Allah. Kuma ya zama kana da yaƙini cewa wani amfani ba zai sameka ba, ko da mutanen duniya gaba ɗaya sun taru akan amfanarka sai dai abin da Allah Ya rubuta maka, kuma wani abin cutarwa ba zai faru a kanka ba, ko da mutanen duniya gaba ɗaya za su taru a kan cutarka, sai dai abin da Allah Ya ƙaddara shi a kanka. Kuma wannan al'amarin tabbas Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya rubuta maka Ya kuma ƙaddara shi daidai da abin da hikimarSa da saninSa suka hukunta, babu canji ga abin da Allah Ya rubuta shi. Kuma cewa wanda ya kiyaye Allah ta hanyar kiyaye umarninSa da nisantar hane-hanenSa; to Allah - tsarki ya tabbatar maSa - Yana gaban bawa, Yana sanin abin da yake a kansa, kuma zai taimake shi Ya kuma ƙarfafe shi. Kuma lallai mutum idan ya bi Allah a cikin wadata to lallai cewa Allah zai sanya masa yayewa da mafita a lokacin tsanani, kuma kowane bawa ya yarda da abin da Allah Ya ƙaddara masa na alheri da na sharri. Kuma ya lazimci haƙuri a lokacin tsanani da kuma jarrabawa, domin haƙuri mabuɗin yaye baƙin ciki ne, kuma baƙin ciki idan ya yi tsanani sai yayewa tazo daga Allah, kuma cewa tsanani idan ya faru Allah sai Allah Ya biye masa da sauƙi.
Fa’idoji
- Muhimmancin sanar da yara al'amuran addini na tauhidi da ladubba da sauransu.
- Sakamako yana kasancewa daga irin aikin da aka yi.
- Umarni a kan dogaro ga Allah, da tawakkali gare shi ba da waninsa ba, madalla da Shi a matsayin wakili.
- Imani da hukunci da ƙaddara da yarda da shi, kuma Allah Ya ƙaddara kowane abu.
- Wanda ya tozarta umarnin Allah, to, Allah Zai tozarta shi ba kuma zai kiyaye shi ba.
- Bushara mai girma cewa mutum idan tsanani ya same shi to ya saurari sauƙi.
- lallashin bawa a lokacin faruwar musiba, da rasa abin da ake so a cikin faɗinsa: «Ka sani cewa abin da ya sameka bai zama zai kuskureka ba, abin da kuma ya kuskureka to bai zama zai sameka ba» to jumal ta farko bada haƙuri ce a lokacin faruwar wani abin ƙi, ta biyu kuma bada haƙuri a kokacin rasa abin da ake so.
Madogara
سنن الترمذي (4/ 284) (2516).
التحفة الربانية في شرح الأربعين حديثًا النووية (ص42).
شرح الأربعين النووية، لابن عثيمين (ص200).
فتح القوي المتين في شرح الأربعين وتتمة الخمسين، للعباد (ص69).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comKowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com