Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari game da ganawar Allah ga bawanSa mumini ranar alƙiyama, sai ya ce: Za'a kusanto da mumini ranar alƙiyama daga Ubangijinsa sai Ya sanya suturarSa daga ma'abota wurin tsayuwa har ya zama waninsa ba zai yi tsinkaye akan sirrinsa ba, sai ya ce masa: Shin kana sanin zunubi kaza da kaza... Zai tabbatar masa da zunuban da suke tsakanin bawa da UbangijinSa. Sai ya ce: Na'am Eh, ya Ubangiji. Har idan mumini ya firgita ya ji tsoro, sai Tsarki ya tabbatar maSa Ya ce masa: Lallai cewa Ni na suturta su gareka a duniya, kuma cewa Ni na gafartasu gareka a yau, sai a ba shi takardar kyawawan ayyukansa. Amma kafiri da munafuki sai a yi kira a gabn mahalarta: Waɗannan sune waɗanda suka yi wa Ubangijinsu ƙarya, ku saurara tsinuwar Allah ta tabbata akan azzalumai.
- Falalar Allah da rahamarSa ga muminai saboda rufa musu asiri a duniya da lahira.
- Kwaɗaitarwa akan rufawa mumini asiri gwargwadan iko.
- Ayyukan bayi gaba ɗayansu Ubangijin bayi Zai kiyayesu, wanda ya samu alheri to ya godewa Allah, wanda ya samu wanin haka to kada ya zargi kowa sai kansa, kuma shi yana ƙarƙashin Mashi'ar Allah.
- Ibnu Hajar ya ce: Dukkan hadisan sun yi nuni akan cewa masu saɓo cikin muminai a alƙiyama sun kasu gida biyu: Na ɗayansu: Wanda saɓonsa tsakaninsa da Ubanginjinsa ne, sai hadisin Ibnu Umar ya yi nuni akan cewa wannan ɓangaren ya kasu gida biyu: Wani ɓangaren: Saɓonsu zai zama abin suturtawa a duniya, to wannan wanda Allah Zai yi masa sutura ne a alƙiyama shi a mafurtar (hadisn). Wani ɓangaren kuma: Saɓonsu zai zama a bayyane, sai mafhum ɗin sa ya yi nuni akan cewa shi saɓanin haka ne. Bangare na biyu: Wanda saɓonsa tsakanin sa da bayi ne to su sun kasu kashi biyu kuma: Wani ɓangaren: Mummunan ayyukansu sun rinjayi kyawan ayyukansu, to wadannan zasu fada cikin wuta sannan su fita da ceto, wani bangaren kuma: Munanan ayyukansu zasu yi daidai da kyawawan ayyukansu, to wadannan ba zasu shiga aljanna ba har sai sakayya ta faru tsakaninsu.
صحيح البخاري (6/ 74) (4685). صحيح مسلم (4/ 2120) (2768). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (3/ 323). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (7/ 12). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 501). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 390). جامع العلوم والحكم في شرح خمسين حديثا من جوامع الكلم، لابن رجب الحنبلي (1/ 452).