Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

ALAƘA TSAKANIN NAMIJI DA MACE

Hadisai 2

Ya kasance yana cikin hidimar iyalansa, idan lokacin sallah ya yi sai ya fita zuwa ga sallah

عَنِ الأَسْوَدِ بنِ يَزِيدَ قَالَ: سَأَلْتُ عَائِشَةَ مَا كَانَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَصْنَعُ فِي بَيْتِهِ؟ قَالَتْ: كَانَ يَكُونُ فِي مِهْنَةِ أَهْلِهِ -تَعْنِي خِدْمَةَ أَهْلِهِ-، فَإِذَا حَضَرَتِ الصَّلاَةُ خَرَجَ إِلَى الصَّلاَةِ.
Daga al-Aswad Ibnu Yazid ya ce: Na tambayi Nana A'isha abinda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yake yi a cikin gidansa? ta ce: Ya kasance yana cikin hidimar iyalansa, idan lokacin sallah ya yi sai ya fita zuwa ga sallah.
Bukhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

An tambayi Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - game da halin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin gidansa kuma me yake aikatawa? Sai ta ce: Ya kasance mutum ne daga cikin mutane, yana aikata abinda maza suke aikatawa a cikin gidajensu, sai ya kasance a cikin hidimar kansa da iyalansa; yana tatsar nonon akuyarsa, yana ɗinke tufafinsa, yana gyara takalminsa, yana ɗinke gugansa, kuma ya kasance idan lokacin tada sallah ya yi sai ya fita zuwa gareta - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba tare da wani jinkiri ba.

Fa’idoji
  1. Cikar tawali'unsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da kuma kyakkyawan mu'amalarsa ga iyalansa.
  2. Ayyukan duniya yana kamata kada su shagaltar da bawa daga sallah.
  3. Kiyayewar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - akan sallah a cikin farkon lokutanta.
  4. Ibnu Hajar ya ce: A cikinsa akwai kwaɗaitarwa a kan tawali'u da barin girman kai da kuma hidimar iyalai ga namiji.
Madogara

صحيح البخاري (1/ 136) (676). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 660). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (3/ 526). شرح صحيح البخاري، لابن بطال (2/ 296). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 516).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Lallai ni bana gaisawa da mata, kawai maganata ga mata dari kamar maganata ce ga mace daya

عَنْ أُمَيْمَةَ بِنْتِ رُقَيْقَةَ رضي الله عنها أَنَّهَا قَالَتْ: أَتَيْتُ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فِي نِسْوَةٍ مِنَ الْأَنْصَارِ نُبَايِعُهُ، فَقُلْنَا: يَا رَسُولَ اللَّهِ، نُبَايِعُكَ عَلَى أَلَّا نُشْرِكَ بِاللَّهِ شَيْئًا، وَلَا نَسْرِقَ، وَلَا نَزْنِيَ، وَلَا نَأْتِيَ بِبُهْتَانٍ نَفْتَرِيهِ بَيْنَ أَيْدِينَا وَأَرْجُلِنَا، وَلَا نَعْصِيَكَ فِي مَعْرُوفٍ، قَالَ: «فِيمَا اسْتَطَعْتُنَّ، وَأَطَقْتُنَّ» قَالَتْ: قُلْنَا اللَّهُ وَرَسُولُهُ أَرْحَمُ بِنَا، هَلُمَّ نُبَايِعْكَ يَا رَسُولَ اللَّهِ، فَقَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «إِنِّي لَا أُصَافِحُ النِّسَاءَ، إِنَّمَا قَوْلِي لِمِائَةِ امْرَأَةٍ كَقَوْلِي لِامْرَأَةٍ وَاحِدَةٍ، أَوْ مِثْلُ قَوْلِي لِامْرَأَةٍ وَاحِدَةٍ».
Daga Umaimah 'yar Ruƙaiƙah - Allah Ya yarda da ita - cewa ita ta ce: Na zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin wasu mata daga matan Madina, dan mu yi masa caffa, sai muka ce: Ya manzon Allah, zamu yi maka caffa akan kada mu hada Allah da wani abu (a bauta), kada mu yi sata ba, kada mu yi zina, kada mu zo da ƙirƙirarriyar ƙarya da zamu aikata a tsakanin hannayenmu da ƙafafuwanmu, kuma kada mu saɓa maka a wani aikin alheri, ya ce: "A abinda zaku iya da abinda zaku samu ikon yi". Ta ce: Muka ce: Allah da manzonSa ne mafi tausayi garemu, zo mu yi maka caffa ya manzon Allah, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai ni bana gaisawa da mata, kawai maganata ga mata dari kamar maganata ce ga mace daya, ko kwatankwacin magana ga mace ɗaya".
Tirmizi da Nasa'i da Ibnu Majah ne Suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Umaimah 'yar Ruƙaiƙah - Allah Ya yarda da ita -: Cewa ita ta zo wurin annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a tare da ita akwai wasu mata daga matan Madina, zasu yi masa caffa (mubaya’a) akan ba zasu yi wa Allah shirka da wani abu ba, kuma ba zasu yi sata ba, ba zasu yi zina ba, ba zasu zo wa ƙirƙirarriyar ƙaryar ba da zasu aika tsakanin hannayensu da ƙafafuwansu ba, kuma ba zasu saɓa masa a wani aikin alheri ba, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: A cikin abinda zaku iya, kuma kuke da iko, Muka ce: Allah da manzonSa ne mafi jin ƙai da mu, ka zo mu yi maka caffa (mubaya’a) ya manzon Allah da gaisawa hannu da hannu kamar yadda maza suke yi maka, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Lallai ni bana gaisawa da mata hannu da hannu, kawai maganata da mubaya'ata ga mata ɗari kamar maganata ce ga mace ɗaya.

Fa’idoji
  1. Bayanin yadda mubaya'ar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga mata take.
  2. Haramcin gaisawa da mata hannu da hannu banda muharramai.
  3. Hukunci na shari'a an rataya shi ne da iko da kuma yi yadda za'a iya.
Madogara

سنن الترمذي (3/ 247) (1597). سنن النسائي (7/ 149) (4181). سنن ابن ماجه (4/ 128) (2874). ذخيرة العقبى في شرح المجتبى (32/ 263).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com