Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Ya kasance yana cikin hidimar iyalansa, idan lokacin sallah ya yi sai ya fita zuwa ga sallah

عَنِ الأَسْوَدِ بنِ يَزِيدَ قَالَ: سَأَلْتُ عَائِشَةَ مَا كَانَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَصْنَعُ فِي بَيْتِهِ؟ قَالَتْ: كَانَ يَكُونُ فِي مِهْنَةِ أَهْلِهِ -تَعْنِي خِدْمَةَ أَهْلِهِ-، فَإِذَا حَضَرَتِ الصَّلاَةُ خَرَجَ إِلَى الصَّلاَةِ.
Daga al-Aswad Ibnu Yazid ya ce: Na tambayi Nana A'isha abinda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yake yi a cikin gidansa? ta ce: Ya kasance yana cikin hidimar iyalansa, idan lokacin sallah ya yi sai ya fita zuwa ga sallah.
Bukhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

An tambayi Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - game da halin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin gidansa kuma me yake aikatawa? Sai ta ce: Ya kasance mutum ne daga cikin mutane, yana aikata abinda maza suke aikatawa a cikin gidajensu, sai ya kasance a cikin hidimar kansa da iyalansa; yana tatsar nonon akuyarsa, yana ɗinke tufafinsa, yana gyara takalminsa, yana ɗinke gugansa, kuma ya kasance idan lokacin tada sallah ya yi sai ya fita zuwa gareta - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba tare da wani jinkiri ba.

Fa’idoji
  1. Cikar tawali'unsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da kuma kyakkyawan mu'amalarsa ga iyalansa.
  2. Ayyukan duniya yana kamata kada su shagaltar da bawa daga sallah.
  3. Kiyayewar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - akan sallah a cikin farkon lokutanta.
  4. Ibnu Hajar ya ce: A cikinsa akwai kwaɗaitarwa a kan tawali'u da barin girman kai da kuma hidimar iyalai ga namiji.
Madogara

صحيح البخاري (1/ 136) (676). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 660). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (3/ 526). شرح صحيح البخاري، لابن بطال (2/ 296). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 516).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
MATAYENSA TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARESHI DA YANAYIN GIDAN ANNABTA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com