عن عبد الله بن عمر رضي الله عنهما : «أن رسول الله صلى الله عليه وسلم نهى عن الشِّغَارِ».
Daga Abdullahi Dan Umar - Allah ya yarda da shi - zuwa ga Annabi : "Cewa Manzon Allah-Tsira da Amincin Allah su Tabbata a gareshi- ya hana Auren Musanya"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Asalin Daurin Aure cewa baya cika sai anbawa Mace Sadaki, sakamakon abinda zata bayar na bada kanta, don haka Annabi ya hana irin wannan Aure na Jahilliyya, wanda Waliyyan mata suke zaluntarta iyayen gida ma, yadda suke Aurar da su ba tar da Sadaki ba da zzai Mayar musu da amfani zuwa gare su ba, sai dai da abinda zai biya musu bukatar sha'awar su kawai, sai su gabatar da su ga Mazaje, suma da niyyar su Aurar musu da yayansu ba tare da anbada Sadaki ba, to wannan zalunci ne kuma yin iko ne da abunda Allah ya basu na Al'aura ba ta hanyar da Allah ya saukar ba kuma hakan ya kasance Haramun ne kuma in anyi batacce ne.
Madogara
-صحيح البخاري، ط1، تحقيق: محمد زهير بن ناصر الناصر دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، 1422ه.
-صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت.
- الإلمام بشرح عمدة الأحكام للشيخ إسماعيل الأنصاري-مطبعة السعادة-الطبعة الثانية 1392ه.
-تيسير العلام شرح عمدة الأحكام-عبد الله البسام-تحقيق محمد صبحي حسن حلاق- مكتبة الصحابة- الشارقة- الطبعة العاشرة- 1426ه.
-خلاصة الكلام شرح عمدة الأحكام- فيصل بن عبد العزيز بن فيصل ابن حمد المبارك الحريملي النجدي - الطبعة: الثانية، 1412 هـ - 1992 م.
عن علي بن أبي طالب رضي الله عنه «أن النبي صلى الله عليه وسلم نهى عن نكاح المتعة يوم خيبر، وعن لحوم الحُمُرِ الأهلية».
An rawaito daga Ali Bn Abu Dalib -Allah ya yarda da shi- "Cewa Annabi ya hana Auren Mutu'a a Ranar yakin Khaibara, da kuma cin Naman Jakin gida"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara
- صحيح البخاري –الجامع الصحيح-؛ للإمام أبي عبد الله محمد بن إسماعيل البخاري، عناية محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة، الطبعة الأولى، 1422هـ.
- صحيح مسلم؛ للإمام مسلم بن الحجاج، حققه ورقمه محمد فؤاد عبد الباقي، دار عالم الكتب-الرياض، الطبعة الأولى، 1417هـ.
- الإلمام بشرح عمدة الأحكام للشيخ إسماعيل الأنصاري-مطبعة السعادة-الطبعة الثانية 1392ه.
- تيسير العلام شرح عمدة الأحكام-عبد الله البسام-تحقيق محمد صبحي حسن حلاق- مكتبة الصحابة- الشارقة- الطبعة العاشرة- 1426ه.
Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com