عن عقبة بن عامر رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «أَحَقُّ الشُّرُوطِ أَنْ تُوفُوا بِهِ مَا اسْتَحْلَلْتُمْ بِهِ الْفُرُوجَ».
Daga Uƙubah Ibnu Amir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Mafi cancantar sharuɗɗa da za ku cika; su ne wadanda aka halatta muku mata da su.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana bayyana cewa mafi cancantar sharaɗin da za a cika shi ne wanda ya kasance dalili na halatta jin daɗi da mace, su ne sharuɗɗan da suke na halal ga mace ta nema a lokacin ɗaurin aure.
Fa’idoji
Wajibcin cika sharuɗɗa wanda ɗayan ma’aurata ya sa, sai dai sharaɗin da ya haramta halal, ko ya halatta haram.
Cika sharuɗɗan aure ya fi sauran ƙarfi, domin yana matsayin halatta farji ne.
Girman matsayin aure a Musulunci ta yadda ya fi kowanne sharaɗi ƙarfin cikawa.
Madogara
صحيح البخاري (3/ 190) (2721).
صحيح مسلم (2/ 1035) (1418).
الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (2/ 63).
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، لعبد الله البسام (ص573).
Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com