Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

FALALAR AURE

Hadisai 1

Duk wanda yake da iko a cikinku to ya yi aure, domin cewa shi ne yafi rintse ido, kuma ya fi katange farji, wanda ba zai iya ba to na umarce shi da azimi, domin shi kariyane gare shi

عَن عَبْدِ اللَّهِ بنِ مَسْعُودٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: كُنَّا مَعَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقَالَ: «مَنِ اسْتَطَاعَ البَاءَةَ فَلْيَتَزَوَّجْ، فَإِنَّهُ أَغَضُّ لِلْبَصَرِ، وَأَحْصَنُ لِلْفَرْجِ، وَمَنْ لَمْ يَسْتَطِعْ فَعَلَيْهِ بِالصَّوْمِ، فَإِنَّهُ لَهُ وِجَاءٌ».
Daga Abdullahi ɗan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Mun kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: "Duk wanda yake da iko a cikinku to ya yi aure, domin cewa shi ne yafi rintse ido, kuma ya fi katange farji, wanda ba zai iya ba to na umarce shi da azimi, domin shi kariyane gare shi".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kwaɗaitar da wanda yake da iko akan jima'i da ɗawainiyar aure da ya yi aure; domin cewa shi yafi kiyaye gani daga haram, kuma ya fi tsananin katange farjinsa, da kuma hana afkawa cikin alfasha, wanda ba zai iya ɗaukar ɗawainiyar aure ba alhali shi yana mai iko akan jima'i to ya yin azimi domin cewa shi yana yanke sha'awar farji da sharrin maniyyi.

Fa’idoji
  1. Kwaɗayin Musulunci akan sabubban kamewa da kuɓuta daga alfasha.
  2. Kwaɗaitar da wanda ba zai iya ɗaukar nauyin ɗawainiyar aure ba da ya yi azimi; domin cewa shi yana raunana sha'awa.
  3. Ta yadda ya kamanta azimi da kariya; domin kariya (dandaƙa) ita ce kwankwatsa jijiyoyin maraina, da zarar sun tafi sai sha'awar jima'i ta tafi da tafiyarsu, haka nan azimi, shi mai raunana sha'awar jima'i ne.
Madogara

صحيح البخاري (3/ 26) (1905). صحيح مسلم (2/ 1018) (1400). الإلمام بشرح عمدة الأحكام للشيخ ،لإسماعيل الأنصاري (2/ 57). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، لعبد الله البسام (ص565). خلاصة الكلام شرح عمدة الأحكام، لفيصل آل مبارك (ص281).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com