عَنِ ابْنِ عُمَرَ رَضيَ اللهُ عنهما قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «إِذَا جَمَعَ اللهُ الْأَوَّلِينَ وَالْآخِرِينَ يَوْمَ الْقِيَامَةِ يُرْفَعُ لِكُلِّ غَادِرٍ لِوَاءٌ، فَقِيلَ: هَذِهِ غَدْرَةُ فُلَانِ بْنِ فُلَانٍ».
Daga ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan Allah Ya tara mutanen farko da na ƙarshe ranar alƙiyama za'a ɗaga tuta ta dukkan wani mayaufdari, sai a ce: Wannan yaudarar wane ɗan wane ce".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa Allah - Maɗaukakin sarki - idan ya tara mutanen farko dana ƙarshe ranar alƙiyama saboda hisabi, za'a kafawa kowanne maha'incin da bai cika alƙawarin da ya dauka ba tare da Allah ko tare da mutane ba, wata alamar da za'a kunya shi da ita akan ha'incinsa, kuma za’a yi kira akan sa a wannan ranar: Wannan ha'incin wane ɗan wane ne; dan bayyanar da mummunan aikinsa a filin taron alƙiyama.
Fa’idoji
- Haramta yaudara kuma cewa ita tana daga cikin manyan zunubai; domin a cikinta ne wannan narkon mai tsanani yake.
- Yaudarar da aka yi narko a kanta ta ƙunshi dukkan wanda ya amince maka akan jini, ko mutunci, ko sirri, ko dukiya sai ka ha'ince shi, ka kuma saɓawa zatinsa a cikin amanarka.
- AlƘurɗubi ya ce: wannan magana ce daga gare shi zuwa ga larabawa da irin abinda suke aikatawa; domin su sun kasance suna ɗaga farar tuta dan cika alƙawari, suna ɗaga baƙar tuta kuma dan yaudara, dan su zargi mayaudari, sai Hadisin ya hukunta afkuwar irin haka ga mayaudari; dan ya shahara da siffarsa a taron alƙiyama, kuma al’umma da suke a filin alƙiyama su zarge shi.
- Ibnu Hajar ya ce: Kuma a cikinsa mutane za'a kirasu ranar alƙiyama (tare da sunayen) iyayen su; saboda faɗinsa: "Wannan ce yaudarar wane ɗan wane".
Madogara
صحيح البخاري (4/ 104) (3188)
صحيح مسلم (3/ 1359) (1735).
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام (ص745).
الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (2/ 188).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ عَبْدِ اللَّهِ بنِ عُمَرَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُما: أَنَّ امْرَأَةً وُجِدَتْ فِي بَعْضِ مَغَازِي النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ مَقْتُولَةً، فَأَنْكَرَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَتْلَ النِّسَاءِ وَالصِّبْيَانِ.
Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Cewa an samu wata mace a wasu daga yakokin Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi a kashe, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana kashe mata da yara.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ga wata mace an kashe ta a ɗaya daga cikin yake-yake, sai ya yi inkarin kashe mata da kananan yara waɗanda basu isa mafarki ba.
Fa’idoji
- Wanda bai yi yaki ba cikin mata da yara, da wanda ke cikin hukuncinsu na tsofaffi da masu ibada, domin cewa su ba'a kashe su, muddin dai waɗannan basu kasance daga ma'abota ra'ayi da taimako akan yakar musulmai ba, idan sun kasance hakan to za'a kashe su.
- Hani akan kashe mata da yara; domin su ba sa yakar musulmai, abin nufi a yaki a tafarkin Allah - Maɗaukakin sarki - (shi ne) karya karfin mayaka kawai; har Da’awar gaskiya ta kai zuwa ga mutane baki ɗaya.
- Jin kan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - har a fagen yaki.
Madogara
صحيح البخاري (4/ 61) (3014).
صحيح مسلم (3/ 1364) (1744).
الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (2/ 189).
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام (ص746).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أَبِي مُوسَى رضي الله عنه قَالَ: سُئِلَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَنِ الرَّجُلِ يُقَاتِلُ شَجَاعَةً، وَيُقَاتِلُ حَمِيَّةً، وَيُقَاتِلُ رِيَاءً، أَيُّ ذَلِكَ فِي سَبِيلِ اللهِ؟ فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَنْ قَاتَلَ لِتَكُونَ كَلِمَةُ اللهِ هِيَ الْعُلْيَا، فَهُوَ فِي سَبِيلِ اللهِ».
Daga Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - ya ce: An tambayi manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da mutumin da yake yaƙi dan jarumta, (da wanda) yake yaƙi dan ƙabilanci, (da wanda) yake yaƙi dan riya, wanne ne saboda Allah? sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya yi yaƙi dan kalmar Allah ta zama maɗaukakiya, to shi ne sabo da Allah".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
An tambayi annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - daga saɓanin manufofin masu yin yaƙi; wanda ya yi yaƙi dan jarumtaka ko ƙabilanci ko dan aga matsayinsa a cikin mutane ko wanin hakan, wannene saboda Allah? Sai annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda ya yi yaƙi saboda Allah shi ne: Wanda ya yi yaƙi dan kalmar Allah ta zama ita ce maɗaukakiya.
Fa’idoji
- Asali a cikin gyaruwar ayyuka da ɓacinsu (ita ce) niyya da tsarkake aiki saboda Allah.
- Idan manufa daga yaƙi ita ce ɗaukaka kalmar Allah, kuma wata manufar daban abar shara'antawa ta haɗu a cikinsa, kamar samun ganima, to shi ba ya cutarwa.
- Kare maƙiya daga shiga garuruwa da mutuncin mata yana daga yaƙi saboda Allah.
- Falalar da ta zo a cikin mayaƙa tana keɓantuwa ne ga wanda ya yi yaƙi dan kalmar Allah - Maɗaukakin sarki - ta zama ita ce maɗaukakiya.
Madogara
صحيح البخاري (9/ 136) (7458).
صحيح مسلم (3/ 1513) (1904).
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، لعبد الله البسام (ص753).
الإعلام بفوائد عمدة الأحكام، لابن الملقن (10/ 380).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أبي هريرة رضي الله عنه قال: بَعَثَنَا رسول الله صلى الله عليه وسلم في بَعْثٍ، فقال: «إن وجَدْتُم فُلانا وفُلانا» لرجلين من قُرَيْش سَمَّاهُما «فأَحْرِقُوهُمَا بالنَّار» ثم قال رسول الله صلى الله عليه وسلم حين أردنا الخروج: «إني كنت أَمَرْتُكُمْ أن تُحْرِقُوا فلانًا وفلانًا، وإن النَّار لا يُعَذِّبُ بها إلا الله، فإن وجَدْتُمُوهُما فاقْتُلُوهُما».
Daga Abu Hurairah - yardar Allah ta tabbata a gare shi - wanda ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya aiko mu a kan wani aiki, kuma ya ce: "Idan kun same mu haka kuma haka" na wasu mutane biyu daga Kuraishawa ya kira su "Don haka ya ƙone su da wuta." Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Fitowa: "Na umurce ku da ku ƙone haka-da-da, da kuma cewa Allah ne kawai ya ke shan azaba da wuta, in ka same su, ka kashe su. ”
Buhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Abu Hurairah, Allah ya kara yarda a gare shi, ya fada a cikin wannan hadisin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya aike su cikin rundunar yaki da abokan gaba, kuma ya umarce su idan suka ga wasu mutane biyu daga Kuraishawa da ya nada. su kona su da wuta, to, shi, tsira da aminci su tabbata a gare shi, ya ce da su lokacin da suka zo yi masa ban kwana kafin tafiyarsu: Na umarce ku da ku kona haka-da-haka, kuma cewa Allah ne kadai ke da azaba da wuta , kuma idan ka dauke su, kashe su.
Madogara
نزهة المتقين، تأليف: جمعٌ من المشايخ، الناشر: مؤسسة الرسالة، الطبعة الأولى: 1397 هـ الطبعة الرابعة عشر 1407 هـ.
كنوز رياض الصالحين، تأليف: حمد بن ناصر بن العمار ، الناشر: دار كنوز أشبيليا، الطبعة الأولى: 1430 هـ.
بهجة الناظرين، تأليف: سليم بن عيد الهلالي، الناشر: دار ابن الجوزي ، سنة النشر: 1418 هـ- 1997م.
رياض الصالحين، تأليف: محيي الدين يحيى بن شرف النووي ، تحقيق: د. ماهر بن ياسين الفحل ، الطبعة: الأولى، 1428 هـ.
صحيح البخاري، تأليف: محمد بن إسماعيل البخاري، تحقيق: محمد زهير الناصر، الناشر: دار طوق النجاة الطبعة: الأولى، 1422هـ.
دليل الفالحين، تأليف: محمد بن علان، الناشر: دار الكتاب العربي، نسخة الكترونية ، لا يوجد بها بيانات نشر.
شرح رياض الصالحين، تأليف: محمد بن صالح العثيمين، الناشر: دار الوطن للنشر، الطبعة: 1426 ه.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعنْ ابنِ مَسْعُودٍ رَضيَ اللهُ عنهُ قَالَ: كُنَّا مَعَ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فِي سَفَرٍ، فَانْطَلَقَ لِحَاجَتِهِ، فَرَأَيْنَا حُمَّرَةً مَعَهَا فَرْخَانِ، فَأَخَذْنَا فَرْخَيْهَا، فَجَاءَتِ الْحُمَرَةُ فَجَعَلَتْ تَفْرِشُ، فَجَاءَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَقَالَ: «مَنْ فَجَعَ هَذِهِ بِوَلَدِهَا؟ رُدُّوا وَلَدَهَا إِلَيْهَا»، وَرَأَى قَرْيَةَ نَمْلٍ قَدْ حَرَّقْنَاهَا، فَقَالَ: «مَنْ حَرَّقَ هَذِهِ؟» قُلْنَا: نَحْنُ. قَالَ: «إِنَّهُ لَا يَنْبَغِي أَنْ يُعَذِّبَ بِالنَّارِ إِلَّا رَبُّ النَّارِ».
Daga Ibu Mas’ud - Allah Ya yarda da shi- ya ce: Mun kasance tare da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a cikin tafiya, sai ya tafi wata buƙatarsa, sai muka ga wata tsuntsuwa tare da 'yayanta biyu, sai muka ɗauke su, sai tsuntsuwar ta zo tana fakan-fakan (tana nemansu), sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo, sai ya ce: «Waye ya raba wannan da ɗanta? ku maida mata da ɗanta», kuma sai ya ga wasu ramin tururuwa wanda muka ƙona shi, sai ya ce: «Waye ya ƙona wannan?» mukace: Mune. Ya ce: «Babu wanda yake yin azaba da wuta sai Ubangijin wuta».
Abu Dawud ne Ya Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Abdullahi Ibnu Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ambaci cewa su sun kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a wata tafiya, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tafi dan wata buƙatarsa, sai sahabbansa suka samu wata tsuntsuwa tare da 'ya'yanta biyu, sai suka ɗaukesu, sai tsuntsuwar ta fara fakan-fakan da fukafukanta tana buɗesu dan firgicin rasa 'ya'yanta, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kuma ya ce: Waye ya baƙanta mata rai ya tsoratar da ita ta hanyar ɗauke mata 'ya'yanta?! Sannan ya yi umarni a mayar mata da su. Sannan ya ga wani ramin tururuwar da aka ƙona shi da wuta, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Waye ya ƙona wannan? Wasu daga cikin sahabbansa suka ce: Mu ne. Sai ya ce da su: Lallai ba ya halatta ga wani ya azabtar da mai rai da wuta; sai Allah Mahaliccinta.
Fa’idoji
- Halaccin ɓoyuwa don biyan buƙata (kewayawa).
- Hani daga azabtar da dabbobi ta hanyar ɗaukar 'ya'yansu.
- Hani daga ƙona tururuwa da ƙwari da wuta.
- Kwaɗaitarwa akan rangwami da tausayawa dabbobi, kuma Musulunci ya rigaya da hakan.
- Jinƙansa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga dabbobi.
- Azabtarwa da wuta yana daga abinda Ubangiji - Mai girma da ɗaukaka - Ya keɓanta da shi.
Madogara
سنن أبي داود (4/ 309) (2675).
نزهة المتقين، لمجموعة من الباحثين (2/ 1105).
كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (19/ 150).
بهجة الناظرين، لسليم الهلالي (3/ 120).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (6/ 300).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comKowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com