Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai taɓa yaƙar wasu mutane ba har sai ya kirasu (zuwa ga Addini)

عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رَضِيَ اللهُ عَنْهُمَا قَالَ: مَا قَاتَلَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَوْمًا قَطُّ حَتَّى يَدْعُوَهُمْ.
Daga Abdullahi Ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai taɓa yaƙar wasu mutane ba har sai ya kirasu (zuwa ga Addini).
Ahmad da Baihaki suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - ya bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai taɓa farawa da yaƙar wasu mutane ba har sai ya kirasu zuwa ga Musulunci a farko, idan ba su amsa kiransa ba sai ya yaƙe su.

Fa’idoji
  1. An sharɗanta kira zuwa ga Musulunci kafin yaƙi idan Musuluncin bai isa zuwa garesu ba.
  2. Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana kiransu zuwa Musulunci, idan sun ƙi sai ya bijiro musu da bada da jizya, idan sun ƙi sai ya yaƙesu, kamar yadda ya zo a cikin wasu hadisan daban.
  3. Hikima a cikin yaƙi ita ce shigar mutane cikin Addinin Musulunci, ba wai kwaɗayi a kan bayinsu ko dukiyoyinsu da garuruwansu ba.
Madogara

مسند أحمد (4/ 16) (2105). السنن الكبرى للبيهقي (9/ 181) (18232). تحفة الأحوذي (5/ 130).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
HUKUNCE-HUKUNCE DA MAS'ALOLIN JIHADI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com