Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Duk wanda ya kashe wani (a wajen yaqi) yana da kayansa da abun da yake tare da shi na ganima

عن أبي قتادة الأنصاري رضي الله عنه قال: «خَرَجْنَا مَعَ رَسُول الله صلى الله عليه وسلم إلَى حُنَيْنٍ -وَذَكَرَ قِصَّةً- فَقَالَ رَسُولُ الله صلى الله عليه وسلم : مَنْ قَتَلَ قَتِيلاً لَهُ عَلَيْهِ بَيِّنَةٌ فَلَهُ سَلَبُهُ» قَالَهَا ثَلاثاً.
Daga Abu Qatada Al-ansari -Allah ya yarda da shi- ya ce: Mun fita tare da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - zuwa yakin Hunain- sai ya faxi Qissar sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Duk wanda ya kashe wani (a wajen yaqi) yana da kayansa da abun da yake tare da shi na ganima"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Cewa Annabi - SAW- ya ce a ranar Hunain: Duk wanda ya kashe wanda sukai futo na futo kuma yana da Shaida ko Dalili, yana da ganima, wato yana da tufafi da makaman wanda aka kashe, da sulkensa da ya yi yaƙi da shi, da kuma cewa Abu Qatada ya kashe wani mutum, sai ya ce wa waɗanda suke kewaye da shi: Na kashe wani mutum, don haka ya yi rantsuwa Wanda ya san wannan dole ne ya ba da shaida a gare ni, ya faɗi hakan sau uku.

Madogara

1- صحيح البخاري، محمد بن إسماعيل البخاري الجعفي، تحقيق: محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، الطبعة: الأولى 1422هـ. 2- صحيح مسلم، مسلم بن الحجاج القشيري النيسابوري، تحقيق محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، الطبعة: 1423هـ. 3- خلاصة الكلام شرح عمدة الأحكام، فيصل بن عبد العزيز المبارك، الطبعة: الثانية 1412هـ، 1992م. 4- الإفهام في شرح عمدة الأحكام لابن باز، تحقيق: سعيد القحطاني، مؤسسة عبد العزيز بن باز الخيرية، الرياض، الطبعة: الأولى 1435هـ. 5- الإلمام بشرح عمدة الأحكام، إسماعيل بن محمد الأنصاري، دار الفكر، دمشق، الطبعة: الأولى 1381هـ. 6- تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، عبد الله بن عبد الرحمن البسام، دار الميمان، الطبعة: الأولى 1426هـ، 2005م. 7- تأسيس الأحكام، أحمد بن يحيى النجمي، دار المنهاج، الطبعة: 1427هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
HUKUNCE-HUKUNCE DA MAS'ALOLIN JIHADI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com