Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Wanda ya kasance yana da abin yankan da zai yanks shi (na Layya) to idan jijirin watan Zul-Hijja ya kama, to kada ya cire wani abu daga gashinsa ko faratansa har sai ya yi layya

عَن أُمِّ سَلَمَةَ أُمِّ المُؤْمِنينَ زَوْجِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ رضي الله عنها قَالت: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَنْ كَانَ لَهُ ذِبْحٌ يَذْبَحُهُ فَإِذَا أُهِلَّ هِلَالُ ذِي الْحِجَّةِ، فَلَا يَأْخُذَنَّ مِنْ شَعْرِهِ، وَلَا مِنْ أَظْفَارِهِ شَيْئًا حَتَّى يُضَحِّيَ».
Daga Ummu Salama Uwar muminai matar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya kasance yana da abin yankan da zai yanks shi (na Layya) to idan jijirin watan Zul-Hijja ya kama, to kada ya cire wani abu daga gashinsa ko faratansa har sai ya yi layya".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annbi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarci wanda ya yi nufin ya yanka abin layyarsa cewa kada ya cire wani abu daga gashin kansa ko hammatarsa ko gashin bakinsa ko waninsu ko daga faratan hannunsa ko ƙafarsa idan jinjirin watan Zul-Hijja ya bayyana har sai ya yi layya.

Fa’idoji
  1. Wanda ya yi nufin yin layya bayan shigar goman (Zul Hijja) to sai ya fara kamewa da abinda aka ambata tun daga lokacin da ya yi niyya har sai ya yi layya.
  2. Idan ba zai yi layya ba a rana ta farko ba sai ya wanzu yana mai kamewa har sai ya yi layya a kowace rana daga ranakun Tshriƙ (ranakun layya 10, 11 da kuma 12 ga Zul Hajji).
Madogara

صحيح مسلم (3/ 1566) (1977). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (3/ 199). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (6/ 450). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (2/ 1165).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
LAYYA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com