عَنْ أَنَسٍ رَضيَ اللهُ عنهُ قَالَ: ضَحَّى النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ بِكَبْشَيْنِ أَمْلَحَيْنِ أَقْرَنَيْنِ، ذَبَحَهُمَا بِيَدِهِ، وَسَمَّى وَكَبَّرَ، وَوَضَعَ رِجْلَهُ عَلَى صِفَاحِهِمَا.
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi layya da raguna biyu masu farar fuska da baƙi-baƙi masu ƙaho, ya yanka su da hannunsa, kuma ya ambaci Allah ya yi kabbara, ya ɗora ƙafarsa akan fatun wuyayensu.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Anas - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yanka raguna biyu wato mazan tumakai, masu fararen ƙahunhuna waɗanda baƙi ya cakuɗa da su, kuma ya ce: Da sunan Allah, Allah ne Mafi girma, kuma ya ɗora ƙafarsa akan wuyansu.
Fa’idoji
- Halaccin layya, haƙiƙa musulmai sun haɗu akanta.
- Abin da ya fi layya ta zama daga wannan nau'in da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi layya da shi; dan kyan ganinsa da kuma kasancewar kitsensa da namansa yafi daɗi.
- AlNawawi ya ce: A cikinsa cewa an so mutum ya jiɓinci yanka layyarsa da kansa, kada ya wakilta a yankata sai da wani uzuri, a wannan lokacin an so ya halacci yankanta, idan ya wakilta wani musulmi ya halatta babu wani saɓani.
- Ibnu Hajar ya ce: A cikinsa akwai son kabbara tare da basmala a lokacin yanka da son ɗora ƙafar dama akan fatar wuyan abin layyar, kuma sun haɗu akan cewa kwantar da ita yana kasancewa ne a ɓangaren hagu sai ya ɗora ƙafaresa akan ɓangaren dama dan ya zama ya fi sauƙi ga mai yankan a wurin riƙe wuƙa da dama, da riƙe kanta da hannunsa na hagu.
- An so layya da mai ƙaho kuma yana halatta da waninsa.
Madogara
صحيح البخاري (7/ 102) (5565).
صحيح مسلم (3/ 1556) (1966).
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، لعبد الله البسام (ص724).
الإعلام بفوائد عمدة الأحكام، لابن الملقن (10/ 179).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن جُنْدُب بن عَبْدِ الله البجَليِّ رضي الله عنه قال: «صلى النبي صلى الله عليه وسلم يوم النَّحر، ثم خطب، ثم ذبح، وقال: من ذبح قبل أن يُصَلِّيَ فَلْيَذْبَحْ أُخرى مكانها، ومن لم يذبح فَلْيَذْبَحْ باسم الله».
Daga Jundub bin Abdullah Al-Bajali - Allah ya yarda da shi - ya ce: "Annabi - Salati da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi salla a ranar yanka, sa'annan ya yi huxuba, sa'annan aka yanka shi, sai ya ce: Duk wanda ya yanka kafin ya yi salla, to ya yanka wani a madadinsa, kuma wanda ba ya yanka to a yanka shi da sunan Allah".
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya fara ranar layya da addu'a, sannan ya nade huxuba, sa'annan ya yi sulusin sadakar, sai ya fita tare da hadayarsa zuwa zauren salla Nuna ayyukan ibada na Musulunci da gama-gari na fa'ida da ilimi ga al'umma, kuma ya fadi yana nuna musu hukunci kuma daya daga cikin sharuddan layya: Duk wanda ya yanka kafin ya yi sallar idi, hadayarsa ba ta isa ba, to ya yanka wani a madadinta, wanda kuwa bai yanka ba to a yanka shi da sunan Allah. Don yankan ya zama mai inganci, kuma hadayar ta zama ta halatta, wanda ke nuna halaccin wannan tsari wanda ba karbabbe bane. Wannan hadisin yana nuna farkon lokacin yankan ne tare da karewar sallar Idi, ba a lokacin sallah ba ko ta hanyar yanka liman, sai wadanda ba a bukatar sallar Idi a kansu, kamar yana tafiya.
Madogara
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، عبد الله بن عبد الرحمن البسام، تحقيق: محمد صبحي حلاق، مكتبة الصحابة، الأمارات، مكتبة التابعين، القاهرة، الطبعة: العاشرة 1426هـ.
تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، محمد بن صالح العثيمين، مكتبة الصحابة، الإمارات، الطبعة: الأولى 1426هـ، 2005م.
الإفهام في شرح عمدة الأحكام لابن باز، تحقيق: سعيد القحطاني، مؤسسة عبد العزيز بن باز الخيرية، الرياض، الطبعة: الأولى 1435هـ.
العمدة في الأحكام، عبد الغني بن عبد الواحد المقدسي الجماعيلي، تحقيق: سمير بن أمين الزهيري، الناشر: مكتبة المعارف للنشر والتوزيع، الرياض، المملكة العربية السعودية، الطبعة: الأولى 1419هـ، 1998م.
صحيح البخاري، محمد بن إسماعيل البخاري الجعفي، تحقيق: محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، الطبعة: الأولى 1422هـ.
صحيح مسلم، مسلم بن الحجاج القشيري النيسابوري، تحقيق محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، الطبعة: 1423هـ.
تأسيس الأحكام، أحمد بن يحيى النجمي، دار المنهاج، القاهرة، الطبعة: الأولى 1427هـ.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن البَرَاء بن عَازب رضي الله عنهما قال: «خطبنا النبي صلى الله عليه وسلم يوم الأضحى بعد الصلاة، فقال: من صلى صلاتنا وَنَسَكَ نُسُكَنَا فقد أصاب النُّسُكَ، ومن نسك قبل الصلاة فلا نُسُك له. فقال أبو بُرْدَةَ بن نِيَار -خال البَرَاء بن عَازبٍ-: يا رسول الله، إني نسكت شاتي قبل الصلاة، وعرفت أن اليوم يوم أكل وشرب، وأحببت أن تكون شاتي أول ما يذبح في بيتي، فذبحت شاتي، وتغديت قبل أن آتي الصلاة. فقال: شاتك شاة لحم. قال: يا رسول الله، فإن عندنا عَنَاقًا لنا هي أحب إلي من شاتين؛ أَفَتَجْزِي عني؟ قال: نعم، ولن تَجْزِيَ عن أحد بعدك».
A kan Al-Bara 'bin Azib - Allah ya yarda da shi - ya ce: "Annabi - Salatin Allah da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya yi magana da mu a ranar Idin layya bayan salla, sai ya ce: Duk wanda ya yi sallolinmu da ibadunmu ibadunmu, kuma duk wanda ya gabatar da ibada kafin salla, to bai kamata mu kiyaye ta ba. Abu Burda bin Nayyar - kawun mahaifin Al-Baraa bin Azeb - ya ce: Ya Manzon Allah, na yi shiru da hirata kafin na yi salla, kuma na san cewa yau rana ce ta ci da sha. Ya ce: Hirar ku ita ce ragon nama. Ya ce: Ya Manzon Allah, lalle ne mu, muna da runguma a kanmu, wadanda suka fi soyuwa a gare ni fiye da tumaki biyu. Za ku ba ni lada? Ya ce: Ee, kuma ba za a ba ka lada a bayanka ba.
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara
تيسير العلام للبسام الناشر: مكتبة الصحابة، الإمارات - مكتبة التابعين، القاهرة الطبعة: العاشرة، 1426 هـ - 2006 م.
تنبيه الأفهام للعثيمين -طبعة مكتبة الصحابة الإمارات - مكتبة التابعين، القاهرة الطبعة الأولى 1426.
الإفهام في شرح عمدة الأحكام –عبد العزيز بن باز-اعتناء سعيد بن علي بن وهف القحطاني - الرياض - الطبعة الأولى -1435.
خلاصة الكلام لفيصل المبارك الحريملي -الطبعة: الثانية، 1412 هـ - 1992 م.
الإلمام بشرح عمدة الأحكام لإسماعيل الأنصاري طبعة دار الفكر دمشق الأولى 1381.
تأسيس الأحكام لأحمد بن يحيى النجمي- دار المنهاج القاهرة مصر الطبعة الأولى.
صحيح البخاري لأبي عبد الله محمد بن إسماعيل الجعفي البخاري تحقيق محمد زهير بن ناصر الناصر -الناشر : دار طوق النجاة -الطبعة : الأولى 1422هـ.
صحيح مسلم المحقق: محمد فؤاد عبد الباقي - الناشر: دار إحياء التراث العربي - بيروت.
الموسوعة الفقهية الكويتية- وزارة الأوقاف والشئون الإسلامية – الكويت -الطبعة: (من 1404 - 1427 هـ) الأجزاء 1 - 23: الطبعة الثانية، دار السلاسل - الكويت، الأجزاء 24 - 38: الطبعة الأولى، مطابع دار الصفوة - مصر، الأجزاء 39 - 45: الطبعة الثانية، طبع الوزارة.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَن أُمِّ سَلَمَةَ أُمِّ المُؤْمِنينَ زَوْجِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ رضي الله عنها قَالت: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَنْ كَانَ لَهُ ذِبْحٌ يَذْبَحُهُ فَإِذَا أُهِلَّ هِلَالُ ذِي الْحِجَّةِ، فَلَا يَأْخُذَنَّ مِنْ شَعْرِهِ، وَلَا مِنْ أَظْفَارِهِ شَيْئًا حَتَّى يُضَحِّيَ».
Daga Ummu Salama Uwar muminai matar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya kasance yana da abin yankan da zai yanks shi (na Layya) to idan jijirin watan Zul-Hijja ya kama, to kada ya cire wani abu daga gashinsa ko faratansa har sai ya yi layya".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annbi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarci wanda ya yi nufin ya yanka abin layyarsa cewa kada ya cire wani abu daga gashin kansa ko hammatarsa ko gashin bakinsa ko waninsu ko daga faratan hannunsa ko ƙafarsa idan jinjirin watan Zul-Hijja ya bayyana har sai ya yi layya.
Fa’idoji
- Wanda ya yi nufin yin layya bayan shigar goman (Zul Hijja) to sai ya fara kamewa da abinda aka ambata tun daga lokacin da ya yi niyya har sai ya yi layya.
- Idan ba zai yi layya ba a rana ta farko ba sai ya wanzu yana mai kamewa har sai ya yi layya a kowace rana daga ranakun Tshriƙ (ranakun layya 10, 11 da kuma 12 ga Zul Hajji).
Madogara
صحيح مسلم (3/ 1566) (1977).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (3/ 199).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (6/ 450).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (2/ 1165).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comKowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com