Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Ku yi kirdadon daren Lailatul-ƙadri a cikin mara daga goman ƙarshe na Ramadan

عَنْ عَائِشَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهَا أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «تَحَرَّوْا لَيْلَةَ القَدْرِ فِي الوِتْرِ مِنَ العَشْرِ الأَوَاخِرِ مِنْ رَمَضَانَ».
Daga A'isha - Allah Ya yarda da ita - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ku yi kirdadon daren Lailatul-ƙadri a cikin mara daga goman ƙarshe na Ramadan".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kwaɗaitar akan yin ƙoƙari a nema da kirdadon daren lailatul-ƙadr da yawaita aiki na gari, shi ne mafi ƙauna ya kasance a darare na mara daga goman ƙarshe a Ramadan a kowace shekara, sune: Ashirin da ɗaya, da ashirin da uku, da ashirin da biyar, da ashirin da bakwai, da ashirin da tara.

Fa’idoji
  1. Falalar lailatul-ƙadr da kwaɗaitarwa akan kirdadonsa.
  2. Daga hikimar Allah da rahamarSa cewa Ya ɓoye wannan daren dan mutane su yi ƙoƙari a cikin ibada, dan neman sa, sai ladansu ya yi yawa.
  3. Daren Lailatul-ƙadr a goman ƙarshe na Ramadan (yake), kuma an fi ƙauna a mara daga gare shi .
  4. Daren Lailatul-ƙadr ɗaya ne daga dararen goman ƙarshe na Ramadan, shi ne daren da Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya saukar da Al-Kur'ani a cikinsa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, kuma Ya sanya wannan daren ya fi wata dubu a albarkarsu, da girman darajarsu, da tasirin aiki na gari a cikinsu.
  5. An ambaci (Lailatul-ƙadr) da yi wa (Dal ) ɗauri da hakan, kodai daga ɗaukaka ne, sai ace: Wane mai girman daraja ne, sai raɓawar daren ta zama daga babin raɓawar abu zuwa siffarsa, wato dare maɗaukaki, yana nufin cewa shi mai girman daraja ne da ɗaukaka da buwaya da matsayi zuwa ƙarshensa, (lallai Mu Mun saukar da shi a cikin wani dare Mai albarka). [al-Dukhan: 3], ko kuma daga ƙaddarawa ne: Sai raɓawar gare shi ta zama daga raɓawar Zarfi zuwa abinda yake tattaroshi, wato wannan daren wanda a cikinsa akwai ƙaddarawar abinda yake gudana a cikin shekara, (A cikinta ne ake rarraba kowane al'amarin da ake hukuntawa) [al-Dukhan: 4].
Madogara

صحيح البخاري (3/ 46) (2017). صحيح مسلم (2/ 828) (1169). تيسير العلام، لعبد الله البسام (ص347). تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، لابن عثيمين (3/ 470).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
GOMAN ƘARSHE TA RAMADAN

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com