Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

GOMAN ƘARSHE TA RAMADAN

Hadisai 6

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana ƙoƙari a cikin goman ƙarshe irin ƙoƙarin da ba ya yi a cikin waninsa

عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المؤْمِنينَ رَضِيَ اللهُ عَنْهَا: كَانَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَجْتَهِدُ فِي الْعَشْرِ الْأَوَاخِرِ مَا لَا يَجْتَهِدُ فِي غَيْرِهِ.
Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita -: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana ƙoƙari a cikin goman ƙarshe irin ƙoƙarin da ba ya yi a cikin waninsa.
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan goman ƙarshe ya zo na Ramadan yana ƙoƙari a cikinsu da yin ibada da ɗa'a, kuma yana kai matuƙa a cikin nau'ikan alherai da sinfofin ayyukan kirki da ibadu mafi yawa daga abinda yake ƙoƙari a cikin waninsa; hakan dan girma da falalar waɗancan dararen da kuma dan neman daren Lailatul Ƙadr.

Fa’idoji
  1. Kwaɗaitarwa akan yawaita alheri da fuskokin ayyukan ɗa'a a cikin watan Ramadan a hade da kuma goman ƙarshe daga gare shi a keɓance.
  2. Goman ƙarshe na Ramadan suna farawa ne daga daren ashirin da ɗaya har zuwa ƙarshen wata.
  3. An so ribatar lokuta mafifita da ayyukan ɗa'a.
Madogara

صحيح مسلم (2/ 832) (1175). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (14/ 463). نزهة المتقين، لمجموعة من الباحثين (2/ 848). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 339).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Wanda ya yi tsayuwar dare a daren Lailatul ƙadari yana mai imani da neman lada za'a gafarta masa abin da ya gabata daga zunubinsa

عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «مَنْ يَقُمْ لَيْلَةَ الْقَدْرِ إِيمَانًا وَاحْتِسَابًا غُفِرَ لَهُ مَا تَقَدَّمَ مِنْ ذَنْبِهِ»
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya yi tsayuwar dare a daren Lailatul ƙadari yana mai imani da neman lada za'a gafarta masa abin da ya gabata daga zunubinsa"
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana ba da labari game da falalar tsayuwar Lailatul kadari wacce take kasancewa a goman ƙarshe na Ramadan, cewa wanda ya yi ƙoƙarin yin sallah a cikinta da addu'a da karatun al-ƙur'ani da zikiri, yana mai imani da ita, da kuma abin da ya zo a falalarta, yana mai kwaɗayin sakamakon Allah - Maɗaukakin sarki - da aikinsa, ba don riya ko jiyarwa ba, to, za'a gafarta masa abin da ya gabata daga zunubansa.

Fa’idoji
  1. Falalar daren lailatul ƙadri da kwaɗaitarwa a kan tsayuwarsa.
  2. Ayyuka na gari ba'a karɓarsu sai tare da gaskiyar niyyoyi.
  3. Falalar Allah da rahamarsa, cewa wanda ya tsaya (da ibada) a daren Lailatul ƙadri yana mai imani da neman lada za'a gafarta masa abin da ya gabata daga zunubinsa.
Madogara

صحيح البخاري (1/ 16) (35). صحيح مسلم (1/ 523) (760). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (14/ 435). بهجة الناظرين، لسليم الهلالي (2/ 337). نزهة المتقين، (2/ 846). شرح النووي على مسلم (6/ 40). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (5/ 220). شرح صحيح البخاري، لابن بطال (4/ 21).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Duk wanda ya yi E'itikafi tare da ni to yayi a goman karshe domin nagani a wannan daren sannan kuma aka ikin ruwa da tabo tun daga , mantar dani, kuma hakika na ganni inayin Sujada a cikin tabo da ruwa safiyarta , to ku nemi riskarta a cikin goman karshe na watan.

عن أبي سعيد الخُدْري رضي الله عنه : «أن رسول الله صلى الله عليه وسلم كان يَعْتَكِفُ في العَشْرِ الأَوْسَطِ من رمضان. فاعتكف عامًا، حتى إذا كانت لَيْلَةَ إِحْدَى وَعِشْرِينَ -وهي اللَّيْلَةُ التي يخرج من صَبِيحَتِهَا من اعتكافه- قال: من اعتكف معي فَلْيَعْتَكِفِ العَشْرَ الأَوَاخِرَ فقد أُرِيتُ هَذِهِ اللَّيْلَةَ ثم أُنْسِيتُهَا، وقد رَأَيْتُنِي أَسْجُدُ فِي مَاءٍ وَطِينٍ من صَبِيحَتِهَا، فَالْتَمِسُوهَا فِي العَشْرِ الأَوَاخِرِ، والتمسوها في كل وِتْرٍ. فَمَطَرَتِ السَّمَاءُ تلك الليلة، وكان المسجد على عَرِيشٍ، فَوَكَفَ المسجد، فَأبْصَرَتْ عَيْنَايَ رسول الله صلى الله عليه وسلم وعلى جَبْهَتِهِ أَثَرُ المَاءِ وَالطِّين من صُبْحِ إحْدَى وَعشْرِيْنَ».
Daga Abu Sa'id -Allah ya yarda da shi- cewa Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi cewa ya kasance yanayin E'itikafi a goman tsakiya na Ramalana wata shekara sai yai E'itikafi har sai da ranar Ashirin da daya ta o wacce ita ce rananar da yake futowa a safiyarta daga E'itikafin sa ya ce: "Duk wanda ai yi E'itikafi tare da ni to yayi a goman karshe, to hakika an nunamun wannan daren sannan kuma aka manatar da ni ita, kuma na ganni ina Sujada a ikin Ruwa da tabo a Asubar ta, to ku neme ta a goman karshe kuma ku neme ta a Mara na kowawane dare kuma Masallacin ya kasance rufin arbar dabino ne , to sai Masallacin yayi ta zuba to naga -Manzon Allah- da idanuna goshinsa alamar ruwa da tabo a Asubar ranar Ashirin da daya.
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Abu Sa'id Al'khudri yana bada labari cewa Annabi ya kasance yana yin I'itikafin goman tsakiya na Azumi don neman daren lailatul kadari, sai wata shekara yayi -kamar yadda ya saba- har sai da adaren Ashirin da daya, ita ce ranar da yake futowa a safiyarta daga I'itikafinsa, sai ya san cewa lallai daren lailatul kadari tana goman karshe, sai yace da Sahabbansa: Duk wanda yayi I'itikafi tare da ni goman tsakiya, to ya zarce da I'itikafinsa, yayi a goman karshe, kuma ya bada labarin cewa Allah yanuna masa ita a Mafarkinsa sannan ya mantar da shi ita, sai dai ya ce kamar yagani a barcin wasu alamominta a cikin wannan shekarar su ne: Sujadarsa a cikin sallar Asuba akan tabo mai ruwa, to Allah ya gasgata Mafarkin Annabinsa, sai akayi ruwa a daren Ashirin da daya kuma ya kasance Masallacinsa an gina shi ne da yayin danga, kuma kututtudabino shi ne ginshikansa kuma rufinsa na ganyen Dabino ne, to sai Masallacin yayi ta zubar ruwa, sai Annabi yayi Sujada a safiyar Ashirin da daya, a cikin ruwa da tabo, Taisir Allam (349) Tanbih Al'afham (3/472) Ta'asis Al'ahkam 3/292

Madogara

عمدة الأحكام، تأليف: عبد الغني بن عبد الواحد المقدسي، تحقيق: محمود الأرناؤوط، دار الثقافة العربية ومؤسسة قرطبة، الطبعة الثانية، 1408هـ. تيسير العلام، تأليف: عبد الله بن عبد الرحمن البسام، تحقيق محمد صبحي بن حسن حلاق، مكتبة الصحابة ومكتبة التابعين، الطبعة العاشرة، 1426 هـ. تأسيس الأحكام شرح عمدة الأحكام، تأليف: أحمد بن يحي النجمي: نسخة إلكترونية لا يوجد بها بيانات نشر. تنبيه الأفهام شرح عمدة الإحكام، تأليف: محمد بن صالح العثيمين، مكتبة الصحابة ومكتبة التابعين، الطبعة الأولى: 1426هـ. الإفهام في شرح عمدة الأحكام، للشيخ عبد العزيز بن عبد الله بن باز، تحقيق: سعيد بن علي بن وهف القحطاني، الطبعة الأولى، 1435 هـ خلاصة الكلام على عمدة الأحكام، تأليف: فيصل بن عبد العزيز آل مبارك، الطبعة الثانية، 1412 هـ صحيح البخاري ، تأليف: محمد بن إسماعيل البخاري ، تحقيق: محمد زهير الناصر، الناشر: دار طوق النجاة الطبعة: الأولى، 1422هـ صحيح مسلم ، تأليف: مسلم بن الحجاج النيسابوري، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، الناشر: دار إحياء التراث العربي – بيروت.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Ku yi kirdadon daren Lailatul-ƙadri a cikin mara daga goman ƙarshe na Ramadan

عَنْ عَائِشَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهَا أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «تَحَرَّوْا لَيْلَةَ القَدْرِ فِي الوِتْرِ مِنَ العَشْرِ الأَوَاخِرِ مِنْ رَمَضَانَ».
Daga A'isha - Allah Ya yarda da ita - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ku yi kirdadon daren Lailatul-ƙadri a cikin mara daga goman ƙarshe na Ramadan".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kwaɗaitar akan yin ƙoƙari a nema da kirdadon daren lailatul-ƙadr da yawaita aiki na gari, shi ne mafi ƙauna ya kasance a darare na mara daga goman ƙarshe a Ramadan a kowace shekara, sune: Ashirin da ɗaya, da ashirin da uku, da ashirin da biyar, da ashirin da bakwai, da ashirin da tara.

Fa’idoji
  1. Falalar lailatul-ƙadr da kwaɗaitarwa akan kirdadonsa.
  2. Daga hikimar Allah da rahamarSa cewa Ya ɓoye wannan daren dan mutane su yi ƙoƙari a cikin ibada, dan neman sa, sai ladansu ya yi yawa.
  3. Daren Lailatul-ƙadr a goman ƙarshe na Ramadan (yake), kuma an fi ƙauna a mara daga gare shi .
  4. Daren Lailatul-ƙadr ɗaya ne daga dararen goman ƙarshe na Ramadan, shi ne daren da Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya saukar da Al-Kur'ani a cikinsa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, kuma Ya sanya wannan daren ya fi wata dubu a albarkarsu, da girman darajarsu, da tasirin aiki na gari a cikinsu.
  5. An ambaci (Lailatul-ƙadr) da yi wa (Dal ) ɗauri da hakan, kodai daga ɗaukaka ne, sai ace: Wane mai girman daraja ne, sai raɓawar daren ta zama daga babin raɓawar abu zuwa siffarsa, wato dare maɗaukaki, yana nufin cewa shi mai girman daraja ne da ɗaukaka da buwaya da matsayi zuwa ƙarshensa, (lallai Mu Mun saukar da shi a cikin wani dare Mai albarka). [al-Dukhan: 3], ko kuma daga ƙaddarawa ne: Sai raɓawar gare shi ta zama daga raɓawar Zarfi zuwa abinda yake tattaroshi, wato wannan daren wanda a cikinsa akwai ƙaddarawar abinda yake gudana a cikin shekara, (A cikinta ne ake rarraba kowane al'amarin da ake hukuntawa) [al-Dukhan: 4].
Madogara

صحيح البخاري (3/ 46) (2017). صحيح مسلم (2/ 828) (1169). تيسير العلام، لعبد الله البسام (ص347). تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، لابن عثيمين (3/ 470).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Ina ganin mafarkenku haƙiƙa sun haɗu a bakwan ƙarshe, duk wanda ya kasance zai yi kardadonsa to ya yi kardadonsa a bakwan ƙarshe

عَنِ ابْنِ عُمَرَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا: أَنَّ رِجَالًا مِنْ أَصْحَابِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أُرُوا لَيْلَةَ القَدْرِ فِي المَنَامِ فِي السَّبْعِ الأَوَاخِرِ، فَقَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «أَرَى رُؤْيَاكُمْ قَدْ تَوَاطَأَتْ فِي السَّبْعِ الأَوَاخِرِ، فَمَنْ كَانَ مُتَحَرِّيهَا فَلْيَتَحَرَّهَا فِي السَّبْعِ الأَوَاخِرِ».
Daga Ɗan Umar Allah Ya yarda da su: Cewa wasu mazaje daga sahabban Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - an nuna musu daren Lailatul-ƙadr a cikin mafarki a bakwan ƙarshe, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ina ganin mafarkenku haƙiƙa sun haɗu a bakwan ƙarshe, duk wanda ya kasance zai yi kardadonsa to ya yi kardadonsa a bakwan ƙarshe".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Wasu mazaje daga sahabban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sun gani a cikin mafarki cewa daren Lailatul-ƙadr yana kasancewa ne a ƙarshen daren bakwai na Ramadan. Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Ina ganin mafarke-mafarkenku haƙiƙa sun dace a bakwan ƙarshe na Ramadan, wanda ya kasance yana nufinsa, yana mai kwaɗayi akan nemansa, to sai ya yi ƙoƙari a kardadonsa da nemansa da yawaitawa daga aiki na gari shi ya fi ƙaunar ya zama a bakwan ƙarshe, shi yana farawa ne daga daren ashirin da huɗu idan watan Ramadan ya zama kwana talatin ne, kuma daren ashirin da uku yana farawa ne idan watan ya zama mai kwana ashirin da tara ne.

Fa’idoji
  1. Falalar daren Lailatul-ƙadr da kwaɗaitarwa akan kardadonsa.
  2. Daga hikimar Allah da rahamarSa cewa Ya ɓoye wannan daren dan mutane su yi ƙoƙari a cikin ibada, dan nemansa, sai ladansu ya yi yawa.
  3. Lailatul-ƙadr a cikin goman ƙarshe na Ramadan, kuma ya fi (samun) ƙauna a bakwan ƙarshe daga gare shi.
  4. Daren Lailatul-ƙadr ɗaya ne daga dararen goman ƙarshe na Ramadan, shi ne daren da Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya saukar da AlKur'ani a cikinsa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, kuma Ya sanya wannan daren ya fi wata dubu a albarkarsu, da girman darajarsu, da tasirin aiki na gari cikinsu.
  5. An anbace shi (Lailatul-ƙadr) da w (Dal) ɗauri da hakan, kodai daga ɗaukaka ne sai a ce: Wane mai girman daraja ne, sai raɓa daren ya zama daga raɓawar abu ne zuwa siffarsa, wato dare maɗaukaki, yana nufin cewa shi mai girman daraja ne a ɗaukaka da bunƙasa da matsayi har zuwa ƙarshensa, (Lallai ne mu Mun saukar da shi a cikin wani dare mai albarka) [al-Dukhan: 3], ko kuma daga ƙaddarawa ne; Sai raɓawarsa zuwa gareshi ta zama daga raɓawar Zarfi ne zuwa abinda ya tattaroshi, wato wannan daren wanda ƙaddara abinda yake gudana cikin shekara yake kasancewa a cikinsa, (A cikinsa ne ake rarrabe kowane al'amari abin hukuntawa)) [al-Dukhan: 4].
Madogara

صحيح البخاري (3/ 46) (2015). صحيح مسلم (2/ 822) (1165). تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، لابن عثيمين (3/ 467). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، لعبد الله البسام (ص347).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan goman ƙarshe ta shiga zai raya dare, zai farkar da iyalansa, zai yi ƙoƙari zai ɗaure gwabso

عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المُؤْمِنينَ رَضِيَ اللهُ عَنْهَا قَالَتْ: كَانَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ إِذَا دَخَلَ الْعَشْرُ أَحْيَا اللَّيْلَ، وَأَيْقَظَ أَهْلَهُ، وَجَدَّ وَشَدَّ الْمِئْزَرَ.
Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan goman ƙarshe ta shiga zai raya dare, zai farkar da iyalansa, zai yi ƙoƙari zai ɗaure gwabso.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan goman ƙarshe na Ramadan ya shiga zai rayar da dukkan dare da nau'ikan ayyukan ɗa'a, kuma ya farkar da iyalansa dan yin sallah, ya yi ƙoƙari a cikin ibada ƙari akan al'adarsa, ya duƙufa gareta, kuma ya nisanci matansa.

Fa’idoji
  1. Kwaɗaitarwa da ribatar mafifitan lokuta da ayyuka na gari.
  2. AlNawawi ya ce: A cikin wannan hadisin: Cewa an so a yi ƙari daga ibadu a cikin goman ƙarshe na Ramadan, kuma an so raya dararensa da ibadu.
  3. Yana kamata ga bawa ya zama mai kwaɗayi akan iyalansa da umartarsu da yin ibada, kuma ya yi haƙuri akansu.
  4. Aikata alherai yana buƙatuwa zuwa ƙudirin niyya da haƙuri da dagewa.
  5. AnNawawi ya ce: Malamai sun yi saɓani a ma'anar (ya ɗaure gwabso) an ce: Shi ne ƙoƙari a cikin ibadu ƙari akan al'adarsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a waninsa, kuma ma'anarsa: Zage damtse a cikin ibadu, ana cewa; Na ɗaure gwabso na dan wannan al'amarin, wato: Na zage damtse gare shi na yi ƙoƙari, an ce: Shi kinaya ne game da nisantar iyali dan shagaltuwa da ibadu.
Madogara

صحيح البخاري (3/ 47) (2024). صحيح مسلم (2/ 832) (1174). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 132). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 181).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com