(Labari) ya kai ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa Abdullahi ɗan Amr - Allah Ya yarda da shi - ya kasance yana jeranta azimi ba ya ajiyewa tsawon shekara, kuma yana sallar dare gaba ɗayansa ba ya bacci, sai ya hana shi daga hakan, kuma ya ce masa: Ka yi azimi kuma ka huta, ka yi sallar dare kuma ka yi bacci. Kuma ya hane shi daga jeranta azimi da tsayuwar dare gaba ɗayansa, kuma ya ce masa: Lallai cewa kai idan ka aikata hakan idanka zai yi rauni saboda shi zai yi kogo zai shige, kuma zuciyarka zata gaji ta ƙosa saboda haka; babu azimi (ga) wanda ya azimci shekara; inda cewa shi bai samu ladan azimin ba dan saɓawa hani, kuma bai buɗe baki ba domin cewa shi ya kame. Sannan ya shiryar da shi zuwa azimin kwana uku a kowane wata shi ne azimin shekara; domin kowace rana (kwatankwacin ladan) kwanaki goma ne, kuma hakan shi ne mafi ƙarancin riɓanyawa ga kyakkyawa. Sai Abdullahi ya ce: Lallai ni zan iya sama da hakan. Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: To sai ka yi azimin (Annabi) Dawud - aminci ya tabbata agare shi - shi ne mafificin azimi, ya kasance yana azimin yini kuma yana hutawa yini, kuma ya kasance ba ya gudu idan ya gamu da maƙiya; domin tsarin aziminsa ba ya raunana jikinsa ba.
- Azimin kwana uku a kowane wata kamar azimin shekara ne gabaɗayanta, hakan domin kyakkywa ɗaya da kwatankwacin sa goma ne, sai ta zama kwana talatin, idan ya yi azimin kwana uku a kowane wata kamar shi ya azmici shekara ce gaba ɗayanta.
- Daga usuluban kira zuwa ga Allah (akwai) kwaɗaitarwa a cikin aiki da ambatan ladansa da ladan dawwama a kansa.
- AlKhaɗɗabi ya ce: A taƙaice ƙissar Abdullahi ɗan Amr cewa Allah - Maɗaukakin sarki - bai ɗorawa bawanSa ibadar azimi a keɓance ba, kai Ya bautar da shi da nau'ikan ibadu, da zai ƙarar da ƙoƙarinsa da ya taƙaita a waninsa, to abinda ya fi shi ne tattali a cikinsa dan sashin ƙarfinsa ya ragu ga waninsa, haƙiƙa an yi nuni zuwa ga hakan da faɗinsa - aminci ya tabbata agare shi - a (Annabi) Dawud - aminci ya tabbata agare shi -: "Ya kasance ba ya gudu idan ya gamu da maƙiyi"; domin cewa shi ya kasance yana ƙarfafuwa da buɗa baki saboda yaƙi.
- Hani daga zirfafawa da ɗorawa kai nauyi a cikin ibada, alheri shi ne lazimtar sunna.
- Mazahabar Jumhur ɗin ma'abota ilimi ita ce karhancin azimin zamani (shekara a jere), kuma yana zama haram idan ya tsanantawa kansa kuma ya cutar da ita ya ɗora mata, ya kauce daga sunnar Annabinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ya kuma ƙudirce cewa canja sunnarsa ya fi daga gareta.
صحيح البخاري (3/ 40) (1979). صحيح مسلم (2/ 812) (1159). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (2/ 214). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (3/ 297).