Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Wanda ya yi azumin wani yini a tafarkin Allah, Allah Zai nisantar da fuskarsa daga wuta (tsawon) shekara saba'in

عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الْخُدْرِيِّ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ قَالَ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «مَنْ صَامَ يَوْمًا فِي سَبِيلِ اللهِ بَاعَدَ اللهُ وَجْهَهُ عَنِ النَّارِ سَبْعِينَ خَرِيفًا».
Daga Abu Sa'id Alkhudr - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- yana cewa: "Wanda ya yi azumin wani yini a tafarkin Allah, Allah Zai nisantar da fuskarsa daga wuta (tsawon) shekara saba'in".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa wanda ya azumci wani yini a yaƙi, an ce a yaƙi da waninsa yana mai ikhlasi ga Allah dan neman sakamako da lada daga Allah; to lallai Allah da falalarsa Zai nisantar da tsakaninsa da tsakanin wuta (tsawon) shekara saba'in.

Fa’idoji
  1. AlNawawi ya ce: Falalar azimi a tafarkin Allah, shi abin ɗauka ne akan wanda ba ya cutuwa da yin azumin, kuma ba zai salwantar da wani haƙƙi idan ya yi azumin, kuma yaƙinsa ko waninsa ba zai bata muhimman yaƙi da shi ba.
  2. Zaburarwa da kwaɗaitarwa akan azimin nafila.
  3. Wajabcin ikhlasi da neman yardar Allah, kuma kada ya yi azimi dan riya ko jiyarwa ko dan wasu manufofin daban.
  4. Sindi ya ce: Faɗinsa (A tafarkin Allah), za'a iya ɗaukar cewa abin nufi mujarradin gyara niyya, kuma za'a iya ɗaukar cewa abin nufi da shi cewa shi ya yi azimi a halin kasancewarsa mai yaƙi, na biyun shi ne abin gaggawar (manufa).
  5. Ibnu Hajar ya ce: Faɗinsa: (Kharif saba'in) Kharif wani lokaci ne sananne a shekara, abin nufi da shi a nan shekarar (gaba ɗayanta), kuma keɓance Kharif (Kaka) da ambato banda ragowar lokutan - zafi da sanyi da damina -; domin cewa Kharif (Kaka) ya fi ragowar lokutan kyau domin kasancewarsa ana tsinkar 'ya'yan itatuwa a cikinsa.
Madogara

صحيح البخاري (4/ 26) (2840). صحيح مسلم (2/ 808) (1153). تيسير العلام، لعبد الله البسام (ص346). تنبيه الأفهام شرح عمدة الإحكام، لابن عثيمين (3/ 465). الإفهام في شرح عمدة الأحكام، لابن باز (ص426). خلاصة الكلام على عمدة الأحكام، لفيصل آل مبارك (ص162).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
AZUMIN NAFILA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com