عَنْ مُعَاذَةَ قَالَتْ: سَأَلْتُ عَائِشَةَ، فَقُلْتُ: مَا بَالُ الْحَائِضِ تَقْضِي الصَّوْمَ، وَلَا تَقْضِي الصَّلَاةَ؟ فَقَالَتْ: أَحَرُورِيَّةٌ أَنْتِ؟ قُلْتُ: لَسْتُ بِحَرُورِيَّةٍ، وَلَكِنِّي أَسْأَلُ. قَالَتْ: كَانَ يُصِيبُنَا ذَلِكَ، فَنُؤْمَرُ بِقَضَاءِ الصَّوْمِ، وَلَا نُؤْمَرُ بِقَضَاءِ الصَّلَاةِ.
Daga Mu'azah ta ce : Na tambayi Nana A'isha, sai na ce: Me yasa mai al’ada take rama azimi, bata rama sallah? Sai ta ce: Shin ke baharuriyyace? na ce: Ni ba baharuriyya ba ce, sai dai tambaya nake. Ta ce: Hakan yana samunmu, sai a umarcemu da rama azimi, ba'a umartarmu da rama sallah.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Mu'azah al'adawiyya - ta tambayi uwar muminai Nana A'isha - Allah Yarda da ita -, sai ta ce: Me yasa mai al’ada take rama azimi, bata rama sallah? Sai ta ce mata: Shin ke daga Khawarijawa Hirarura’a kike ne ? waɗanda suke yawaita tambaya dan ta'annuti da kuma tsanantawa? Na ce: Ni ba baharuriyyababa ce, sai dai tambaya nake yi, ta ce: al’ada tana samunmu tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai a umarcemu da rama azimi, ba'a umartarmu da rama sallah.
Fa’idoji
- Yin inkari akan dukkan wanda ya yi tambaya irin ta ta'annitanci da kuma jayayya.
- Haruriyya an dangantasu ga wani gari kusa da Kufa, sunansa "Hiraura’a'; wasu jama'a ne daga Khwarijawa, ta kamantata da su ne saboda tsanantawarsu a cikin al'amarinsu da kuma yawan tayambayarsu da ta'annitancinsu da ita.
- Malami ya bayyanawa wanda ya neme shi dan neman sani da kuma neman shiriya.
- Bada amsa da nassi ya fi; domin cewa Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - bata bijiro da ma'anar da mai tambayar ta tambayeta ba; hakan domin cewa amsa da nassi ya fi yanke musu.
- Sallamawa hukuncin Allah da ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - koda bawa bai san hikimar ba.
- Nawawi ya ce: Ma'anar faɗin Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - cewa wasu jama'a daga Khwarij suna wajabtawa mai al’ada rama sallar da ta wuce a lokacin al’ada, wannan kuwa saɓanin Ijma'in musulmai ne, wannan tambayar da Nana A'isha ta tambayeta tambaya ce ta inkari wato: Wannan hanyar Haruriyya ce tir da wannan hanyar.
Madogara
صحيح البخاري (1/ 71) (321).
صحيح مسلم (1/ 265) (335).
الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (1/ 68).
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، لعبد الله البسام (ص81).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن عائشة رضي الله عنها أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «من مات وعليه صِيَامٌ صَامَ عنه وَلِيُّهُ».
Daga Abu Buraida Allah ya yarda dashi daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
A’isha, Allah Ya yarda da ita, ta sanar da cewa Annabi –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya umarci waliyyin wanda ya mutu, kuma shi ke da alhakin azumin da ake nema na alwashi, ko kaffara, ko ramuwar Ramadhan, don yin azumi a madadinsa. Domin bashi ne yake binsa, danginsa ma sun fi shi iya biyansa Saboda alheri ne a gare shi, alheri da haɗi, kuma wannan abin kyawawa ne, ba tabbatacce ba.
Madogara
عمدة الأحكام، تأليف: عبد الغني بن عبد الواحد المقدسي، تحقيق: محمود الأرناؤوط، دار الثقافة العربية ومؤسسة قرطبة، الطبعة الثانية، 1408هـ.
تيسير العلام، تأليف: عبد الله بن عبد الرحمن البسام، تحقيق محمد صبحي بن حسن حلاق، مكتبة الصحابة ومكتبة التابعين، الطبعة العاشرة، 1426 هـ.
تأسيس الأحكام شرح عمدة الأحكام، تأليف: أحمد بن يحي النجمي: نسخة إلكترونية لا يوجد بها بيانات نشر.
تنبيه الأفهام شرح عمدة الإحكام، تأليف: محمد بن صالح العثيمين، مكتبة الصحابة ومكتبة التابعين، الطبعة الأولى: 1426هـ.
صحيح البخاري، تأليف: محمد بن إسماعيل البخاري، تحقيق: محمد زهير الناصر، الناشر: دار طوق النجاة الطبعة: الأولى 1422هـ.
صحيح مسلم، تأليف: مسلم بن الحجاج النيسابوري، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، الناشر: دار إحياء التراث العربي - بيروت.
الموسوعة الفقهية الكويتية، صادر عن: وزارة الأوقاف والشئون الإسلامية - الكويت، الطبعة: (من 1404 - 1427هـ).
إحكام الإحكام شرح عمدة الأحكام، تأليف: ابن دقيق العيد -مطبعة السنة المحمدية- بدون طبعة وبدون تاريخ.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن عبد الله بن عباس رضي الله عنهما قال: «جاء رجل إلى النبي صلى الله عليه وسلم فقال: يا رسول الله، إن أمي ماتت وعليها صوم شهر. أَفَأَقْضِيهِ عنها؟ فقال: لو كان على أمك دَيْنٌ أَكُنْتَ قَاضِيَهُ عنها؟ قال: نعم. قال: فَدَيْنُ اللهِ أَحَقُّ أن يُقْضَى ».
وفي رواية: «جاءت امرأة إلى رسول الله صلى الله عليه وسلم فقالت: يا رسول الله، إن أمي ماتت وعليها صوم نذر. أفأصوم عنها؟ فقال: أرأيت لو كان على أمك دَيْنٌ فَقَضَيْتِيهِ ، أكان ذلك يُؤَدِّي عنها؟ فقالت: نعم. قال: فَصُومِي عن أمك».
Daga Abudullahi Dan Abbas -Allah ya yarda da shi- "Lallai ce wa Mahaifiyata ta Mutu kuma akanta akwai bashin Azumi ko na iya rama mata? sai ya ce: da ace a kanta akwai bashin kudi zaka biya mata? ya ce: Ey sai ya ce: to Bashin Allah shi yafi cancanta a biya" a cikin wata riwayar kuma: "wata Mata tazo wajen Mazon Allah "Lallai ce wa Mahaifiyata ta Mutu kuma akanta akwai bashin Azumi ko na iya rama mata? sai ya ce: da ace a kanta akwai bashin kudi zaki biya mata?tiyarki Bashin ya ce: Ey sai ya ce:to biyawa mahaifiyarki bashin Azumin ta.
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Kuma wannan Hadisin riwaya biyu aka samu, Kuma abunda ya ke a fili na siyakin, cewa abubuwa biyu ne suka faru ba abu daya ba, Na farko: ceawa wani Mutum yazo wajen Annabi Tsira da Amincin Allah Su tabbata a gare shi to sai ya bada labarin cewa Mahaifiyarsa ta Mutu kuma ana binta bashin Azumin ta yi Bakancensa shin zai iya rama mata? Riwaya ta biyu: Cewa wata Mata ta zo wajen Mazon Allah -Tsira da Aminc in Allah Su tabbata a gare shi -ceawa wata Mata ta zo wajen Annabi -Tsira da Amincin Allah Su tabbata a gare shi- to sai ya bada labarin cewa Mahaifiyarta ta Mutu kuma ana binta bashin Azumin ta yi Bakancensa shin zai iya rama mata? to duka kuma ya basu fatawa da raa Azumin, sannan ya buga musu Misali da abun da zai kusanta musu da fahimtar abunda yake muwa ga Iyayensu nufi kuma ya kara musu bayani Kuma: shi ne cewwa lallai wannan Azumin Bashi ne na Allah akan Iyayen su, to idan bashin Mutum za'a biya to bashin Allah shi ne mafi cancanta da a biya.
Madogara
عمدة الأحكام، تأليف: عبد الغني بن عبد الواحد المقدسي، تحقيق: محمود الأرناؤوط، دار الثقافة العربية ومؤسسة قرطبة، الطبعة الثانية، 1408هـ.
تيسير العلام، تأليف: عبد الله بن عبد الرحمن البسام، تحقيق محمد صبحي بن حسن حلاق، مكتبة الصحابة ومكتبة التابعين، الطبعة العاشرة، 1426 هـ.
تنبيه الأفهام شرح عمدة الإحكام، تأليف: محمد بن صالح العثيمين، مكتبة الصحابة ومكتبة التابعين، الطبعة الأولى: 1426هـ.
صحيح البخاري ، تأليف: محمد بن إسماعيل البخاري ، تحقيق: محمد زهير الناصر، الناشر: دار طوق النجاة الطبعة: الأولى، 1422هـ
صحيح مسلم ، تأليف: مسلم بن الحجاج النيسابوري، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي - الناشر: دار إحياء التراث العربي – بيروت.
Wannan hadisi a HadeethEnc.com