Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kwaɗaitar akan sahur shi ne cin (abin ci) a ƙarshen dare dan yin tanadi ga azimi; domin cewa a cikinsa akwai (albarka) alheri mai yawa na lada da sakamako, da tashi a ƙarshen dare dan addu'a, da ƙarfafuwa akan azimi, da nishaɗuwa gare shi, da kuma sauƙaƙa wahalarsa.
- An so sahur da riko umarnin shari'a da aikata shi.
- Ibnu Hajar ya ce a cikn Fathul Bari: Albarka a cikin sahur tana samuwa ne ta ɓangarori masu yawa, su ne bin sunna, da saɓawa Ahlul kitabi, da ƙarfafuwa da shi akan ibada, da ƙari a cikin nishaɗi, da tunkuɗe munanan ɗabi'u wanda yunwa take taso shi, da kawo sababin sadaka ga wanda yake roƙo a wannan lokacin ko yake haɗuwa da shi akan cin abin ci, da sabbaba zikiri da addu'a a lokacin ana fatan amsawa, da riskar niyyar azimi ga wanda ya rafkana daga gareta kafin ya yi bacci.
- Kyakkyawar koyarwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - inda yake haɗa hukunci da hikima; dan ƙirji ya buɗe da shi, kuma a san matsayin shari'a da shi.
- Ibnu Hajar ya ce: Sahur yana samuwa ne da mafi ƙarancin abinda mutum yake samunsa na abin ci da abin sha.
صحيح البخاري (3/ 29) (1923). صحيح مسلم (2/ 770) (1095). تيسير العلام، لعبد الله البسام (ص317). تنبيه الأفهام شرح عمدة الإحكام، لابن عثيمين (3/ 416).