عَنْ سَهْلِ بْنِ سَعْدٍ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «لَا يَزَالُ النَّاسُ بِخَيْرٍ مَا عَجَّلُوا الْفِطْرَ».
Daga Sahl ɗan Sa'ad - Allah Ya yarda da shi - lallai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Mutane ba zasu gushe ba cikin alheri matuƙar sun gaggauta buɗa baki".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa mutane ba za su gushe ba a cikin alheri muddin dai sun gaggauta buɗa baki a azimi, bayan tabbatar da faɗuwar rana; hakan dan ruko da sunna, da tsayuwa a iyakarta.
Fa’idoji
- AlNawawi ya ce: A cikinsa akwai kwaɗaitarwa akan gaggauta shi bayan tabbatar da faɗuwar rana, ma'anarsa al'amarin al'ummata ba zai gushe ba a tsare alhali su suna cikin alheri muddin dai sun kiyaye wannan sunnar, idan sun jinkirta shi to hakan ya zama alama akan ɓarnar da zasu faɗa a cikinta.
- Wanzuwar alheri a cikin mutane saboda biyayyarsu ne ga Sunnah, kuma ɓacin al'amura yana ratayane da canja sunna.
- Saɓawa mazawa littafi (Yahudawa da Nasara) da 'yan bidi'a, domin cewa su suna jinkirta buɗa baki.
- Ibnu Hajar ya ce: A cikinsa akwai bayanin sababin hakan, Muhallab ya ce: Hikima a cikin hakan kada a yi ƙari a yini a dare, kuma ya fi tausayi ga mai azimi kuma ya fi ƙarfafa gare shi akan ibada, malamai sun haɗu akan cewa mahallin hakan idan faɗuwar rana ta tabbata da gani (faɗuwar rana) ko da labartawar adalai biyu, haka adali ɗaya a zance mafi rinjaye.
- Ibnu Hajar ya ce: Faɗakarwa: Daga bidi'o'i ababen ƙi abinda aka farar a wannan zamanin na yin kiran sallah na biyu kafin Asuba da kwatankwacin ɗaya bisa uku na awa a cikin (watan ) Ramadan, da kashe fitilun da aka sanya su alama dan haramta ci da sha ga wanda yake nufin yin azimi dan riyawa daga wanda ya farar da shi cewa shi dan tsare ibada, kuma babu wanda ya san hakan sai ɗaiɗaikun mutane, haƙiƙa hakan ya jasu zuwa sun kasance ba sa kiran sallah sai bayan faɗuwar rana da daraja dan tabbatar da lokaci a yadda suka riya, sai suka jinkirta buɗa baki, kuma suka gaggauta sahur, suka saɓawa Sunnah, saboda haka alheri ya karanta a garesu kuma sharri ya yawaita a cikinsu, Allah ne abin neman taimako.
Madogara
صحيح البخاري (3/ 36) (1957).
صحيح مسلم (2/ 771) (1098).
تيسير العلام، لعبد الله البسام (ص335).
تنبيه الأفهام شرح عمدة الإحكام، لابن عثيمين (3/ 442).
خلاصة الكلام على عمدة الأحكام، لفيصل آل مبارك (ص155).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ زَيْدِ بْنِ ثَابِتٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: تَسَحَّرْنَا مَعَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، ثُمَّ قَامَ إِلَى الصَّلاةِ، قُلْتُ: كَمْ كَانَ بَيْنَ الأَذَانِ وَالسَّحُورِ؟ قَالَ: قَدْرُ خَمْسِينَ آيَةً.
Daga Zaidu ɗan Sabit - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Mun yi sahur tare da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sannan ya tashi zuwa sallah, na ce: Nawa ne tsakanin kiran sallah da sahur? ya ce: Gwargwadan ayoyi hamsin.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Wasu daga sahabbai - Allah Ya yarda da su - sun yi sahur tare da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tashi zuwa sallar Asuba. Sai Anas ya cewa Zaid ɗan Sabit - Allah Ya yarda da shi -: Nawane gwargwadan lokaci sahur tsakanin kiran sallah da iƙama? Sai Zaid ɗan Sabit - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Gwargwadan karanta ayoyi hamsin ne matsakaita, ba dogwaye ba ba kuma gajeru ba, ba karatu da gaggawa ba ba kuma a hankali ba.
Fa’idoji
- Falalar jinkirta sahur har zuwa gab da Asuba; domin idan ya jinkirta to anfanin jikin daga gare shi ya fi girma kuma anfaninsa a yinin ya fi yawa.
- Kwaɗayin sahabbai da haɗuwa da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - dan su yi koyi da shi.
- Kyakkyawar mu'amalar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga sahabbansa, inda ya kasance yana cin (abin ci) tare da su.
- Lokacin kamewa shi ne ɓullowar alfijir.
- Faɗinsa: "Nawa ne tsakanin kiran sallah da sahur", abin nufi tsakanin sahur da iƙama; saboda faɗinsa a wani hadisn: "Nawa ne tsakanin gamawarsu daga sahur ɗinsu da kuma shigarsu sallah", hadisai sashinsu suna fassara sashi.
- AlMuhallab ya ce: A cikinsa akwai ƙaddara lokuta da ayyukan jiki, larabawa sun kasance suna ƙaddara lokuta da ayyuka kamar faɗinsu: Gwargwadan tatsar nonon akuya, da gwargwadan soke raƙumi, sai Zaid ɗan Sabit - Allah Ya yarda da shi - ya kauce daga hakan zuwa ƙaddarawa da karatu; dan nuni zuwa cewa wancan lokacin ya kasance lokacin ibada ne da karatu, da sun kasance suna ƙaddarawa da wanin aiki da ya ce misali: Gwargwadan daraja, ko ɗaya bisa uku ɗaya bisa biyar na awa.
- Ibnu Abi Jamrah ya ce: Tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya kasance yana duba abinda shi ne mafi sauƙi ga al'ummarsa sai ya aikata shi; domin cewa shi da bai yi sahur ba da sun bi shi sai ya yi wa wasunsu wahala, da kuma ya yi sahur a tsakiyar dare da ya yi wa wanda bacci yake rinjayarsa wahala zai iya kai shi zuwa barin sallar Asuba ko ya buƙatu zuwa ƙoƙarin rashin bacci.
Madogara
صحيح البخاري (3/ 29) (1921).
صحيح مسلم (2/ 771) (1097).
تيسير العلام، لعبد الله البسام (ص318).
تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، لابن عثيمين (3/ 418).
خلاصة الكلام على عمدة الأحكام، لفيصل آل مبارك (ص147).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «تَسَحَّرُوا، فَإِنَّ فِي السَّحُورِ بَرَكَةً».
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ku yi sahur, domin lallai cewa akawai albarka a cikin sahur".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kwaɗaitar akan sahur shi ne cin (abin ci) a ƙarshen dare dan yin tanadi ga azimi; domin cewa a cikinsa akwai (albarka) alheri mai yawa na lada da sakamako, da tashi a ƙarshen dare dan addu'a, da ƙarfafuwa akan azimi, da nishaɗuwa gare shi, da kuma sauƙaƙa wahalarsa.
Fa’idoji
- An so sahur da riko umarnin shari'a da aikata shi.
- Ibnu Hajar ya ce a cikn Fathul Bari: Albarka a cikin sahur tana samuwa ne ta ɓangarori masu yawa, su ne bin sunna, da saɓawa Ahlul kitabi, da ƙarfafuwa da shi akan ibada, da ƙari a cikin nishaɗi, da tunkuɗe munanan ɗabi'u wanda yunwa take taso shi, da kawo sababin sadaka ga wanda yake roƙo a wannan lokacin ko yake haɗuwa da shi akan cin abin ci, da sabbaba zikiri da addu'a a lokacin ana fatan amsawa, da riskar niyyar azimi ga wanda ya rafkana daga gareta kafin ya yi bacci.
- Kyakkyawar koyarwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - inda yake haɗa hukunci da hikima; dan ƙirji ya buɗe da shi, kuma a san matsayin shari'a da shi.
- Ibnu Hajar ya ce: Sahur yana samuwa ne da mafi ƙarancin abinda mutum yake samunsa na abin ci da abin sha.
Madogara
صحيح البخاري (3/ 29) (1923).
صحيح مسلم (2/ 770) (1095).
تيسير العلام، لعبد الله البسام (ص317).
تنبيه الأفهام شرح عمدة الإحكام، لابن عثيمين (3/ 416).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن عمرو بن العاص رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «فَصْلُ مَا بَيْنَ صِيَامِنَا وصِيَامِ أهْلِ الكِتَابِ، أكْلَةُ السَّحَرِ».
An rawaito daga Amr Bn Al-As -Allah ya yarda da shi- cewa Manzon Allah ya ce:"Ka Sadar da Azumin mu da azumin Ahlulkitab cin Sahur"
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara
- شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين، نشر: دار الوطن للنشر، الرياض، الطبعة: 1426ه.
- رياض الصالحين، للنووي، تحقيق: ماهر الفحل، دار ابن كثير - بيروت، الطبعة الأولى، 1428ه- 2007م.
- صحيح مسلم, ترقيم محمد فؤاد عبد الباقي, دار إحياء التراث العربي, بيروت.
- نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين, مؤسسة الرسالة, الطبعة الرابعة عشر, 1407ه.
- كنوز رياض الصالحين، نشر: دار كنوز إشبيليا، الطبعة الأولى، 1430ه - 2009م.
- بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي، ط1، دار ابن الجوزي، الدمام، 1415ه.
- المنهاج شرح صحيح مسلم بن الحجاج، للنووي، دار إحياء التراث العربي - بيروت، الطبعة الثانية، 1392.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أنس بن مالك رضي الله عنه قال: كان رسولُ اللهِ صلى الله عليه وسلم يُفطِر قبْل أن يصلي على رُطَبات، فإن لم تكنْ رُطَباتٌ فَتُمَيْراتٌ، فإن لم تكنْ تُمَيْراتٌ، حَسَا حَسَواتٍ مِن ماء.
An rawaito daga Anas Bn Malik -Allah ya yarda da shi-ya ce:Manzon Allah ya kasance yana bude baki da danyan dabino kafin yayi salla, idan babu danyan dabino sai yayi da bushasshen Dabino, idan babu sai ya kurbi wani abu daga Ruwa"
Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shiDarajaHasan ne
Madogara
سنن الترمذي، للإمام محمد بن عيسى الترمذي، تحقيق أحمد شاكر وآخرين، مكتبة الحلبي - مصر، الطبعة الثانية، 1388هـ.
رياض الصالحين من كلام سيد المرسلين، للإمام أبي زكريا النووي، تحقيق د. ماهر الفحل، دار ابن كثير - دمشق، الطبعة الأولى، 1428هـ.
سلسلة الأحاديث الصحيحة، للشيخ محمد ناصر الدين الألباني، مكتبة المعارف - الرياض، 1415هـ.
شرح رياض الصالحين، للشيخ محمد بن صالح العثيمين، مدار الوطن، الرياض، 1426هـ.
فيض القدير شرح الجامع الصغير، تأليف عبدالرؤوف المناوي، دار الحديث - القاهرة.
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، تأليف د. مصطفى الخِن وغيره، مؤسسة الرسالة - بيروت، الطبعة الرابعة عشر، 1407هـ.
سنن أبي داود, أبو داود سليمان بن الأشعث السِّجِسْتاني, المحقق: محمد محيي الدين عبد الحميد, المكتبة العصرية، صيدا – بيروت.
مسند الإمام أحمد بن حنبل، تحقيق: شعيب الأرنؤوط - عادل مرشد، وآخرون، نشر: مؤسسة الرسالة، الطبعة الأولى، 1421هـ - 2001م.
فيض القدير شرح الجامع الصغير, زين الدين محمد المدعو علي بن زين العابدين, الناشر: المكتبة التجارية الكبرى - مصر, الطبعة الأولى، 1356.
زاد المعاد في هدي خير العباد, ابن قيم الجوزية, الناشر: مؤسسة الرسالة، بيروت - مكتبة المنار الإسلامية، الكويت, الطبعة: السابعة والعشرون, 1415هـ - 1994م.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comKowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com