Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Lallai a cikin aljanna akwai wata ƙofa ana kiranta Rayyanu, masu azumi ne za su shiga ta cikin ta a ranar Alƙiyama, ba wanda zai shiga ta nan in ba su ba

عَنْ ‌سَهْلٍ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «إِنَّ فِي الْجَنَّةِ بَابًا يُقَالُ لَهُ الرَّيَّانُ، يَدْخُلُ مِنْهُ الصَّائِمُونَ يَوْمَ الْقِيَامَةِ، لَا يَدْخُلُ مِنْهُ أَحَدٌ غَيْرُهُمْ، يُقَالُ: أَيْنَ الصَّائِمُونَ، فَيَقُومُونَ لَا يَدْخُلُ مِنْهُ أَحَدٌ غَيْرُهُمْ، فَإِذَا دَخَلُوا أُغْلِقَ، فَلَمْ يَدْخُلْ مِنْهُ أَحَدٌ».
Daga Sahl - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Lallai a cikin aljanna akwai wata ƙofa ana kiranta Rayyanu, masu azumi ne za su shiga ta cikin ta a ranar Alƙiyama, ba wanda zai shiga ta nan in ba su ba, za'a ce: Ina masu azumi? sai su tashi, babu wanda zai shiga ta nan in ba su ba, idan suka shige za'a kulleta, ba wanda zai shiga ta ita".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa akwai wata ƙofa daga cikin ƙofofin aljanna ana kiranta: Kofar Rayyan, masu azimi zasu shigeta ranar alƙiyama, babu wanda zai shiga (aljanna) ta kofar sai su, za’a yi kira: Ina masu azimi, sai su miƙe su shiga, waninsu ba zai shiga ba, idan na ƙarshensu ya shiga sai akulleta, babu wani da zai shiga bayan nan.

Fa’idoji
  1. Nawawi ya ce: A cikin hadisin akwai falalar azimi da kuma girman masu azimin.
  2. Allah Ya ware wata ƙofa daga cikin ƙofofin aljanna guda takwas ga masu azimi, idan suka shiga ta kofar sai akulleta.
  3. Bayanin cewa aljanna tana da ƙofofi.
  4. Sindi ya ce: Faɗinsa: (Ina masu azimi), wato masu yawaita yin azimi kamar mai adalci da azzalimi, ana faɗin haka ga wanda ya saba da hakan, ba ga wanda ya aikata sau ɗaya ba kawai.
  5. (al-Rayyan) yana nufin wacce take ƙosarwa; domin cewa masu azimi suna jin ƙishirwa musammanma dai acikin kwanukan bazara masu tsawo masu zafi; sai a yi musu sakayya da ambatan wannan ƙofar da abinda yake keɓantarsu da shi da sunan ƙofar Arrayyan, kuma an ce Arrayyan wato Fa'alan mai yawan ƙoshi kishiyar ƙishirwa, an anbaceta da shi; domin cewa ita sakamakon masu azimi ce saboda ƙishirwarsu da kuma yunwarsu.
Madogara

صحيح البخاري (3/ 25) (1896). صحيح مسلم (2/ 808) (1152). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 360). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (2/ 868). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (5/ 270).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
FALALAR AZUMI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com