عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «قَالَ اللَّهُ: كُلُّ عَمَلِ ابْنِ آدَمَ لَهُ، إِلَّا الصِّيَامَ، فَإِنَّهُ لِي وَأَنَا أَجْزِي بِهِ، وَالصِّيَامُ جُنَّةٌ، وَإِذَا كَانَ يَوْمُ صَوْمِ أَحَدِكُمْ فَلاَ يَرْفُثْ وَلاَ يَصْخَبْ، فَإِنْ سَابَّهُ أَحَدٌ أَوْ قَاتَلَهُ، فَلْيَقُلْ إِنِّي امْرُؤٌ صَائِمٌ، وَالَّذِي نَفْسُ مُحَمَّدٍ بِيَدِهِ، لَخُلُوفُ فَمِ الصَّائِمِ أَطْيَبُ عِنْدَ اللَّهِ مِنْ رِيحِ المِسْكِ، لِلصَّائِمِ فَرْحَتَانِ يَفْرَحُهُمَا: إِذَا أَفْطَرَ فَرِحَ، وَإِذَا لَقِيَ رَبَّهُ فَرِحَ بِصَوْمِهِ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Allah Ya ce: Dukkan aikin ɗan Adam nasa ne, sai azimi, lallai shi nawa ne kuma nine zan yi sakayya da shi, azimi garkuwa ne, idan yinin azimin ɗayanku ya kasance to kada ya yi kwarkwasa kada ya yi zancen banza, idan wani ya zage shi ko ya yi faɗa da shi, to ya ce lallai ni mai azimi ne, na rantse da wanda ran (Annabi) Muhammad yake a hannunSa, bashin bakin mai azimi shi ne mafi ɗaɗi a wurin Allah daga ƙanshin almiski, mai azimi yana da farin ciki biyu da zai yi farin ciki da su: Idan zai yi buɗa baki zai yi farin ciki, kuma idan ya gamu da Ubangijinsa zai yi farin ciki da aziminsa".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Yana faɗa a cikin Hadisi Ƙudsi:
Dukkan aikin Ɗan Adam ana ninka kyakkyawa da kwatankwacinsa goma zuwa ninki ɗari bakwai, sai azimi; shi nawa ne riya ba ta shiga cikinsa, kuma nine zan yi sakayya da shi, sai in kaɗaita da sanin gwargwadan ladansa da kuma ninka kyawawan (ladansa).
Sannan Ya ce: (Azimi garkuwa ne) kuma kariya ne kuma sitira ne kuma katanga ne mai katangewa daga wuta; domin cewa shi kamewa ne daga sha'awowi da afkawa cikin zunubai, wuta kuma abar kewayewa ce da sha'awowi.
(Idan yinin azimin ɗayanku ya kasance to kada ya yi kwarkwasa) da yin jima'i da abubuwan gabatarwarsa, ko mummunan zance kai tsaye.
(Kada ya yi zancen banza) da yin husuma da kuma kururuwa.
(Idan wani ya zage shi ko ya yi faɗa da shi) a cikin Ramadan to ya ce: Lallai ni mai azimi ne; wataƙila ya ƙyale shi, idan ya nace sai dai faɗa to a haƙiƙa to sai ya tunkuɗe shi da mafi sauƙi, sai mafi sauƙi kamar wanda ya shigo maka gida.
Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi rantsuwa da wanda ransa yake a hannunSa cewa canzawar bashin bakin mai azimi saboda azimin ya fi daɗi a wurin Allah ranar alƙiyama daga ƙanshin almiski a wurinku, kuma ya fi yawan lada daga almiski abin so gare shi a ranakun juma'a da kuma majalisan zikiri.
Mai azimi yana da farin ciki biyu da zai yi farin ciki da su:
Idan zai yi buɗa baki zai yi farin ciki da gushewar yunwarsa da kuma ƙishirwarsa saboda yadda aka halatta masa buda baki.
Kuma zai yi farin ciki da cikar aziminsa da kuma kammala bautarsa, da kuma sauƙi daga Ubangijinsa, da taimako akan aziminsa na gaba.
(Idan ya gamu da Ubangijinsa zai yi farin ciki da aziminsa) da sakamakonsa da kuma ladansa.
Fa’idoji
- Falalar azimi kuma shi yana kiyaye maishi a duniya daga sha'awowi, a lahira kuma daga azabar wuta.
- Daga ladubban azimi barin zancen alfasha da zancen mara anfani, da kuma haƙuri akan cutarwar mutane da fuskantar munanawarsu da yin haƙuri da kuma kyautatawa.
- Mai azimi ko mai ibada idan ya yi farin ciki saboda cikar bautarsa da kuma ƙarewa daga gareta to hakan ba zai tauye ladansa a lahira ba.
- Cikakken farin ciki shi ne na haɗuwa da Allah - Maɗaukakin sarki -, lokacin da ake cika wa masu haƙuri da masu azimi ladansu ba tare da hisabi ba.
- Sanar da mutane aikin ɗa'a a lokacin buƙata da maslaha ba ya daga cikin riya saboda faɗinsa: (Lallai ni mai azimi ne).
- Mai azimin da ya cika aziminsa shi ne wanda gaɓɓansa suka yi azimi daga zunubai, kuma harshensa daga ƙarya da alfasha, da faɗin zur, cikinsa kuma daga abin ci da abin sha.
- Karfafawar hani daga zance mara anfani da husuma da ihu a lokacin azimi, inba haka ba to wanda ba ya azimi ma an hana shi hakan.
- Wannan hadisin yana daga abin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yake ruwaito shi daga Ubangijinsa, ana ambatonsa da Hadisi Ƙudsi, ko Ilahi, shi ne wanda lafazinsa da ma'anarsa daga Allah ne, sai dai cewa shi babu abubuwan da Alƙur’ani ya keɓannta da su a cikinsa, waɗanda ya keɓanta da su daga waninsa, kamar bauta da karanta shi, da yin tsarki sabo da shi da I’IJAZ (ƙalubalanta) da gajiyarwa, da sauransu.
Madogara
صحيح البخاري (3/ 26) (1904).
صحيح مسلم (2/ 807) (1151).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 357).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (2/ 866).
كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (15/ 5).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (5/ 265).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ سَهْلٍ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «إِنَّ فِي الْجَنَّةِ بَابًا يُقَالُ لَهُ الرَّيَّانُ، يَدْخُلُ مِنْهُ الصَّائِمُونَ يَوْمَ الْقِيَامَةِ، لَا يَدْخُلُ مِنْهُ أَحَدٌ غَيْرُهُمْ، يُقَالُ: أَيْنَ الصَّائِمُونَ، فَيَقُومُونَ لَا يَدْخُلُ مِنْهُ أَحَدٌ غَيْرُهُمْ، فَإِذَا دَخَلُوا أُغْلِقَ، فَلَمْ يَدْخُلْ مِنْهُ أَحَدٌ».
Daga Sahl - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Lallai a cikin aljanna akwai wata ƙofa ana kiranta Rayyanu, masu azumi ne za su shiga ta cikin ta a ranar Alƙiyama, ba wanda zai shiga ta nan in ba su ba, za'a ce: Ina masu azumi? sai su tashi, babu wanda zai shiga ta nan in ba su ba, idan suka shige za'a kulleta, ba wanda zai shiga ta ita".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa akwai wata ƙofa daga cikin ƙofofin aljanna ana kiranta: Kofar Rayyan, masu azimi zasu shigeta ranar alƙiyama, babu wanda zai shiga (aljanna) ta kofar sai su, za’a yi kira: Ina masu azimi, sai su miƙe su shiga, waninsu ba zai shiga ba, idan na ƙarshensu ya shiga sai akulleta, babu wani da zai shiga bayan nan.
Fa’idoji
- Nawawi ya ce: A cikin hadisin akwai falalar azimi da kuma girman masu azimin.
- Allah Ya ware wata ƙofa daga cikin ƙofofin aljanna guda takwas ga masu azimi, idan suka shiga ta kofar sai akulleta.
- Bayanin cewa aljanna tana da ƙofofi.
- Sindi ya ce: Faɗinsa: (Ina masu azimi), wato masu yawaita yin azimi kamar mai adalci da azzalimi, ana faɗin haka ga wanda ya saba da hakan, ba ga wanda ya aikata sau ɗaya ba kawai.
- (al-Rayyan) yana nufin wacce take ƙosarwa; domin cewa masu azimi suna jin ƙishirwa musammanma dai acikin kwanukan bazara masu tsawo masu zafi; sai a yi musu sakayya da ambatan wannan ƙofar da abinda yake keɓantarsu da shi da sunan ƙofar Arrayyan, kuma an ce Arrayyan wato Fa'alan mai yawan ƙoshi kishiyar ƙishirwa, an anbaceta da shi; domin cewa ita sakamakon masu azimi ce saboda ƙishirwarsu da kuma yunwarsu.
Madogara
صحيح البخاري (3/ 25) (1896).
صحيح مسلم (2/ 808) (1152).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 360).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (2/ 868).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (5/ 270).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أبي هريرة رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «مَنْ صَامَ رَمَضَانَ إِيمَانًا وَاحْتِسَابًا غُفِرَ لَهُ مَا تَقَدَّمَ مِنْ ذَنْبِهِ»
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya azumci Ramadan yana mai imani da neman lada za'a gafarta masa abin da ya gabata daga zunubinsa".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana ba da labari cewa wanda ya azumci watan Ramadan yana mai imani da Allah, yana mai gasgatawa da wajabcin azumin da abinda Allah - Maɗaukakin sarki - Ya yi tanadi na gwaggwaɓan ladaddaki da sakamako, yana mai nufin zatin Allah - Maɗauakakin sarki - da shi ba don riya ko jiyarwa ba, za'a gafarta masa zunubansa da suka shuɗe.
Fa’idoji
- FALALAR TSARKAKE NIYYA DA MUHIMMANCINSA A AZUMIN RAMADAN DA WANINSA NA AYYUKA NA GARI.
Madogara
صحيح البخاري (1/ 16) (38).
صحيح مسلم (1/ 523) (760).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 361).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمصطفى الخِن وغيره (2/ 868).
كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (15/ 40).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (5/ 270).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَن عَبْدِ اللَّهِ بنِ مَسْعُودٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: كُنَّا مَعَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقَالَ: «مَنِ اسْتَطَاعَ البَاءَةَ فَلْيَتَزَوَّجْ، فَإِنَّهُ أَغَضُّ لِلْبَصَرِ، وَأَحْصَنُ لِلْفَرْجِ، وَمَنْ لَمْ يَسْتَطِعْ فَعَلَيْهِ بِالصَّوْمِ، فَإِنَّهُ لَهُ وِجَاءٌ».
Daga Abdullahi ɗan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Mun kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: "Duk wanda yake da iko a cikinku to ya yi aure, domin cewa shi ne yafi rintse ido, kuma ya fi katange farji, wanda ba zai iya ba to na umarce shi da azimi, domin shi kariyane gare shi".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kwaɗaitar da wanda yake da iko akan jima'i da ɗawainiyar aure da ya yi aure; domin cewa shi yafi kiyaye gani daga haram, kuma ya fi tsananin katange farjinsa, da kuma hana afkawa cikin alfasha, wanda ba zai iya ɗaukar ɗawainiyar aure ba alhali shi yana mai iko akan jima'i to ya yin azimi domin cewa shi yana yanke sha'awar farji da sharrin maniyyi.
Fa’idoji
- Kwaɗayin Musulunci akan sabubban kamewa da kuɓuta daga alfasha.
- Kwaɗaitar da wanda ba zai iya ɗaukar nauyin ɗawainiyar aure ba da ya yi azimi; domin cewa shi yana raunana sha'awa.
- Ta yadda ya kamanta azimi da kariya; domin kariya (dandaƙa) ita ce kwankwatsa jijiyoyin maraina, da zarar sun tafi sai sha'awar jima'i ta tafi da tafiyarsu, haka nan azimi, shi mai raunana sha'awar jima'i ne.
Madogara
صحيح البخاري (3/ 26) (1905).
صحيح مسلم (2/ 1018) (1400).
الإلمام بشرح عمدة الأحكام للشيخ ،لإسماعيل الأنصاري (2/ 57).
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، لعبد الله البسام (ص565).
خلاصة الكلام شرح عمدة الأحكام، لفيصل آل مبارك (ص281).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أبي أمامة رضي الله عنه مرفوعاً: «من صام يوماً في سبيل الله جعل الله بينه وبين النار خَنْدَقًا كما بين السماء والأرض».
An karbo daga Abu Umama -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Annabi: "Duk wanda ya yi Azumi daya Saboda Allah Allah zai sanya wani gwalalo tsakaninsa da Wuta kamar nisan Sama da Kasa"
Al-Tirmithi Ya Rawaito shiDarajaHasan ne
Sharhi
Cikin wannan Hadisin akwai Bayanin Falalar Azumin wata Rana daya Sabida Allah, yadda Allah zai tserar da shi daga Wuta kuma ya nisanta shi ga barinta Kamar nisan sama da Kasa.
Madogara
سنن الترمذي، تحقيق بشار عواد، دار الغرب الإسلامي – بيروت، 1998 م.
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين, مؤسسة الرسالة, الطبعة الرابعة عشر, 1407ه.
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي, دار ابن الجوزي.
دليل الفالحين لطرق رياض الصالحين لمحمد بن علان الصديقي, دار الكتاب العربي.
كنوز رياض الصالحين بإشراف حمد العمار, دار كنوز إشبيليا, الطبعة الأولى, 1430ه.
سلسلة الأحاديث الصحيحة، محمد ناصر الدين الألباني، دار المعارف، 1415ه.
شرح الأربعين النووية، لعطية بن محمد سالم.
مصابيح التنوير على صحيح الجامع الصغير، تأليف الألباني، إعداد معتز أحمد.
تأسيس الأحكام بشرح عمدة الأحكام، أحمد النجمي، دار علماء السلف.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ: «إِذَا جَاءَ رَمَضَانُ فُتِّحَتْ أَبْوَابُ الْجَنَّةِ، وَغُلِّقَتْ أَبْوَابُ النَّارِ، وَصُفِّدَتِ الشَّيَاطِينُ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Idan (watan) Ramadan ya zo sai a buɗe ƙofofin aljanna, kuma a kukkule ƙofofin wuta, a ɗaɗɗaure shaiɗanu".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa idan watan Ramadan ya shiga sai al'amura uku su faru: Na farko: Za'a buɗe ƙofofin aljanna ba za'a kulle wata ƙofa ba daga cikinsu. Na biyu: Za'a kulle ƙofofin wuta, kuma ba za'a buɗe wata ƙofa daga cikinsu ba. Na uku: Za'a ɗaure shaiɗanu da aljanu masu tsaurin kai da sarƙoƙi, ba zasu kai zuwa ga abinda suke tsira da shi a cikin wanin (watan) Ramadan ba. Dukkanin wannan dan girmamawa ne ga wannan watan, da kwaɗaitar da masu aiki akan yawaita ayyukan ɗa'a na sallah da sadaka da zikiri da karatun Alkur'ani da wanin haka; da kuma nisantar zunubai da saɓo.
Fa’idoji
- Falalar watan Ramadan.
- Yi wa masu azimi albishir a cikinsa da cewa wannan watan mai albarka mausimi ne na ibada da alheri.
- A cikin ɗaure shaiɗanu a cikin Ramadan akwai nuni zuwa ɗauke uzurin mukallafi, kamar cewa shi ana ce masa ne: Haƙiƙa an ɗaure shaiɗanu daga gareka dan haka kada ka bada uzuri da su a cikin barin aikin ɗa'a ko a cikin aikata saɓo,
- AlKurɗubi ya ce: Idan an ce: Yaya muke ganin sharruka da saɓo masu yawa suna faruwa a cikin (watan) Ramadan ?da a ce an ɗaure shaiɗanu da hakan bai faru ba? To amsa (ita ce ace): Cewa su (sharruka) suna ƙaranta ne daga masu azimi azimin da aka kiyaye sharuɗɗansa kuma aka lura da ladubbansa, ko kuma waɗanda ake ɗaurewa wasu daga cikin shaiɗanu ne kawai sune masu tsaurin kai ba dukkansu ba kamar yadda ya gabata a cikin wasu daga ruwayoyi, ko kuma abin nufi ƙaranta sharrukansu a cikinsa, to wannan wani al'amari ne abin gani, domin cewa afkuwar hakan a cikinsa shi ne mafi ƙaranci daga waninsa, dan ba ya lazimta daga daure gabadayansu cewa sharri ko sabo ba zai faru ba; domin akwai sabubba ga hakan banda shaidanu kamar munanan rayuka da al'adu munana da kuma shaidanun mutane.
Madogara
صحيح البخاري (3/ 25) (1899).
صحيح مسلم (2/ 758) (1079).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 362).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (5/ 273).
كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (15/ 46).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 869).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comKowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com