Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Babu wani yinin da bayi zasu wayi gari a cikinsa sai (akwai) wasu mala'iku biyu suna sauka, ɗayansu zaice: Ya Allah Ka bada mayewa ga mai ciyarwa (mai kyauta), ɗayan kuma zaice: Ya Allah ka bada ɓarna ga mai riƙewa (mai rowa)

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «مَا مِنْ يَوْمٍ يُصْبِحُ العِبَادُ فِيهِ إِلَّا مَلَكَانِ يَنْزِلاَنِ، فَيَقُولُ أَحَدُهُمَا: اللَّهُمَّ أَعْطِ مُنْفِقًا خَلَفًا، وَيَقُولُ الآخَرُ: اللَّهُمَّ أَعْطِ مُمْسِكًا تَلَفًا».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Babu wani yinin da bayi zasu wayi gari a cikinsa sai (akwai) wasu mala'iku biyu suna sauka, ɗayansu zaice: Ya Allah Ka bada mayewa ga mai ciyarwa (mai kyauta), ɗayan kuma zaice: Ya Allah ka bada ɓarna ga mai riƙewa (mai rowa)".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa a kowane yinin da rana zata ɓullo a cikinsa akwai wasu mala'ilku biyu zasu sauka suna masu kira, ɗayansu yana cewa: Ya Allah Ka baiwa mai ciyarwa a ayyukan ɗa'a da iyalai da baƙi da abubuwan alheri mayewa Ka canja masa mafi alheri a cikin abinda ya ciyar, kuma Ka yi masa albarka. Ɗayan kuma yana cewa: Ya Allah Ka bawa mai riƙewa (mai rowa) ɓaci ka halakar da dukiyarsa wacce ya hanata ga waɗanda suka cancanceta.

Fa’idoji
  1. Halaccin addu'a ga mai kyauta dan Allah y ƙara masa a abinda ya bayar, kuma Ya maye masa da mafi alheri daga abinda ya ciyar, da kuma halaccin mummunar addu'a akan marowaci da ɓata dukiyarsa wacce ya yi rowa da ita ya kuma hana ciyarwarta a cikin abinda Allah Ya wajabta akansa.
  2. Addu'ar mala'iku ga muminai na gari masu ciyarwa da alheri da kuma albarka, kuma cewa addu'arsu abar karɓa ce.
  3. Kwaɗaitarwa akan ciyarwa a cikin wajibai da nafilfili; kamar ciyarwa ga iyali, da sada zumunci, da ƙofofin alheri.
  4. Bayanin falalar mai ciyarwa a cikin fuskokin alheri, kuma ƙarshensa shi ne cewa Allah Zai maye masa gurbin (abinda ya ciyar), Allah - Maɗaukain sarki - Ya ce: {Abinda kuka ciyar na wani abu to Shi Mai maye gurbinsa ne kuma Shi ne mafi alherin masu azirtawa} [Saba'i: 39].
  5. Wannan mummunar addu'ar akan mai riƙewa ne daga ciyarwa ta wajibi, amma ciyarwa ta mustahabbi ba zata shiga ba; domin mai ita ba ya cancantar irin wannan addu'ar.
  6. Haramcin rowa da ƙwauro.
Madogara

صحيح البخاري (2/ 115) (1442). صحيح مسلم (2/ 700) (1010). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (3/ 157). نزهة المتقين بشرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 293). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 376).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
SADAKA TA NAFILA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com