Musulmai sun kasance suna fitar da zakkar fidda kai Sa’i ɗaya na abinci a zamanin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da zamanin Khalifofi masu shiryarwa a bayansa daga ƙaramin (yaro) da babba. Abin cin su ya kasance sha'ir ne da (zabibi): Bushasshen inibi, da (cukwi): Busasshen nono da kuma dabino. Gwargwadan Sa’i mudu huɗu ne, mudu kuma ya yi daidai da cikin tafi biyu na namiji madaidaici (ba babba ba ba kuma ƙarami ba). Lokacin da Mu'awiya - Allah Ya yarda da shi - ya zo Madina alhali shi yana Khalifa, kuma alkamar Sham ta yi yawa, sai ya yi huɗuba sai ya ce: Lallai ni ina ganin cewa mudu biyu na alkamar Sham (rabin Sa’i), sun yi daidai da Sa’i ɗaya na dabino, sai mutane suka yi riƙo da hakan. Abu Sa'idul Khudri - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Amma ni ba zan gushe ba ina fitar da shi kamar yadda na kasance ina fitar da shi a zamanin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi har abada muddin dai ina raye.
- Bayanin gwargwadan sadakar fidda kai a zamanin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, Sa’i ne na abinci koda jinsi da ƙima sun saɓa.
- Dukkan abin cin 'yan Adam mai isuwa ne a (zakkar) fidda kai, kawai an keɓanci nau'ikan nan huɗu da ambato ne; domin cewa sune abincin mutane a zamanin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
- Fitar da wanin abinci na sulalla da kuɗi, ba ya isuwa a (zakkar) fidda kai.
- AlNawawi ya faɗa a a Sharhin Muslim: Idan sahabbai suka saɓa to maganar sashinsu ba ta zama mafi cancanta daga sashi ba, sai mu koma zuwa ga wani dalilin daban, mun samu cewa zahirin hadisan da ƙiyasin sun haɗu a kan sharɗanta kwano na alkama kamar waninta, sai dogaro a kansa ya wajaba.
- Ibnu Hajar ya ce: A cikin hadisin Abu Sa'id akwai abinda ya kasance akansa na tsananin biyayya da riƙo da tafarkin magabata, da barin bauɗewa zuwa ijtihadi tare da samun nassi, kuma a cikin aikin Mu'awiya da amsawar mutane gare shi akwai nuni akan halaccin ijtihadi, kuma shi abin so ne, saidai ijtihadi tare da samuwar nassi to (zai zama) mai ɓataccen lura.
صحيح البخاري (2/ 131) (1508). صحيح مسلم (2/ 678) (985). تيسير العلام، لعبد الله البسام (ص309). تنبيه الأفهام شرح عمدة الإحكام، لابن عثيمين (3/ 409). الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (1/ 251).