Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

ZAKKAR FID-DA-KAI

Hadisai 3

Mun kasance muna fitar da zakkar fidda kai lokacin da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana cikinmu, daga kowane ƙaramin (yaro) da babba, ɗa ne ko bawa, Sa’i na abinci, ko Sa’i na cukwi, ko Sa’i na sha'ir, ko Sa’i na dabino, ko Sa’i na zabibi

عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الْخُدْرِيِّ رضي الله عنه قَالَ: كُنَّا نُخْرِجُ إِذْ كَانَ فِينَا رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ زَكَاةَ الْفِطْرِ، عَنْ كُلِّ صَغِيرٍ وَكَبِيرٍ، حُرٍّ أَوْ مَمْلُوكٍ، صَاعًا مِنْ طَعَامٍ، أَوْ صَاعًا مِنْ أَقِطٍ، أَوْ صَاعًا مِنْ شَعِيرٍ، أَوْ صَاعًا مِنْ تَمْرٍ، أَوْ صَاعًا مِنْ زَبِيبٍ، فَلَمْ نَزَلْ نُخْرِجُهُ حَتَّى قَدِمَ عَلَيْنَا مُعَاوِيَةُ بْنُ أَبِي سُفْيَانَ رضي الله عنه حَاجًّا، أَوْ مُعْتَمِرًا فَكَلَّمَ النَّاسَ عَلَى الْمِنْبَرِ، فَكَانَ فِيمَا كَلَّمَ بِهِ النَّاسَ أَنْ قَالَ: إِنِّي أَرَى أَنَّ مُدَّيْنِ مِنْ سَمْرَاءِ الشَّامِ، تَعْدِلُ صَاعًا مِنْ تَمْرٍ، فَأَخَذَ النَّاسُ بِذَلِكَ، قَالَ أَبُو سَعِيدٍ: فَأَمَّا أَنَا فَلَا أَزَالُ أُخْرِجُهُ كَمَا كُنْتُ أُخْرِجُهُ، أَبَدًا مَا عِشْتُ.
Daga Abu Sa'id Alkhudr - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Mun kasance muna fitar da zakkar fidda kai lokacin da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana cikinmu, daga kowane ƙaramin (yaro) da babba, ɗa ne ko bawa, Sa’i na abinci, ko Sa’i na cukwi, ko Sa’i na sha'ir, ko Sa’i na dabino, ko Sa’i na zabibi, kuma bamu gushe ba muna fitar da shi har saida Mu'awiya ɗan Abu Sufyan - Allah Ya yarda da shi - ya gabato gurinmu yana mai aikin Hajji, ko yana mai Umarah sai ya yi wa mutane magana akan minbari, ya kasance daga abinda ya yi wa mutane magana da shi cewa ya ce: Lallai ni na ga cewa mudu biyu na alkamar Sham, sun yi daidai da sa'i ɗaya na dabino, sai mutane suka yi riko da hakan, Abu sa'id ya ce: Ammma ni ba zan gushe ba ina fitar da shi kamar yadda na kasance ina fitar da shi, muddin dai na rayu har abada.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Musulmai sun kasance suna fitar da zakkar fidda kai Sa’i ɗaya na abinci a zamanin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da zamanin Khalifofi masu shiryarwa a bayansa daga ƙaramin (yaro) da babba. Abin cin su ya kasance sha'ir ne da (zabibi): Bushasshen inibi, da (cukwi): Busasshen nono da kuma dabino. Gwargwadan Sa’i mudu huɗu ne, mudu kuma ya yi daidai da cikin tafi biyu na namiji madaidaici (ba babba ba ba kuma ƙarami ba). Lokacin da Mu'awiya - Allah Ya yarda da shi - ya zo Madina alhali shi yana Khalifa, kuma alkamar Sham ta yi yawa, sai ya yi huɗuba sai ya ce: Lallai ni ina ganin cewa mudu biyu na alkamar Sham (rabin Sa’i), sun yi daidai da Sa’i ɗaya na dabino, sai mutane suka yi riƙo da hakan. Abu Sa'idul Khudri - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Amma ni ba zan gushe ba ina fitar da shi kamar yadda na kasance ina fitar da shi a zamanin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi har abada muddin dai ina raye.

Fa’idoji
  1. Bayanin gwargwadan sadakar fidda kai a zamanin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, Sa’i ne na abinci koda jinsi da ƙima sun saɓa.
  2. Dukkan abin cin 'yan Adam mai isuwa ne a (zakkar) fidda kai, kawai an keɓanci nau'ikan nan huɗu da ambato ne; domin cewa sune abincin mutane a zamanin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
  3. Fitar da wanin abinci na sulalla da kuɗi, ba ya isuwa a (zakkar) fidda kai.
  4. AlNawawi ya faɗa a a Sharhin Muslim: Idan sahabbai suka saɓa to maganar sashinsu ba ta zama mafi cancanta daga sashi ba, sai mu koma zuwa ga wani dalilin daban, mun samu cewa zahirin hadisan da ƙiyasin sun haɗu a kan sharɗanta kwano na alkama kamar waninta, sai dogaro a kansa ya wajaba.
  5. Ibnu Hajar ya ce: A cikin hadisin Abu Sa'id akwai abinda ya kasance akansa na tsananin biyayya da riƙo da tafarkin magabata, da barin bauɗewa zuwa ijtihadi tare da samun nassi, kuma a cikin aikin Mu'awiya da amsawar mutane gare shi akwai nuni akan halaccin ijtihadi, kuma shi abin so ne, saidai ijtihadi tare da samuwar nassi to (zai zama) mai ɓataccen lura.
Madogara

صحيح البخاري (2/ 131) (1508). صحيح مسلم (2/ 678) (985). تيسير العلام، لعبد الله البسام (ص309). تنبيه الأفهام شرح عمدة الإحكام، لابن عثيمين (3/ 409). الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (1/ 251).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Babu komai na Zakka akan Musulmi cikin dokinsa

عن أبي هريرة رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «ليس على المُسلِم في عبدِهِ وَلاَ فَرَسهِ صَدَقَة». وفي لفظ: «إلا زكاة الفِطر في الرقيق».
Daga Abu Huraira - Allah ya yarda da shi -:zuwa ga Annabi : "Babu komai na Zakka akan Musulmi cikin dokinsa "
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Angina Zakka ne kan daidaito da kuma Adalci, don haka Allah ya wajabta ta cikin Dukiyoyin Mawadata kuma wacce take karuwa da kuma wacce aka tanada don juyawa, kamar abubuwan da suke futa daga cikin Kasa, da kayan siyarwa, kuma Dukiyar da bata Karuwa, wacce aka tanada don ajiya da Amfani to wannan babu zakka acikinta; don kebantarwar Musulmi don bukatar kansa: kuma kamar Abun Hawansa, Kamar Doki, da Rakumi, da Mota, kuma haka bawansa da ya tanada don yi masa Hidima da shimfidar sa da kwanuka da aka tanada don amfani sai dai antogace Zakkar fidda kai, to lallai cewa Ta wajaba kuma koda ba'a tanadi ta ba don kasuwanci, domin suna danfare da jiki ba da Dukiya ba.

Madogara

عمدة الأحكام، تأليف: عبد الغني بن عبد الواحد المقدسي، تحقيق: محمود الأرناؤوط، دار الثقافة العربية ومؤسسة قرطبة، الطبعة الثانية، 1408هـ. تيسير العلام، تأليف: عبد الله بن عبد الرحمن البسام، تحقيق محمد صبحي بن حسن حلاق، مكتبة الصحابة ومكتبة التابعين، الطبعة العاشرة، 1426هـ. تأسيس الأحكام شرح عمدة الأحكام، تأليف: أحمد بن يحي النجمي: نسخة إلكترونية لا يوجد بها بيانات نشر. تنبيه الأفهام شرح عمدة الإحكام، تأليف: محمد بن صالح العثيمين، مكتبة الصحابة ومكتبة التابعين، الطبعة الأولى: 1426هـ. الإلمام بشرح عمدة الأحكام، تأليف: إسماعيل الأنصاري، مطابع دار الفكر، الطبعة الأولى:1381هـ. صحيح البخاري، تأليف: محمد بن إسماعيل البخاري، تحقيق: محمد زهير الناصر، الناشر: دار طوق النجاة الطبعة: الأولى 1422هـ. صحيح مسلم، تأليف: مسلم بن الحجاج النيسابوري، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، الناشر: دار إحياء التراث العربي - بيروت.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya wajabta zakkar fidda kai, Sa'i na dabino, ko Sa'i na alkama, akan bawa da ɗa, namiji da mace, ƙarami da babba cikin musulmai, kuma ya yi umarni a bada ita kafin fitar mutane zuwa sallah

عَنِ ابْنِ عُمَرَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا قَالَ: فَرَضَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ زَكَاةَ الفِطْرِ صَاعًا مِنْ تَمْرٍ، أَوْ صَاعًا مِنْ شَعِيرٍ، عَلَى العَبْدِ وَالحُرِّ، وَالذَّكَرِ وَالأُنْثَى، وَالصَّغِيرِ وَالكَبِيرِ مِنَ المُسْلِمِينَ، وَأَمَرَ بِهَا أَنْ تُؤَدَّى قَبْلَ خُرُوجِ النَّاسِ إِلَى الصَّلاَةِ.
Daga Ɗan Umar - Allah ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya wajabta zakkar fidda kai, Sa'i na dabino, ko Sa'i na alkama, akan bawa da ɗa, namiji da mace, ƙarami da babba cikin musulmai, kuma ya yi umarni a bada ita kafin fitar mutane zuwa sallah.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya wajabta zakkar fidda kai bayan (azimin) Ramadan, ita gwargwadan Sa'i ne (wanda) awonsa yakai mudun Nabiyyi huɗu. Mudun Nabiyyi: (Shi ne) cikin tafukan mutum madaidaici, na dabino ko alkama akan kowane musulmi; ɗa da bawa, namiji da mace, ƙarami da babba, hakan ga wanda a wajensa akwai abinda ya rage daga abin cin yininsa da darensa, (zai fitarwa) kansa da kuma wanda yake kula da su. Kuma ya yi umarni a bada ita kafin fitar mutane zuwa sallar idi.

Fa’idoji
  1. Zakkar fidda kai ta azimi tana wajaba a fitar wa yaro ita da babba, da ɗa da bawa, kuma ana yi wa waliyyin (yaro) da mamallakin (bawa) umarni da ita, kuma mutum yana fitarwa kansa da 'ya'yansa da wanda ciyarwarsu take wajaba akansa.
  2. Zakkar fidda kai ba ta wajaba daga ɗan tayi, saidai an so (a fitar masa).
  3. Bayanin abinda ake fitarwa a zakkar fidda kai, shi ne abincin mutane na al'ada.
  4. Wajabcin fidda ita kafin sallar idi, abinda ya fi ta kasance a safiyar idi, kuma fitar da ita yana halatta kafin idi da kwana ɗaya ko kwanaki biyu.
Madogara

صحيح البخاري (2/ 130) (1503). صحيح مسلم (2/ 679) (986). تيسير العلام، لعبد الله البسام (ص309). تنبيه الأفهام شرح عمدة الإحكام، لابن عثيمين (3/ 406). الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (1/ 249).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com