Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Cewa wani mutum ya tambayi Manzon Allah -tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi: Wanne aiki ne ya fi a Musulunci? ya ce: "Ka ciyar da abin ci, ka yi sallama ga wanda ka sani da wanda baka sani ba

عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عَمْرٍو رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا: أَنَّ رَجُلًا سَأَلَ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: أَيُّ الإِسْلاَمِ خَيْرٌ؟ قَالَ: «تُطْعِمُ الطَّعَامَ، وَتَقْرَأُ السَّلاَمَ عَلَى مَنْ عَرَفْتَ وَمَنْ لَمْ تَعْرِفْ».
Daga Abdullahi Dan Amr - Allah Ya yarda da su -: Cewa wani mutum ya tambayi Manzon Allah -tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi: Wanne aiki ne ya fi a Musulunci? ya ce: "Ka ciyar da abin ci, ka yi sallama ga wanda ka sani da wanda baka sani ba".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

An tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Wadanne dabi'u ne na Musulunci suka fi? sai ya ambaci dabi'u biyu: Na farko: Yawaita ciyar da abin ci ga talakawa, sadaka da kyauta da saukar bako da walima za su shiga ciki, falalar ciyarwa tana karfafa alokutan yunwa da tsadar farashi. na biyu: Yin sallama ga kowanne musulmi, ka san shi ko ba ka san shi ba.

Fa’idoji
  1. Kwadayin sahabbai akan sanin dabi'un da zasu anfanar a duniya da lahira.
  2. Sallama da ciyar da abinci suna daga mafifitan ayyuka; Dan falalarsu da bukatuwar mutane garesu a kowanne lokaci.
  3. Da wadannan dabi'un ne kyautatawa take taruwa da fada da aikatawa, kuma ita ce mafi cikar kyautatawa.
  4. Wadannan dabi'un a cikin abinda yake rataya ne na mu'amalantar musulmai a tsakaninsu, akwai wasu dabi'un na mu'amalantar bawa ga Ubangijinsa.
  5. Farawa da sallama abin kebancewa ne tsakanin musulmai, ba'a Farawa kafirai da sallama.
Madogara

صحيح البخاري (1/ 12) (12). صحيح مسلم (1/ 65) (39). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 604). مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، لعلي القاري (7/ 2936).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
FALALOLI DA LADUBBA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com