Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Mai yanke zumunci ba zai shiga aljanna ba

عن جُبَير بن مُطْعِم رضي الله عنه أنه سمع النبي صلى الله عليه وسلم يقول: «لَا يَدْخُلُ الْجَنَّةَ قَاطِعُ رَحِمٍ».
Daga Jubair ɗan Mut'im - Allah Ya yarda da shi - cewa ya ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana cewa; "Mai yanke zumunci ba zai shiga aljanna ba"
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labarin cewa wanda ya yanke abin da yake wajaba daga 'yan uwansa na haƙƙoƙi, ko ya cutar da su ya munana musu, to, ya cancanci ba zai shiga aljanna ba.

Fa’idoji
  1. Yanke zumunci laifi ne daga manyan laifuka.
  2. Sa da zumunci yana kasancewa ne gwargwadon abin da aka yi sabo a kansa, yana banbanta da banbantar wurare da zamaninnika da mutane.
  3. Sa da zumunci yana kasancewa ne da ziyara da sadaka, da kyautatawa garesu, da duba marasa lafiya, da umartarsu da aikin alheri, da hanasu daga abin ƙi, da makamancin hakan.
  4. A duk lokacin da yanke zumuci ya zama da mafi kusanci, to, zai zama ya fi tsananin laifi.
Madogara

صحيح مسلم (4/ 1981) (2556). صحيح البخاري (8/ 5) (5984). شرح النووي على مسلم (16/ 113). منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (10/ 90). فتح ذي الجلال والإكرام بشرح بلوغ المرام، لابن عثيمين (6/ 277).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
FALALOLI DA LADUBBA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com