Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Kada ku zagi matattu; domin cewa sun iso zuwa abin da suka gabatar

عن عائشة رضي الله عنها قالت: قال النبي صلى الله عليه وسلم: «لَا تَسُبُّوا الْأَمْوَاتَ، فَإِنَّهُمْ قَدْ أَفْضَوْا إِلَى مَا قَدَّمُوا».
Daga A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Kada ku zagi matattu; domin cewa sun iso zuwa abin da suka gabatar".
Bukhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana bayyana haramcin zagin matattu da afkawa a cikin mutuncinsu, kuma wannan yana daga munanan ɗabi'u; domin sun kai zuwa abin da suka gabatar da shi na ayyuka na gari ko na banza, kamar yadda wannan zagin ba ya isa zuwa garesu, to, lallai cewa yana cutar da rayayyu.

Fa’idoji
  1. Hadisin dalili ne a kan haramcin zagin matattu.
  2. Barin zagin matattu a cikinsa akwai kula da maslahar rayayyu, da kiyaye zaman lafiyar jama'a daga gaba da ƙiyayya.
  3. Hikima a kan hana zaginsu, cewa sun isa zuwa abin da suka gabatar, to, zaginsu ba ya amfanarwa, kuma a cikinsa akwai cutarwa ga makusantansa rayayyu.
  4. Cewa ba ya kamata ga mutum ya faɗi abin da babu maslaha a cikinsa.
Madogara

صحيح البخاري (2/ 104) (1393). فتح ذي الجلال والاكرام بشرح بلوغ المرام، لابن عثيمين (2/ 631). منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (4/ 385). توضيح الأحكام من بلوغ المرام، للبسام (3/ 277).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
FALALOLI DA LADUBBA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com