Daga Abu Katada AsSulami - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan ɗayanku ya shiga masallaci, to, ya yi sallah raka'a biyu kafin ya zauna".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kwaɗaitar da wanda ya zo masallaci ya shige shi a kowanne lokaci, da kowacce manufa, ya yi sallah raka'a biyu kafin ya zauna, su ne raka'o'i biyun gaisuwar masallaci.
Fa’idoji
An so yin sallah raka'a biyu gaisuwa ga masallaci kafin zama.
Wannan umarni ne ga wanda ya yi nufin zama, wanda ya shiga masallaci ya fita kafin ya zauna umarnin bai shafe shi ba.
Idan mai sallah ya shiga (masallaci) alhali mutane suna cikin sallah, sai ya shiga cikinta tare da su, to, wannan ya wadatar masa daga raka'o'i biyun.
Madogara
صحيح البخاري (1/ 96) (444)، صحيح مسلم (1/ 495) (714)، المفهم لما أشكل من تلخيص كتاب مسلم (2/ 352)، فتح الباري لابن رجب (3/ 274)، التوضيح (5/524)، البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (15/ 287).
Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com