A kwai sallah tsakanin dukkan kiran sallah biyu, akwai sallah tsakanin dukkan kiran sallah biyu" sannan ana uku ya ce: "Ga wanda ya so
عَنْ عَبْدِ اللهِ بْنِ مُغَفَّلٍ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ النَّبِيُّ صلى الله عليه وسلم: «بَيْنَ كُلِّ أَذَانَيْنِ صَلَاةٌ، بَيْنَ كُلِّ أَذَانَيْنِ صَلَاةٌ» ثُمَّ قَالَ فِي الثَّالِثَةِ: «لِمَنْ شَاءَ».
Daga Abdullahi dan Mugaffal - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "A kwai sallah tsakanin dukkan kiran sallah biyu, akwai sallah tsakanin dukkan kiran sallah biyu" sannan ana uku ya ce: "Ga wanda ya so".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa akwai sallar nafila tsakanin kowanne kiran sallah da iƙama, kuma ya maimaita hakan sau uku, kuma ya bada bayani ana ukun cewa hakan mustahabbi ne ga wanda ya yi nufin yin sallah.
Fa’idoji
An so sallah tsakanin kiran sallah da iƙama.
Shiriyar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a maimaita magana, hakan dan jiyarwa da ƙarfafawa ga muhimmnacin abinda yake faɗa.
Abin nufi da kiran sallah biyu: Kiran sallah da iƙama, kuma ya anbace su da (lafazin) (Kiran sallah biyu) dan rinjayarwa, kamar wata biyu (Rana da wata) da Umar biyu (Abubakar da Umar).
Kiran sallah shi ne sanar da shigar lokaci, iƙama kuma ita ce sanar da halartar yin sallah.
Madogara
صحيح البخاري (1/ 128) (627)، صحيح مسلم (1/ 573) (838)، البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (16/ 671)، النهاية في غريب الحديث والأثر (31).
Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com