Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi sallar Asuba wata rana, sannan ya yi tambaya: Shin wane ya zo wannan sallar da muka yi? Sahabbai suka ce: A'a. Sannan ya ce: Shin wane ya zo ne? ga wani mutumin daban, Suka ce: A'a. (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Lallai sallar Asuba da Issha'i sune mafi nauyin salloli akan munafukai; dan rinjayar kasala a cikinsu, da kuma ƙarancin faruwar riya garesu, tunda ba'a ganinsu a cikin duhu. Da kun san yaku muminai abinda ke cikin sallolin Asuba da Issha'i na lada da sakamako mai ƙaruwa - domin lada yana kan gwargwadan wahala - da kun zo su koda da jan ciki ne da tafiya akan hannaye da gwiwowi. Kuma masu sahu na farko a kusancinsu da liman kamar sahun mala'iku ne a kusancinsu ga Allah - Maɗaukakin sarki -, da muminai suna sanin abinda ke cikin falalar sahun farko da sun yi tsere gare shi . Kuma lallai sallar namiji tare da namiji ita ce mafi girman sakamako da tasiri a sallarsa shi kaɗai, kuma sallarsa tare da maza biyu tafi tare da namiji ɗaya, Sallar da masallatan suka yi yawa a cikinta ita ce mafi soyuwa ga Allah kuma ta fi lada.
- Halaccin limamin masallaci ya bibiyi halayen mamu, da tambaya daga wanda ya bai zo ba daga cikinsu.
- Lazimtar sallar jam’i musamman ma dai sallar Issha'i da Asuba yana daga alamomin imani.
- Girman ladan sallolin Issha'i da Asuba; dan abinda ke cikin zuwa gare su na yaƙar zuciya da nacewa akan ɗa'a, sai ladansu ya zama mafi girma daga wasunsu.
- Sallar jama'a tana ƙulluwa ne daga mutum biyu zuwa sama.
- Bayanin falalar sahun farko, da kwaɗaitarwa a cikin gaggawa zuwa gare shi .
- Falalar yawan jama'a, domin cewa duk lokacin jama'a suka yi yawa ladan yafi yawa.
- Ayyuka na gari suna da fifikon lada gwargwadan fifitawar shari'a garesu, da kuma abinda suka siffantu da su na halaye.
سنن أبي داود (1/ 415) (554). سنن النسائي (2/ 104) (843). مسند أحمد (35/ 188) (21265). شرح الطيبي على مشكاة المصابيح، لشرف الدين الطيبي (4/ 1132). مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، لعلي القاري (3/ 838). سبل السلام شرح بلوغ المرام، للصنعاني (1/ 360 ). شرح سنن أبي داود، لعبد المحسن العباد (40/ 11).