Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa mafi alherin sahun maza a cikin sallah kuma mafi yawansu a lada da falala shi ne na farkonsu; dan kusancinsu ga liman da jinsu ga karatunsa da nisantarsu daga mata. Mafi sharrinsu kuma mafi ƙarancinsu a lada da falala, kuma mafi nisancinsu daga abin nema a shari'a shi ne ƙarshensu. Mafi alherin sahun mata na ƙarshensu; domin cewa yafi sutura garesu, kuma mafi nisanta daga cakuɗuwa da maza da ganinsu da fitinuwa da su, mafi sharrinsu na farkonsu; dan kusancinsu ga maza da bijirowa ga fitina.
- Kwaɗaitar da maza akan gaggawa zuwa biyayya da sahun farko a cikin salloli.
- Halaccin sallar mata a cikin masallaci tare da maza a cikin sahu mai zaman kansa, sai dai tare da suturtuwa da kamewa.
- Mata idan sun taru a cikin masallaci, to cewa su zasu zama sahu kamar sahun maza, kuma kada su rarrabu, kai wajibi ne su daidaitu a cikin sahu da toshe kafa, kamar yadda yake a cikin sahun maza.
- Bayanin tsananin kulawar shari'a ta hanyar kwaɗaitarwa da nisantar mata ga maza har a guraren ibada.
- Fifikon mutane a gwargwadan ayyukansu.
- AlNawawi ya ce: Amma sahun maza shi akan gamewarsa ne, to mafi alherinsa na farkonsa har abada, kuma mafi sharrinsu na ƙarshensu har abada. Amma sahun mata abin nufi da Hadisin: Sahun mata waɗanda zasu yi sallah tare da maza, amma idan zasu yi sallah daban ba tare da maza ba to su kamar maza ne; mafi alherin sahunsu na farkonsu kuma mafi sharrinsu na ƙarshensu.
- AlNawawi ya ce: Sahu na farko abin yabo wanda Hadisai suka zo da falalarsa da kwaɗaitarwa akansa shi ne sahun farko wanda yake bin liman; daidai ne ma'abocinsa ya zo ne da wuri ko a makare, kuma daidai ne, taƙaitawa ta ratsa shi ne da makamancinsa ko a'a.
صحيح مسلم (1/ 326) (440). سبل السلام شرح بلوغ المرام، للصنعاني (1/ 374 ). توضيح الأحكام مِن بلوغ المرام، لعبد الله البسام (2/ 495). فتح ذي الجلال والإكرام شرح بلوغ المرام، لابن عثيمين (2/ 272). مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، للتبريزي (3/ 851).