Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya gargaɗar daga wucewa ta gaban wanda yake sallar farilla ko nafila, kuma cewa da wanda yake aikata haka da gangan da ya san abinda zai haɗu da shi na laifi; da a ce ya zaɓi ya tsaya arba'in; to shi ne mafi alheri gare shi da ya wuce ta gabansa. Abu al-Nadhr maruwaicin hadisin ya ce: Ban sani ba ya ce kwanaki arba'in ne ko wata ko shekara.
- Haramcin wucewa ta gaban mai yin sallah, idan ba shi da sutra; ko kuma wucewa tsakaninsa da ita idan ya kasance yana da sutra.
- Ibnu Hajar ya ce: An yi saɓani a iyankance haka, an ce idan ya wuce tsakaninsa da tsakanin gwargwadan sujjadarsa, kuma an ce tsakaninsa da tsakaninsa gwargwadan zira'i uku, kuma an ce tsakaninsa da stakaninsa gwargwadan jifan dutse.
- Suyuɗi ya ce: Abin nufi da wucewa ta gabansa yana mai bijirewa, amma da a ce idan ya yi tafiya ta gabansa yana mai tafiya ta fuskar alƙibla to bai zama mai shiga cikin narkon ba.
- Abinda ya fi ga mai yin sallah shi ne kada ya yi sallah a hanyoyin mutane, da kuma guraren da babu makawa sai sun wuce ta gurin, dan kada ya bijirar da sallarsa ga tawaya, kuma a bijro wa mai wucewar ga zunubi, kuma wajibi ne a kansa ya sami sutra da kariya tsakaninsa da tsakanin mai wucewar.
- Ana fahimta daga gare shi cewa zunubin da ya jerantu akan saɓo a lahira ko da ya ƙaranta to mai girma ne daga kowace wahla a duniya duk yanda ta tsananta.
صحيح البخاري (1/ 108) (510). صحيح مسلم (1/ 363) (507). تيسير العلام، للبسام تيسير العلام (ص184). تنبيه الأفهام، لابن عثيمين (2/ 239). الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (1/ 154).