Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Lokuta uku Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana hana mu yin salla a cikinsu, ko binne mamatanmu a cikinsu

عَنْ عُقْبَةَ بْنَ عَامِرٍ الْجُهَنِيَّ رضي الله عنه قَالَ: ثَلَاثُ سَاعَاتٍ كَانَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَنْهَانَا أَنْ نُصَلِّيَ فِيهِنَّ، أَوْ أَنْ نَقْبُرَ فِيهِنَّ مَوْتَانَا: حِينَ تَطْلُعُ الشَّمْسُ بَازِغَةً حَتَّى تَرْتَفِعَ، وَحِينَ يَقُومُ قَائِمُ الظَّهِيرَةِ حَتَّى تَمِيلَ الشَّمْسُ، وَحِينَ تَضَيَّفُ الشَّمْسُ لِلْغُرُوبِ حَتَّى تَغْرُبَ.
Daga Uƙuba ɗan Amir al-Juhani - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Lokuta uku Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana hana mu yin salla a cikinsu, ko binne mamatanmu a cikinsu: Lokacin da rana ta fito a bayyane har sai ta ɗaga, da kuma lokacin da ta tsaya a tsakiyar sama har sai ranar ta karkace, da kuma lokacin da ranar ta kusa faɗuwa har sai ta faɗi.
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi hani a yi sallar nafila a lokuta uku, ko a yi ƙabari a binne matattu a cikinsu: Lokaci na farko: Lokacin da rana zata fito a bayyane, hakan a yayin farkon ɓullowarta har sai ta ɗaga gwargwadan goron mashi, shi ana ƙaddara shi da kwatankwacin rubu'in sa'a (minti sha biyar). Na biyu: Lokacin da rana ta tsaya a tsakiyar sama, to babu inuwa gareta ta ɓangaren gabas ko yamma har sai ta karkace daga tsakiyar sama, inuwa ta bayyana daga ɓangaren gabas yayin da farkon lokacin sallar Azahar yake farawa, kuma taƙaitaccen lokaci ne; shi gwargwadan kwatankwacin minti biyar ne. Na uku: Loakcin da ta karkace rana ta fara faɗuwa har sai ta faɗi.

Fa’idoji
  1. Lokutan da aka hana yin sallah a cikinsu kamar yadda wannan hadisin da wasu hadisan daban suka yi nuni akansa sune: Na farko: Bayan sallar Asuba har zuwa ɓullowar rana. Na biyu: Lokacin ɓullowar rana har sai ta ɗaga gwargwadan goron mashi a ganin ido; wato: Gwargwadan kwatankwacin minti goma sha biyar. Na uku: Lokacin da rana ta tsaya a tsakiya har sai rana ta karkace, hakan lokacin da wata inuwa ba zata wanzu ba a gabas ko a yamma ga wanda ya tsaya a garjin rana, wasu daga cikin malamai sun ƙaddara shi da kwatankwacin minti biyar. Na huɗu: Bayan sallar La'asar har sai rana ta faɗi. Na biyar: Lokacin fatsi-fatsin rana har sai ta faɗi.
  2. Hani akan yin sallah a waɗannan lokutan guda biyar waɗanda aka yi hani a cikinsu, an togance farillai da (salloli) masu sabubba daga hanin.
  3. Hani daga jinkirta binne (mamaci) da gangan zuwa waɗannan lokutan guda uku ƙuntatattu waɗanda aka ambata a cikin hadisin, da kuma halaccinsa a cikin kowanne lokaci na dare ko na rana.
  4. Hikima akan hana sallah a cikin waɗannan lokutan: Asali musulmi ya miƙa wuya ga dukkanin umarnin Allah, kuma ya nisanci hane-hanenSa dan yin bauta ga Allah, kada ya tsaya daga bauta har sai ya tsinkayi hikima ko illa daga umarni kaza, ko hani akan hakan, kawai ya wajaba a kansa ya miƙa wuya, haƙiƙa wasu hikimomin sun zo ne a cikin wasu hadisan daban a cikin hakan: Na farko: Lallai cewa a lokacin garjin azahar, kafin zawali ana kunna wuta ta Jahannama kunnawa mai kaiwa koli. Na biyu: Hikima akan hani daga yin sallah a lokacin ɓullowar rana da lokacin faɗuwarta, don hakan kamanceceniya ce da mushrikai, domin su suna yi wa rana sujjada a lokacin bullowarta da lokacin faduwarta. Na uku: Amma hani akan sallah bayan sallar Asuba zuwa bullowar rana, da bayan sallar La'asar har zuwa faduwar rana, to dan toshe kafa ne; don kamanceceniya da kafirai ya yanke, kuma kada musulmi ya yi kamanceceniya da su a cikin shirkarsu, domin cewa su suna yin sujjada ga rana a lokacin bullowarta da lokacin faɗuwarta.
Madogara

صحيح مسلم (1/ 568) (831). توضيح الأحكام مِن بلوغ المرام، لعبد الله البسام (1/ 488). فتح ذي الجلال والإكرام شرح بلوغ المرام، لابن عثيمين (1/ 438). منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (2/ 202). سبل السلام، لمحمد الصنعاني (1/ 167).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
LOKUTAN HANI GAME DA YIN SALLAH

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com