Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan zai shiga bandaki zai ce: "Ya Allah ni ina neman tarinKa daga Shaidanu maza da Shaidanu mata
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan zai shiga bandaki zai ce: "Ya Allah ni ina neman tarinKa daga Shaidanu maza da Shaidanu mata".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya yi nufin shiga gurin da zai biya bukatarsa a cikinsa, fitsarine ko bayan gida, zai nemi tsarin Allah, kuma zai fake gareShi da ya kareShi daga sharrin Shaidanu maza da mata, An fassara khubs da kahaba'is kuma da sharri da kuma najasa.
Fa’idoji
An so yin wannan addu'ar a yayin nufin shiga bandaki.
Dukkanin halitta masu bukatuwa ne zuwa Ubangijinsu na a tunkude abinda yake cutar da su a kowanne yanayi.
Madogara
صحيح البخاري (1/ 40) (142).
صحيح مسلم (1/ 283) (375).
الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (1/ 23).
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام (ص36).
Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan zai shiga bandaki zai ce: "Ya Allah ni ina neman tarinKa daga Shaidanu maza da Shaidanu mata · Hadisai tare da sharhi · Sabīl