Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

WAFATINSA TSIRA DA AMINCIN SU TABBATA A GARESHI

Hadisai 14

Abdurrahman Dan Abubakar Assiddik -Allah ya yarda dasu ya shiga wajen Annabi tsira da aminci su tabbata a gare shi, a lokacin Na jingina Annabi a kirji na, A wajen Abdurrahman akwai danyen asuwaki, sai Manzo tsira da amincin Allah ya kalli asuwakin

عن عائشة رضي الله عنها قالت: ((دخل عبد الرحمن بن أبي بكر الصديق رضي الله عنهما على النبي صلى الله عليه وسلم وأنا مُسْنِدَتُه إلى صدري، ومع عبد الرحمن سِواك رَطْب يَسْتَنُّ به، فأَبَدَّه رسول الله صلى الله عليه وسلم بَصَره، فَأَخَذْتُ السِّوَاك فَقَضَمتُه، فَطَيَّبتُه، ثُمَّ دَفَعتُهُ إلى النبي صلى الله عليه وسلم فَاسْتَنَّ به فما رأيتُ رسول الله صلى الله عليه وسلم استَنَّ اسْتِنَانًا أَحسَنَ منه، فَما عَدَا أن فَرَغَ رسول الله صلى الله عليه وسلم : رَفَع يَدَه -أو إصبعه-، ثم قال: في الرفيق الأعلى -ثلاثا- ثمَّ قَضَى، وكَانت تقول: مَاتَ بَينَ حَاقِنَتِي وَذَاقِنَتِي)).
Daga Aisha Allah ya yarda da ita- tace: ((Abdurrahman Dan Abubakar Assiddik -Allah ya yarda dasu ya shiga wajen Annabi tsira da aminci su tabbata a gare shi, a lokacin Na jingina Annabi a kirji na, A wajen Abdurrahman akwai danyen asuwaki, sai Manzo tsira da amincin Allah ya kalli asuwakin, sai Na karbi asuwakin Na tauna masa shi, Na kuma kansasa shi, sannan Na baiwa Annabi tsira da aminci yayi asuwakin da shi, ban taba ganin Manzon Allah ya yi asuwaki mai kyau irn wannan ba, yana gamawa sai ya daga hannunsa ko danyatsansa sannan yace: Izuwa abota madaukakiya sau uku sannnan ya rasu. Aisha ta kasance tana fadar cewa: ya rasu a tsakanin haba ta da cinyoyi na)).
Buhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Aisha tana bada labarin irin kaunar da Annabi tsira da amincin Allah ke yiwa asuwaki da kuma yadda ya damu da shi. Shi ne take fadar yadda Dan'uwanta - Allah ya yarda da shi- ya zo da danyen asuwaki wajen Annabi tsira da aminci su tabbata a gare shi lokacin barinsa duniyan. lokacin da Annabi tsira da aminci yaga asuwakin a wajensa, rashin lafiyarsa bata hana shi nuna yana son asuwakin ba, sai ya kalli asuwakin, kamar yana so, sai Aisha Allah ya yarda da ita ta kula da haka sai ta karbi asuwakin daga hannun Dan'uwanta ta sa bakinta ta gyarawa Annabi asuwakin, ta bashi ya goge bakinsa da shi -tsira da aminci su tabbata a gare shi. Aisha bata taba ganin wanda ya fi shi iya goge baki ba. Bayan ya gama goge bakin, sai ya daga yatsansa sama, yana dayanta Allah Madaukaki, sannan ya zabi komawa kusa da Mahaliccinsa, sannan ya rasu. Aisha tav kasance cikin farin ciki, ya cancanta tayi farin ciki kuwa, don kuwa Manzo tsira da amincin Allah ya rasu kansa na jingine a kirjinta.

Madogara

الإلمام بشرح عمدة الأحكام، إسماعيل بن محمد الأنصاري، دار الفكر، دمشق، الطبعة: الأولى 1381هـ. تأسيس الأحكام، أحمد بن يحيى النجمي، دار علماء السلف، الطبعة: الثانية 1414هـ. تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، عبد الله بن عبد الرحمن البسام، تحقيق: محمد صبحي حلاق، مكتبة الصحابة، الأمارات، مكتبة التابعين، القاهرة، الطبعة: العاشرة 1426هـ. تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، محمد بن صالح العثيمين ، مكتبة الصحابة، الإمارات، الطبعة: الأولى 1426هـ. عمدة الأحكام من كلام خير الأنام -صلى الله عليه وسلم- لعبد الغني المقدسي، دراسة وتحقيق: محمود الأرناؤوط، مراجعة وتقديم: عبد القادر الأرناؤوط، دار الثقافة العربية، دمشق، بيروت، مؤسسة قرطبة، الطبعة: الثانية 1408 هـ. صحيح البخاري، محمد بن إسماعيل البخاري الجعفي، تحقيق: محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، الطبعة: الأولى 1422هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Ku wuce Abubakar, ku bar shi ya yi Sallah tare da mutane

عن ابن عمر رضي الله عنهما قال: لما اشتد برسول الله صلى الله عليه وسلم وجعه، قيل له في الصلاة، فقال: «مروا أبا بكر فليُصَلِّ بالناس» فقالت عائشة رضي الله عنها : إن أبا بكر رجل رقيق، إذا قرأ القرآن غلبه البكاء، فقال: «مُرُوه فليُصَلِّ». وفي رواية عن عائشة رضي الله عنها ، قالت: قلت: إن أبا بكر إذا قام مقامك لم يُسْمعِ الناس من البكاء.
Daga Ibn Umar, Allah ya yarda da su, wanda ya ce: Lokacin da Manzon Allah - Salati da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya zama mai tsananin ciwo, sai aka ce masa a cikin addu’a, sai ya ce: “Ku wuce Abubakar, ku bar shi ya yi Sallah tare da mutane.” A’isha, Allah Ya yarda da ita, ta ce: Abubakar mutum ne mai tawakkali. Idan ya karanta Alkur'ani, sai kuka ya mamaye shi, sai ya ce: "Nuna masa, sai ya yi addu'a." Kuma a cikin wata ruwaya daga Aisha - Allah ya yarda da ita - ta ce: Na ce: Idan Abubakar ya maye gurbinka, ba zai ji mutane suna kuka ba.
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Lokacin da zafin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya tsananta, bai sami ikon shugabantar da mutane ba, umarni daga gare shi na umartar Abubakar - Allah ya yarda da shi - ya jagoranci liman, kuma ya yi kuka mai yawa a lokacin da yake karatun Alkur'ani, don haka Aisha - Allah ya yarda da ita - ta nemi gafara kan hakan, amma a cikin hadisin kofar Kukarsa daga karatun Alkur'ani ba ita ce babban burinta ba, maimakon haka babban burinta shi ne tsoron kada mutane su zama masu kushewa game da mahaifinta, don haka sai ta nuna - Allah Ya yarda da ita - daban da abin da take so a cikin zuciyarta. A wata ruwaya a cikin Muslim: "Ta ce: Na rantse da Allah, ba ni da komai face kiyayya ga mutane su zama masu bakin ciki, ga wanda ya fara tsayawa a wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -." Ta ce: Don haka na sake bita sau biyu ko uku, sai ya ce: "Don isa ga mutanen Abubakar, don haka ku abokan Yusef ne. Abin da ake nufi da "abokan Yusef" shi ne cewa su kamar sahabban Yusef ne wajen nuna bambancin abin da ke ciki, kuma wannan jawabin, ko da kuwa a jam'i ne, Aisha ce kawai ake nufi, kamar yadda abin da ake nufi da sahabban Yusef Zulekha ne kawai, don haka Al-Hafiz ya ce ita matar ƙaunataccen Misira a lokacin. Kamanceceniya a tsakanin su a cikin haka shi ne, Zulekha ta tara matan ta kuma nuna musu darajar karimci, kuma abin da take so sama da haka shi ne su kalli Hassan Youssef su ba ta uzuri a cikin kaunarsa. Tare da shi, kamar yadda ta bayyana a wasu hadisai, ta ce: "Me ya sanya na sake bibiyar shi sai dai hakan ba ya fada cikin zuciyata mutane su so wani mutum bayan wanda ya maye gurbinsa."

Madogara

رياض الصالحين من كلام سيد المرسلين؛ للإمام أبي زكريا النووي، تحقيق د. ماهر الفحل، دار ابن كثير-دمشق، الطبعة الأولى، 1428ه. - بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين؛ تأليف سليم الهلالي، دار ابن الجوزي- الطبعة الأولى1418ه. - نزهة المتقين شرح رياض الصالحين؛ تأليف د. مصطفى الخِن وغيره، مؤسسة الرسالة-بيروت، الطبعة الرابعة عشر، 1407هـ. - صحيح البخاري عناية محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة، الطبعة الأولى، 1422هـ. - صحيح مسلم؛ حققه ورقمه محمد فؤاد عبد الباقي، دار عالم الكتب-الرياض، الطبعة الأولى، 1417هـ. نيل الأوطار- محمد بن علي الشوكاني -تحقيق: عصام الدين الصبابطي- دار الحديث، مصر- الطبعة: الأولى، 1413هـ - 1993م.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Ya Allah, ka gafarta mini ka yi mani rahama, kuma ka riskar da ni da mafi girman abokin zama

عن عائشة رضي الله عنها ، قالت: سمعت النبي صلى الله عليه وسلم وَهُوَ مُسْتَنِدٌ إلَيَّ، يَقُولُ: «اللَّهُمَّ اغْفِرْ لِي وارْحَمْنِي، وأَلْحِقْنِي بالرَّفِيقِ الأَعْلَى».
Daga A’isha, Allah Ya yarda da ita, wacce ta ce: Na ji Annabi - Salatin Allah da amincin Allah su tabbata a gare shi - yayin da yake dogaro da ni, yana cewa: “Ya Allah, ka gafarta mini ka yi mani rahama, kuma ka riskar da ni da mafi girman abokin zama.”
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Lokacin da rayuwar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ta kusanto, sai ya dogara da Uwar Muminai, A'isha - Allah ya yarda da ita - kamar yadda ya roki Ubangijinsa ya hada shi da sahabi, wato annabawa, masu gaskiya, shahidai da salihai.

Madogara

صحيح البخاري, ترقيم محمد فؤاد عبد الباقي, دار طوق النجاة, الطبعة الأولى، 1422هـ. صحيح مسلم, ترقيم محمد فؤاد عبد الباقي, دار إحياء التراث العربي, بيروت. شرح رياض الصالحين لابن عثيمين, دار الوطن للنشر، الرياض, الطبعة: 1426هـ. بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين لسليم الهلالي, دار ابن الجوزي. نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين, مؤسسة الرسالة, الطبعة الرابعة عشر, 1407ه. الاستذكار لابن عبد البر, ت: سالم محمد عطا، محمد علي معوض, دار الكتب العلمية, الطبعة الأولى، 1421ه.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

An karvi ran Manzon Allah SAW kansa yana tsakanin Wuyana da Qirjina, yayin da ransa ya futa, ban tava jin wani qanshi kamar wannan

عن عائشة رضي الله عنها ، قالت: «قُبِض رسولُ الله صلى الله عليه وسلم ورأسُه بين سَحْري ونَحْري»، قالت: «فلمَّا خَرَجَتْ نفْسُه، لم أَجِدْ ريحا قَطُّ أطْيَبَ منها».
Daga Nana Aisha -Allah ya yarda da ita- ta ce: "An karvi ran Manzon Allah SAW kansa yana tsakanin Wuyana da Qirjina, yayin da ransa ya futa, ban tava jin wani qanshi kamar wannan"
Ahmad ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Nana Aisha Matar Manzon Allah SAW tana bada labarin cewa Manzon Allah SAW ya yi wafati kansa yana tsakanin Wuyanta da Qirjinya, yayin da ransa ya futa, ban tava jin wani qanshi kamar wannan

Madogara

- مسند الإمام أحمد بن حنبل، تحقيق: شعيب الأرنؤوط - عادل مرشد، وآخرون، نشر: مؤسسة الرسالة، الطبعة: الأولى، 1421هـ - 2001م. - النهاية في غريب الحديث والأثر، لابن الأثير، نشر: المكتبة العلمية - بيروت، 1399هـ - 1979م، تحقيق: طاهر أحمد الزاوى - محمود محمد الطناحي. - تاج العروس من جواهر القاموس، للزبيدي، نشر: دار الهداية. - معجم اللغة العربية المعاصرة، للدكتور أحمد مختار عبد الحميد عمر بمساعدة فريق عمل، الناشر: عالم الكتب، الطبعة: الأولى، 1429 هـ - 2008 م.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Yayin da ya Wanke Manzon Allah SAW ya tafi yana neman abunda ake samu ga Mamaci, bai samu komai ba, sai ya ce: Fansarka da Mahaifina , Kana tsaftace a halin kana da Rai, haka ma bayan ka Mutu

عن علي بن أبي طالب رضي الله عنه ، قال: لما غَسَّل النبيَّ صلى الله عليه وسلم ذَهَبَ يَلْتَمِسُ منه ما يُلتمس مِن الميِّت، فلم يَجِدْه، فقال: «بأبي الطيِّب، طِبتَ حيًّا، وطِبتَ ميتًا».
Daga Aliyu Bn Abi Xalib -Allah ya yarda da shi- ya ce: "Yayin da ya Wanke Manzon Allah SAW ya tafi yana neman abunda ake samu ga Mamaci, bai samu komai ba, sai ya ce: Fansarka da Mahaifina , Kana tsaftace a halin kana da Rai, haka ma bayan ka Mutu"
Ibnu Majah ne ya Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Yayin da ya Wanke Manzon Allah SAW ya tafi yana neman abunda ake samu ga Mamaci, na bunda yake futa daga jikinsa na futsari ko bayan gida ko mai kama da shi, bai samu komai ba, saboda ana iya samun wani abu saboda sakin da gavvai suka yi, sai Ali ya ce: Fansarka da Mahaifina ya Manzon Allah , Kana tsaftace a halin kana da Rai, haka ma bayan ka Mutu

Madogara

- سنن ابن ماجه، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، نشر: دار إحياء الكتب العربية - فيصل عيسى البابي الحلبي. - حاشية السندي على سنن ابن ماجه، لمحمد بن عبد الهادي التتوي نور الدين السندي، الناشر: دار الجيل – بيروت. - معجم اللغة العربية المعاصرة، للدكتور أحمد مختار عبد الحميد عمر بمساعدة فريق عمل، الناشر: عالم الكتب، الطبعة: الأولى، 1429 هـ - 2008 م. - صحيح وضعيف سنن ابن ماجه, محمد ناصر الدين الألباني , برنامج منظومة التحقيقات الحديثية - من إنتاج مركز نور الإسلام لأبحاث القرآن والسنة بالإسكندرية.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Qarshen ganin da nayiwa Manzon Allah SAW shi ne lokacin da ya buxe labule yaga Mutane sunyi Sahu a bayan Abubakar -Allah ya yarda da shi

عن أنس رضي الله عنه قال: «آخِرُ نَظْرة نَظَرْتُها إلى رسول الله صلى الله عليه وسلم كَشَف السِّتارة والناسُ صُفوف خَلْف أبي بكر رضي الله عنه ، فأراد أبو بكر أنْ يَرْتَدَّ، فأشار إليهم أَنِ امكثُوا وأَلْقى السِّجْفَ، وتُوفِّي مِن آخِرِ ذلك اليوم، وذلك يومَ الإثنين».
Daga Anas -Allah ya yarda da shi- ya ce: "Qarshen ganin da nayiwa Manzon Allah SAW shi ne lokacin da ya buxe labule yaga Mutane sunyi Sahu a bayan Abubakar -Allah ya yarda da shi- sai Abubakar ya so ya dawo baya, sai yayi masa nuni da yayi zamansa, sai ya saki labulen kuma yayi Wafati a wannan Ranar kuma ita ce ranar litinin"
Al-Nasa'i Ya Rawaito shi - Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Qarshen ganin da Anas -Allah ya yarda da shi yayiwa Manzon Allah SAW shi ne lokacin da ya buxe labulen da yake tsakanin Xakinsa da Masallaci sai yaga Mutane sunyi Sahu suna Sallah a bayan Abubakar -Allah ya yarda da shi- sai Abubakar ya zaci cewa Manzon Allah SAW futowa Sallah zai yi sai ya so ya dawo baya, don Manzon Allah yazo ya ja, sai yayi masa nuni da yayi zamansa, sai ya saki labulen kuma, kuma yayi Wafati a wannan Ranar kuma ita ce ranar litinin

Madogara

- صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، نشر: دار إحياء التراث العربي – بيروت. - السنن الصغرى للنسائي "المجتبى"، تحقيق: عبد الفتاح أبو غدة، نشر: مكتب المطبوعات الإسلامية – حلب، الطبعة: الثانية، 1406ه – 1986م. - حاشية السندي على سنن ابن ماجه، لمحمد بن عبد الهادي التتوي نور الدين السندي، الناشر: دار الجيل – بيروت. - شرح سنن النسائي المسمى «ذخيرة العقبى في شرح المجتبى»، المؤلف: محمد بن علي بن آدم الإثيوبي الوَلَّوِي، الناشر: دار المعراج الدولية للنشر - دار آل بروم للنشر والتوزيع, الطبعة الأولى, 1416- 1424.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Bana kishin Mutuwar wani da Mutuwa da tafi bani tsoro da tsanani kamar Mutuwar Manzon Allah SAW

عن عائشة رضي الله عنها قالت: «ما أَغْبِطُ أحدًا بهَوْنٍ موتٍ بَعْدَ الذي رَأَيتُ مِنْ شدَّة مَوْت رسول الله صلى الله عليه وسلم ».
Daga Nana Aisha -Allah ya yarda da ita ta ce: "Bana kishin Mutuwar wani da Mutuwa da tafi bani tsoro da tsanani kamar Mutuwar Manzon Allah SAW"
Al-Tirmithi Ya Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Nana Aisha tana cewa: lallai cewa ita ba zatayi farin ciki da sauqin Mutuwar wani ba, kuma ba zata yi fatan ta zama mai sauqi ba, bayan abun da ta gani ga Manzon Allah SAW haqiqa tasan cewa tsananin Mutuwa ba ita ce take nuna Mummunan qarshe ga mamaci ba, kuma ba saqinta ba ne yake nuna Karama ba, kuma inda haka ne da Manzon Allah SAW ya kasance Mafi cancantar Mutane da shi, to don haka kada kuji tsoron tsananin Mutuwa, kuma kada kuyi farin cikin don wani ya Mutu ba tare da tsanani ba.

Madogara

- سنن الترمذي، نشر: شركة مكتبة ومطبعة مصطفى البابي الحلبي – مصر، الطبعة: الثانية، 1395هـ - 1975م. - مختصر الشمائل المحمدية، للألباني، نشر: المكتبة الإسلامية – عمان – الأردن. - مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، لعلي بن سلطان الملا الهروي القاري، الناشر: دار الفكر، بيروت – لبنان، الطبعة: الأولى، 1422هـ - 2002م. - تحفة الأحوذي بشرح جامع الترمذي لمحمد عبد الرحمن بن عبد الرحيم المباركفورى، الناشر: دار الكتب العلمية – بيروت.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Yayin da Annabi SAW ya rasu sai suka ce: a ina za'a Binne shi? sai Abiubakar ya ce: a wurin da ya ra su a cikinsa

عن عائشة رضي الله عنها ، قالت: لما مات النبيُّ صلى الله عليه وسلم قالوا: أين يُدْفنُ؟ فقال أبو بكر: في المكان الذي مات فيه.
An rawaito daga Nana Aisha -Allah ya yarda da ita- ta ce: "Yayin da Annabi SAW ya rasu sai suka ce: a ina za'a Binne shi? sai Abiubakar ya ce: a wurin da ya ra su a cikinsa"
Ibnu Sa'ad ne ya Rawaito shi - Al-Tirmithi Ya Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

yayin da Manzon Allah SAW yayi wafati Sahabbai sunyi savanin wurin da za'a binne shi a cikinsa, sai Abubakar ya ce: ku binne shi a wurin da ya rasu a cikinsa, a cikin wasu Riwayoyi: cewa Abubakar ya ji Manzon Allah SAW yana cewa: Babu wani Annabi daga cikin Annabawa sai a Mahallin da yake son a binneshi a cikinsa

Madogara

- الطبقات الكبرى، المؤلف: أبو عبد الله محمد بن سعد بن منيع الهاشمي المعروف بابن سعد، المحقق: إحسان عباس، الناشر: دار صادر – بيروت، الطبعة: الأولى، 1968 م. - سنن الترمذي، نشر: شركة مكتبة ومطبعة مصطفى البابي الحلبي – مصر، الطبعة: الثانية، 1395هـ - 1975م. - مختصر الشمائل المحمدية، للألباني، نشر: المكتبة الإسلامية – عمان – الأردن. - مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، لعلي بن سلطان الملا الهروي القاري، الناشر: دار الفكر، بيروت – لبنان، الطبعة: الأولى، 1422هـ - 2002م.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
8 cikin 14
Hadisai 14
  1. Abdurrahman Dan Abubakar Assiddik -Allah ya yarda dasu ya shiga wajen Annabi tsira da aminci su tabbata a gare shi, a lokacin Na jingina Annabi a kirji na, A wajen Abdurrahman akwai danyen asuwaki, sai Manzo tsira da amincin Allah ya kalli asuwakin
  2. Ku wuce Abubakar, ku bar shi ya yi Sallah tare da mutane
  3. Ya Allah, ka gafarta mini ka yi mani rahama, kuma ka riskar da ni da mafi girman abokin zama
  4. An karvi ran Manzon Allah SAW kansa yana tsakanin Wuyana da Qirjina, yayin da ransa ya futa, ban tava jin wani qanshi kamar wannan
  5. Yayin da ya Wanke Manzon Allah SAW ya tafi yana neman abunda ake samu ga Mamaci, bai samu komai ba, sai ya ce: Fansarka da Mahaifina , Kana tsaftace a halin kana da Rai, haka ma bayan ka Mutu
  6. Qarshen ganin da nayiwa Manzon Allah SAW shi ne lokacin da ya buxe labule yaga Mutane sunyi Sahu a bayan Abubakar -Allah ya yarda da shi
  7. Bana kishin Mutuwar wani da Mutuwa da tafi bani tsoro da tsanani kamar Mutuwar Manzon Allah SAW
  8. Yayin da Annabi SAW ya rasu sai suka ce: a ina za'a Binne shi? sai Abiubakar ya ce: a wurin da ya ra su a cikinsa
  9. Cewa Abubakar ya shiga ga Annabi SAW bayan Wafatinsa, sai ya sanya bakinsa akan Idanunsa, ya sanya Hannayensa akan Mukamukinsa, kuma ya ce: "Ya Annabi, ya Badadi, ya zababbe"
  10. Yayin da Manzon Allah SAW ya shiga Madina a cikinta kowane abu ya haskaka, kuma Ranar da ya rasu a cikinta kowane abu a cikinta yayi duhu
  11. Ba'a rabawa Magadana ko dinare daya ko Dirhami abunda na bari bayan abincin Iyalina, da ladan Ma'aikata na to sauran Sadaka ne
  12. Manzon Allah SAW bai bar Dinare da Dirhami ba ko Akuya ko Raqumi kuma bai yi Wasiyya da komai ba
  13. Lallai ba'a karvar ran wani Annabi face sai an nuna masa Masaukinsa a Al-janna, sannan a bashi zavi" to yayin da Mutuwa ta sauka gare shi, Kansa yana kan cinyata sai ya suma, sannan ya farka sai idonsa ya kafe yana kallon rufin xakin, sannan ya ce: "Ya Ubangiji kusanci Mafi xaukaka"
  14. Ku kula da sallah da abinda hannayenku suka mallaka

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com