Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana shiga bayan gida, sai ni da wani yaro sa'ana mu ɗaukar masa salka ta ruwa da kuma sanda sai ya yi tsarki da ruwa
Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - yana bada labarin cewa shi ya kasance da wani mai yin hidima sa'ansa a shekaru suna bin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - idan ya fita dan biyan buƙatarsa, suna ɗaukar masa sanda mai kai irin kan goron mashi dan ya sanyata kariya da zai rataya wani abu a kanta yana mai suturtawa ko kuma sutura ga sallarsa, kuma suna ɗaukar masa ƙaramar ƙwarya na fata wacce take a cike da ruwa, idan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya gama biyan buƙatarsa sai ɗaya daga cikinsu ya ba shi ƙwaryar, sai ya yi tsarki da ruwa.
- Musulmi ya yi tanadin ruwan tsarki a lokacin biyan buƙata; dan kada ya buƙatar da shi zuwa tashi sai ya ɓata jikinsa.
- Kiyaye al'aura a lokacin biyan buƙata dan kada wani ya ganta; domin kallon al'aura haramun ne, ya kasance yana kafa sanda a ƙasa kuma yana shinfiɗa tufa mai suturtawa a kanta.
- Koyar da yara ladubban Musulunci da kuma tarbiyantar da su akanta; dan su gaje su (su saba da su).
صحيح البخاري (1/ 42) (152). صحيح مسلم (1/ 227) (271). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، لعبد الله البسام (ص40). تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، لابن عثيمين (1/ 43). الإفهام في شرح عمدة الأحكام، لابن باز (ص84).