Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Lallai za'a samu wasu shugabanni zasu dinga ƙarya suna zalinci, wanda ya gasgata su akan ƙaryarsu kuma ya taimakesu akan zalincinsu to ba ya ta tare da ni, nima bana tare da shi

عَنْ حُذَيْفَةَ رَضيَ اللهُ عنهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «إِنَّهَا سَتَكُونُ أُمَرَاءُ يَكْذِبُونَ وَيَظْلِمُونَ، فَمَنْ صَدَّقَهُمْ بِكَذِبِهِمْ وَأَعَانَهُمْ عَلَى ظُلْمِهِمْ فَلَيْسَ مِنَّي، وَلَسْتُ مِنْهُ، وَلَا يَرِدُ عَلَيَّ الْحَوْضَ، وَمَنْ لَمْ يُصَدِّقْهُمْ بِكَذِبِهِمْ وَلَمْ يُعِنْهُمْ عَلَى ظُلْمِهِمْ فَهُوَ مِنِّي، وَأَنَا مِنْهُ، وَسَيَرِدُ عَلَيَّ الْحَوْضَ».
Daga Huzaifa - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai za'a samu wasu shugabanni zasu dinga ƙarya suna zalinci, wanda ya gasgata su akan ƙaryarsu kuma ya taimakesu akan zalincinsu to ba ya ta tare da ni, nima bana tare da shi, kuma ba zai gangarowa Alkausara ba, wanda bai gasgatasu akan ƙaryarsu ba kuma bai taimakesu akan zalincinsu ba to shi yana tare da ni, nima ina tare da shi, kuma zai zo Alkausara".
Ahmad ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wasu shagabanni da zasu shugabanci mutane bayan rasuwarsa zasu dinga ƙarya a magana sai su dinga faɗin abinda ba sa aikatawa, kuma suna zalinci a cikin hukunci, wanda ya shiga gurinsu ya gasgata su akan ƙaryarsu, kuma ya taimakesu da aikata zalinci ko faɗarsa, kamar ba su fatawa dan neman kusancinsu da kwaɗayin abinda ke hannunsu; to ni babu ruwana da shi, ba shi ba ni, ba ni ba shi, kuma ba zai zo Alkausara ba ranar alƙiyama. Wanda bai shige su ba , kuma bai gasgatasu akan ƙaryarsu ba kuma bai taimakesu akan zalincinsu ba to yana tare da ni, kuma zai zo Alkausara ranar alƙiyama ba.

Fa’idoji
  1. Shugabanni idan an shiga gurinsu dan fadakarwa da shiryarwa da sauƙaƙa sharri; wannan shi ne abin nema, amma idan ya shiga gurinsu dan ya taimakesu akan zalinci kuma ya gasgatasu da ƙarya to wannan shi ne abin zargi.
  2. Bayanin narko na azaba ga wanda ya taimaki wani shugaba akan zalincinsa.
  3. Wannan narkon a cikin Hadisin yana nuni akan haramcin wannan aikin, kuma hakan yana daga cikin manyan zunubai.
  4. Kwaɗaitarwa a kan taimakekeniya akan aikin alheri da kuma tsoron Allah, da rashin taimakekeniya a kan zunubi da shisshigi.
  5. Tabbatar da tafkin Alkausara ga Annabinmu Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, kuma lallai cewa al'ummarsa zasu gangaro zuwa gare shi.
Madogara

مسند أحمد (38/ 295) (23260). ذخيرة العقبى في شرح المجتبى (32/ 334).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
LADUBBAN UMARNI DA KYAKKYAWAN AIKI DA HANI DAGA MUMMUNA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com