Kuma yayin da Amr Dan Sa'ad Da Asw, wanda aka fi sani da Al'ashdaq, cewa ya shirya runduna zuwa Makka Mai Alfarma kuma a lokacin yana sarki ne a Madina don ya yaki Abdullahi Dan Zubair sai Abu Shuraih ya zo masa, Khuwailid Dan Amr Alkhuza'i, don yayi masa Nasiha kan hakan. to sabida kasancewar wanda za'a yi wa nasihar yanajin kansa sai Abu Shuraih ya tausasa murya a gares hi, don Hikimarsa da kuma dora shi kan daidai don Nasihar tasa ta samu gurbin karba, da kuma karshen yayi kyau, sai ya nemi ayi masa ison ganin nasadon yi masa Nasiha a al'amarin kan rundunar da zzai aika, kuma ya bashi labarin cewa shi yana da tabbacin abinda zai gaya masa, kuma ya kafa dalili da cewa shi yaji wannan abu ne da kunnensa kuma ya rike shi a cikin zuciyarsa, kuma idonsa yaga lokacin da Annabi yake fadarsa, sai Amr Dan Sa'id yayi masa izinin yin Magana. Sai Abu Shuraih ya ce: Lallai cewa Annabi a Safiyar ranar bude makka ""cewa shi ya godewa Allah kuma yabi Ubangiji sannan ya ce: Lallai Makka Allah ya Haramta taTun lokacin da ya halicci sammai da kasa" kuma tana nan a girmamae da kuma tsarkinta, kuma amma mutane basu haramta ta ba kamar yadda suka haramta makiyaya wacce take ta dan wani lokaci ba da kuma wurin kiwo da shan ruwan dabbobi, kuma cewa Allah ne da kansa ya jibanci Haramtawar, don ya kasance mafi girma da kuma isa wajen haramcin to idan idan haramcin ya kasance tsoho haka kuma daga Allah ya ke to bazai halatta ga wani Mutum ba da yayi imani da Allah da kuma ranar lahira kuma indai yana kishin Imaninsa ya zubar da da Jini ko kuma ya sare bishiyarta, kuma idan wani wani yai iinin yaki na a ranar bude Makka, to ai shi ba kamar Manzon Allah ba ne, kuma shi anyi masa Izini amma kai ai ba'a maka ba.kuma cewa lallai ai bai halatta a Yaketa ba ko yaushe, kuma hakan ma ya faru ne wani Dan lokaci na rana sabida waccan bukatar, kuma haramcinta ya kuma dawowakamar yadda yake to duk wanda yaji ya gayawa wanda baiji ba, don wannan ne ya kai wannan Sarki nake isar maka da wannan sakon don ni sheda ne akan wannan Maganar, safiyar Ranar bude Makkah kuma kai baka nan akai, Sai Mutane suka ce Da Abu Shuraih :dame ya amsa maka Amr din ?sai ya ce ya amsamun da cewa "Nafi ka Sanin Wannan Kai Abu Shuraih , Lallai cewa ai Harami baya Kare Mai laifi, ko kuma wanda ya gudo cikinsa bayan yayi barna" Taisir Allam (Shafi na:381) da Tanbih Al'afham (3/519,510) da kuma Ta'asisu Al'ahkam.
عمدة الأحكام، تأليف: عبد الغني بن عبد الواحد المقدسي، تحقيق: محمود الأرناؤوط، دار الثقافة العربية ومؤسسة قرطبة، الطبعة الثانية، 1408هـ. تيسير العلام، تأليف: عبد الله بن عبد الرحمن البسام، تحقيق محمد صبحي بن حسن حلاق، مكتبة الصحابة ومكتبة التابعين، الطبعة العاشرة، 1426 هـ. تأسيس الأحكام شرح عمدة الأحكام، تأليف: أحمد بن يحي النجمي: نسخة إلكترونية لا يوجد بها بيانات نشر. تنبيه الأفهام شرح عمدة الإحكام، تأليف: محمد بن صالح العثيمين، مكتبة الصحابة ومكتبة التابعين، الطبعة الأولى: 1426هـ. الإفهام في شرح عمدة الأحكام، للشيخ عبد العزيز بن عبد الله بن باز، تحقيق: سعيد بن علي بن وهف القحطاني، الطبعة الأولى، 1435 هـ. خلاصة الكلام على عمدة الأحكام، تأليف: فيصل بن عبد العزيز آل مبارك، الطبعة الثانية، 1412 هـ الإلمام بشرح عمدة الأحكام، تأليف: إسماعيل الأنصاري، مطابع دار الفكر، الطبعة الأولى: 1381 هـ صحيح البخاري ، تأليف: محمد بن إسماعيل البخاري ، تحقيق: محمد زهير الناصر، الناشر: دار طوق النجاة الطبعة: الأولى، 1422هـ صحيح مسلم ، تأليف: مسلم بن الحجاج النيسابوري، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، الناشر: دار إحياء التراث العربي، بيروت.